FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru ya danyi yana kallon ta ganin yadda itama ta tsaya durus tana kallon bakinshi kamar wacce bata taba tsammanin jin wayannan kalaman agareshi ba.

Raunataccen Murmushi ya kara sakar mata cikin sauke nannauyar ajiyar xuciya snn ya rike hannunta a hankli cikin sanyin murya yace bilti alfarma daya zaki mana dan Allah…tsayawa yay da maganan ya dan dubi fuskar wasime wanda already Ciwon Asthman ta ne yake kkrin tashi sosai..

Dauke kansa yy akanta snn ya dubi bilti Yace bilti dan Allah karki yanke zumuncin dake tsakanin mu,”ko sau daya ne a shekara ki daure kizo ki duba mu a gida.yana fadin hakan ya juya ya kalle fuskar wasime data kulle idanunta gam gam ta lafe ajikinshi tana jajjan zuciyarta da kyar

Dauke kansa yy akanta snn ya kalli biltin yanayin sa kamar na wandq zaiyi kuka muryan sa karye yana murmushi ya dada rungumar wasime ajkin shi yana cewa Ni yanzu zan wuce…

Kallon sa Bilti takeyi zuciyarta cike da mamakin yadda taheer yay saurin fahimtar ta ya mata uzuri, batace mishi uffan ba sai tsumanmen kukan datakeyi mai ban tausayi agaban sa wando ko ba’a fada ba kasan tana cikin wani mayuwacin hali na kuncin rabuwa dasu.

tashin hankli da jin tausayin su mai tsanani shi yake ratsa mata zuciya tanajin kamar ta rufe idanunta ace komi daya faru bai faruba…
Tayi nadaman barin gidan,data san hakane zai faru da duk abunda malam musa ya mata zata daure tay hakuri.

Dama tazo ne koda yan uwanta zasu tayata kare mutunci da martaban ta,saidai hakan bai samu ba..sun muzanta ta sun juya mata baya sannan kawu ya rabata da farincikin ta na kasancewa tare da taheer da wasimen ta.

Tana cikin wannan yanayin kawunta ya saka hannu ya janyeta agaban su suka bar wajen suka bar taheer a tsaye tare da wasime data dan bude
Idanunta kadan tana ta kallon wucewar bilti……..
Na kudine pay 300₦ into
0152983148 mohd sule surayya GTB 08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: M J SKIN CARE PRODUCTS
INA MATA YAN GAYU INA YAN KWALISA MASU SON CI GABAN SKIN DINSU KU ZO GA M J SKINCARE TA KAWO MUKU DA PRODUCT DINTA MASU KYAU DA INGANCI KADAN DAGA CIKIN KAYANTA SUN HADA DA
1 GLOWING SOAP wannan sabulun tana gyara skin tana cire pimples
2 glow oil
3 lighting oil
4 sunburn removed oil
5 face cream
6 shower gel
7 face scrub
Akwai set na glowing set

FR31

Desperate13:my only one

Na kudi ne,300₦ via 0152983148..GTB
08060712446

Ajiyar zuciya taheer ya sauƙe ya juya da wasimé a kafadarsa suka bar wajen suka nufi hanyar gida,shikansa baisan yadda akayi ya kawo su gidan ba tunanin duk abunda ya afku shiya mamaye zuciyar sa musamman ma na tausayin halin da bilti take ciki ayanzu.

Jikinshi yana kan basa cewa bilti bata cikin kwanciyar hankli a duk inda take damuwa da rauni duk ya bayyana a yanayinta,dan tunda suke da ita bai taɓa ganinta acikin irin wannan mummunan yanayin ba.

Wasimé kuwa duk ta galabaice tanata kuka marar sauti tare da yin lamo akan kirjinsa,da kyar take sauke ajiyar zuciya,numfashi mai bala’in kara da wahalar wa shi yake fita daga bakinta.

Har ya shigo dasu gida bata san ina hanklinta yake ba,sunkucanta yay suka shige ciki bai tsaya da ita akoina ba sai dakin sa.

Akan gadonsa ya shimfidata ahankli snn ya dawo gefenta ya zauna ya soma rage mata kayan jikinta tare da bata taimako cikin gaggawa.

Yau Allah ya soshi tana zuƙar inhaler ta sau daya ta samu bacci mai nauyi.
Kallonta ya tsayayi ganin ko acikin baccin ma kuka takeyi duk alamar hakan ya bayyana bisaga yadda take jajjan zuciyarta tana juye juye da hawaye cif a kan fuskarta duk dama idanuwanta a rufe suke cikin bacci.

