FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin tana ta juye juye tana kuka wasime taji tausayinta ta amshi kudin ta fita waje ganin haddari sosai a sama yasa ta dauki motarta dantay sauri ta dawo kafin ruwa ya sauko.

Tana fita batako yi nisa ba aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya ahaka dai ta samu ta siyi maganin bata sani ba ashe razia ta riga ta yanke wani igiya acikin motar wanda in aka kashe shikenan bazai kara tashi ba harsai anmaida igiyan nan tay tay mota yakiyi ga ruwa haka ta gaji ta kyale tayi zamanta acikin motar tanajiran ruwan yadan tsagaita ta nemi abun hawa kawai ta koma gida.

Karfe bakwai saura taheer ya dawo gidan a mugun gajiye ransa ya gama baci sabida yau yay ayyukan operation sosai amma bai wani ci nasara ba,kusan dukan aikin dayay yau saida yay kuskure which is very unsual of him,tsaban haushi baima jira ruwan ya tsaya ya dawo gida acikin ruwan haka.

Yanayin daya shigo dashi na bacin rai shiya dada karawa razia karfin gwiwar dora shiryayyen makircinta data kulla akan wasime,baiko je dakinshi ba ya tarar da ita a falo,anan yazauna yace ta kawo masa ruwa yasha memakon tahe fridge sai taje daki tay tsafinta ta dawo masa da gwalban giya da kankara acikin glass cup ta zuba ta mika mishi ya farasha tana daga tsaye akansa.
Bayan yasha ya kalleta yace meye kuma na tsaya min akai tace cime da tsarguwa tace babu

Yace ok akwai abinci agidan nan?im hungry kirata takawo mun abinci

Shiru tay da sigar munafurci tace sweet darling ai bata nan ta fita yawonta data saba wallh kana fita itama take ficewa,yau kuma sainaga hartakai dare shine nace ko lpya?ka ganni nan nima Neman layinta nakeyi duk ta kashe waya
Ta tafi tabar mutane da jin yunwa.

Yace what? Kina nufin yarinyar nan bata gidan nan?tace eh ai kullum ma fita takeyi bata son zama,kuma inkarya nake daga ta dawo ka tambayeta zakaji gaskiya nifa bansan inda take zuwa Amma ai mai gadinka ya sani shima dakake ganinsa munafuki ne darling wallh yasan komi ai har a mota ake kawota kofar gidan nan.

Tsaki yaja ya miƙe tsaye ya fita waje fuuuu kishi yabi ya rufe masa ido dariya razia ta tuntsire dashi dan tasan inyana cikin maye yakan tuna cewa wasime matarsa ce shiyasa ma ta bashi yasha din dan ya tuna da aurenshi yayi ma wasine rashin mutunci akan abunda suka shirya yau akanta.

Har bakin gate ya isa ruwa na dukanshi ya same malam jafaru ransa a mugun bace yake tambayarsa questions akan abubuwan da razia ta fada.

Malam yana son ya rufa ma wasime asiri saiga razia ta fito. daga ya budi baki zaiyi magana saita katse shi tace “karya ne”
Dake ita tana lura da duk sanda wasime take ficewa agidan cikin fushi taje gidan bilti saita alakanta hakan da maganan da sukeyi ta daureshi.

Daga karshe dai ran taheer ne ya dada lalacewa daya gane cewa gaskiya razy ta gaya masa kuma malam jafaru yana neman boyewa..shikansa ranan ya sha balbalin masifa.

Ata fannin wasime kuwa tana zaman zaman ta acikin motar taji anan buga mata kofar glass dagowa tay bata wani gani da kyau sabida ruwa
Kunna hasken motar tay ta kalle saheeb da lema yana tsaye yama waiving dinta,aranshi cewa yake aikin razy yay kyau data bashi xct location din wasime “kirjinta ne ya buga ta kallesa hadi da daure fuskanta “

“Hey beauty? Me kikeyi anan lpya kuwa.

Batako amsashi ba ta shareshi,she tot d door was locked kawai ashe yazo da master key irin wanda barayi ke using a hannunshi,nan yasaka ta waje ya bude motar tsorata tay ta matsa a firgice zata tsala ihu.

Ya rigata yana cewa no no no i swear,i mean no harm,Wasime kiyi hakuri da Allah nariga na gane kuskure na,ki yafemin abunda namiki ranan.
Wallh sharrin shaidan ne ki tambaye mijinki na rokesa gafara abunda namiki ban kyauta ba pls for god’s sake kema ki yafemin.

A dan firgice muryanta na rawa cikin masa ihu tace pls leave me alone how did u even open my car dan Allah ka tafi ni banaso.

Yace okay sounding like he is just trying to help,yace”amma me kikeyi anan u shudnt be here alone inashi taheer din?

Shiru ta masa.

Toh sauko mana inkaiki gida inma tsoron tuki kike acikin ruwan nan

Murya Ciki ciki tace no thanks i knw my way home.

Ganin zai matsa mata yasa ta dauke ledar maganin ta sauka ta dayan gefen dama bawani nesa gidansu yake ba saidai ruwan ne yana sauka da dan yawa
Shiyasa batay tunanin takawa ba sabida condition dinta na asthma da karamin ciki.

Ganin saheeb awajen yasa taji tsoro tanajin bazata iya zama ba karyace zai saceta,bata san daga ina karfi yazo mata ba dan ji take kawai she can do evrything to get away from him,fita tay a motan ta fara takawa da kafa zatabi layin anguwansu

Yana ganin haka ya juya ya shiga motarsa suka fara xchanging tex message da razy yana bin wasime ahankli sai sauri take hijabin jikinta ya jike jagwab tana rawan dari.

Tanakaiwa kofar gate saiga shi shima ya iso da motarsa abayanta yay parking bata hankara ba saiga fitowar taheer da razia da malam jafaru a bayansu.

Gabanta taji ya fadi dan babu shakka tasan ita ake nema ,ran sa abace
Yace “Daga ina kike?
Muryanta na rawa sabida sanyi da tsoron yanayin yadda yay mata tambayar tace anty razia ce ta aikene siyan magani Tanakan masa bayani saiga saheeb ya fito yana tunkarosu kishi saiya rufe ma taheer idanunshi atake jikinshi ya fara rawa sosai.

Wasime Bata kammala rufe bakinta bama ya wanka mata mari ya fixgota sukayi ciki yana cewa “come here”

Da ledar maganin da komi sanda ta watsar akasa tsaban tsoro,suna shiga falo ya watsar da ita akan kujera jikinshi na matsanabcin bari idanunshi sunyi jaa cikin daka mata tsawa yace daga ina kika fito and dont u fucking lie to me,bata amsa ba ya bi kanta da ihu a harkuce yanacewa ashe dama fita kikeyi anyhow agidan nan sabida kin raina aure na dayake kanki?

A tsorace cikin kuka tace wallhy yaya aikana tay kuma ai kai kace ina mata abu in ta sakani itace fa ta aikeni chemist.

Kamar zai bugeta ya hargitso cikin masifa yace “kimin shiru karna tattki anan wajen,nasan ure lyieng to me,yanzun nan ki budi baki ki gayamin gaskiya da uban waye kike fita?ina kike zuwa batare da sanni ba.

Ranta ya baci sosai a harzuke cikin ihu ta mayar masa maganan Tace ni bana fita da kowa yaya,wajen bilti kawai nake zuwa kuma ai bana kaiwa dare nake dawowa..yau fa anty razia ce ta aikeni .

Cikin daka mata tsawar daya sata firgita ta zube kasa, yace karya kikemin ba raziar bace ta toni asirinki?Inda aikan ki tay aida zata gayamin ta aikeki,nd she is right Yanzun nan saurayinki ya kawoki a motarsa ko ba shi bane awaje?

Bata iya amsawa tsabar bacin rai ta girgiza kai cikin matsanancin kuka
Tace “yaya wallhy sharri tay min Yaya mesa zaka furta min haka bayan kasan bana da wani saurayi, yaya saheeb ne fa yabiyo ni ban kulashi ba,kuma da kafata na dawo gidan nan mota tace ya baci a bakin shagon.

Bayanin duniyan nan tay masa amma bai fahimceta ba har waje ya jawota.

Ata wajen kuwa malam jafar na labe yana kallon razy da saheeb suna magana harda rungume rungumen juna abun ya bashi mamaki sosai shide baice komi ba hatta zo ta wuce ciki

Tana shiga agabanta ya wullo da wasime waje yana cewa kije ki sameshi bana son na kara ganin fuskarki kuje duk inda zakuje.

zuciya tay batace mishi komi ba ta fice a gidan saidai bataje koina ba tay tsayuwarta acan gindin bishiya ruwa na dukanta sosai tana kuka mai tsuma,mal jafaru yaji tausayinta na fitar hankli dan ko zama bai iyayi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button