A bakin gadon ya zauna daf da ita ya shafe ilahirin fuskan sa da tafin hannun sa cikin rasa nayi tausayin ta gaba daya ya kashe masa lakar jiki.

Yaukam yasan komi ya kare masa babu wani abunda ya rage face ya sake ransa yay rayuwar sa a daidai yadda tazo masa..

ya dade yana zaune awajen cikin tunani kafin nan can cikin dage kafadun sa sama ya sauke ajiyan zuciya mai sanyi,Daga nan tashi yay ya nufi masallaci Domin gabatar da sallahn asr.

Bai shigo gidan ba har sai can wajen karfe hudu da rabi na yamma har lokcin ya samu wasime tana kan tikar baccinta

Tsayawa yay akanta yanata kallon yadda ta dukunkune waje guda game da rungume kanta gwanin ban tausayi.

Babu abunda yake dawo masa aransa daya kalle fuskanta ayanzu face maganganun data dinga furtawa wa bilti dazu musamman cewa datake yi yanzu komi nayi mata wuya,tace ana barinta a gida ita kadai,bata iya abinci ba,hakan yana nufin babu wanda zaina mata abincin da zataci
Hakama yaji tana cewa babu mai mata kitso,”
Tausayin ta yakeji aransa..bai san sanda ajiyar zuciya ya kufce masa ba..ya dade a tsaye akanta cikin nazari can kafin nan ya sauke ajiyan zuciya cikin maida numfashi snn yabar wajen ya shige bathrum domin yin wanka.

Sauri yake yana Allah Allah ya gama ya fito kafin ta tashi ta kallesa acikin wani yanayin da bai dace ba,after like 15 mins ya fito jikinshi yay wani fresh kugunsa dore da white towel.

Gaban mirronsa ya wuce sharp sharp ya shafa mansa na aloevera vaseline ya bi jikinshi da turare mai qamshi sannan ya dauko wata neat coffe brown colour jallabiya ya sakata akan wata three qtr shot dake jikinshi..

Tsayawa yy agaban mirror yana kkrin taje suman kanshi daga nan yaji kamar Wasime tafara motsawa.
Da sunan bilti abakinta ta farka cikin gigin baccin da baigama saketa ba tana juye juye.

Idanunta a kulle cikin muryan kuka da magiya mai ban tausayi tafara cewa Dan Allah Dan Allah bilti karki tafi kibarni,aje comb din yay cikin sauri snn ya taho ya zauna a gefen gadon yana kallon yanayinta,
tausayi sosai take basa dan yasan ba’ayi mata daidai yau ba.

But there is no way he is gonna let all they problems disturb his peace,gwara ya maida komi bayan keyansa ya fuskanci abunda zai ficcesu gaba daya.

Yau damuwa yasaka shi neman layin iyayen sa dazu dayaje masallaci amma to his greatest suprise none of them was available to pick his call,Mahaifinshi ma layinsa a kashe ne kamar tsawon lokaci yay bai buÉ—e layinsan ba.

Daga nan ya cire ransa akansu kawai Dan Yasan Babu wanda zai taimaka masa akan wasime
shikuma he cant really concentrate on her fully, ga jarabawar sa ga aikinsa ga zuwa training, dolene kawai yasan yay zaiyi wasime tayi hakri ta mance da zancen bilti.

Haka rayuwan su ya kasance kwana biyun baiya samun sukuni kullum yana kulawa da lpyar wasime sosai.

Kwana biyu adan dolenshi ya dawo da ita ganga da jikinsa tana kwana tare dashi a dakin sa suna baccin su tare akan gado daya.
Kafin ta kwanta haka zai
Lullubeta da jikinshi yay musu addua.

Kullum sai ya jira tayi nisa acikin bacci snn yake jawo ta ya rungume ta ajikinshi suyi baccin su atare domin ta dena jin tsoro aranta ta samu wadataccen bacci da kuma cikakken nitsuwa.

Da alamun dadin hakan wasime takeji dan kuwa daga ya jawota jikinshi take sakar masa jikinta gabaki daya snn ta manne masa ko ta kankame sa cikin gigin bacci ta hana sa sakat da juye juye.mostly ita take hankarar da shi har yasan asubah yay cos a lokacin wani sabuwar sanyi ne mai ratsa kwakwala yake sauka toh rungumar datake masa ma na dabanne awann lokci Mannesa takeyi kamar bazasu taba rabuwa da juna ba.

Kullum kafin ta farka yakanyi sauri ya rigata farkawa harya yi abubuwan dake gaban sa shiyasa haryau bata fahimce abunda yake faruwa atsakanin su wajen bacci ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button