FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da cizon yatsa ya zauna yanata kallo aka bawa taheer karramawa na musamman daga united states of America Association of neuro sugeons da general surgery, aka kuma bashi exclusive international appoitnment acan,da kyautar babban gida da tsadaddiyar mota wanda a duk sanda yake sha’awar komawa america yin aikinsa zai zauna awajen da familynsa.

Sabida fitar da saheeb yay awajen yasa aka wuce sunanshi ba akirasa kan stage ba.
Akace masa yazo office ya amsa,duk borinsa haka ya hakura sabida asali taron na sojoji ne.

So civilian doctors din sakayasu kawai dama akayi, So the day was all about doctor TEJ nd he was so honoured nd dignified.

manyan da basu sanshi ba ranan suka hadu dashi in person wasu su karbi contacts wasu su gayyace shi gidajen su a abuja.

Giyan da saheeb yasha yau bana wasa ba,dan tamkar baya wajen haka taro yaci ya watse ba’a a masan da wani gajar likita irinshi ba.

Banda dariyar kayansa da gulmansa da akayi no one really give a damn about his existance.

Sai da yamma aka tashi a taron taheer ya koma lodge dinsa danya huta daga shigarsa bayi zai watsa ruwa ya fadi ya suma bai farfado ba sai can tsakiyar dare,jikinshi ya dau zafi koinanshi na É“ari kar kar ya tsuguna ya dinga kwaza amai yana fidda wasu irin bakaken abubuwan da bai san daga ina suke fitowa ba.

A jikace ya fito bayan ya tsaftace jikinshi,ba a hayyacinshi ba yay magrib yay ishai,jiri ke kai kawo dashi ya fado kan gadonsa yana rike da dakansa idanunsu suna fidda ruwan hawaye kanshi na juyawa

After a while yay bacci ya farka karfe ukun dare wasime na cikin baccinta kusa da anono wayarta yafara ringing tana ganin numbersa ta farka ta dauki wayan ta nufo waje dashi…
COMPLETE DOCUMENT IS 500 VIA O152983148
MOHD SURAYYA SULE GTB CHAT 08060712446
7/31/22, 22:08 – Kawata: 80

Da fargaba da kuma sanyin jiki sosai ayanayinta takai wayan kunnenta cikin sanyin murya tace”Salam Alaikum yaya? jin sassanyar muryan ta mai tsananin taushi da ratsa gangan jiki da kwakwalwa yasashi Lumshe idanunshi…

Atake idanunshin suka hau fidda wasu raunatattun ruwan hawayen da bai san ma’anan su ko dalilin su ba,ayanzu turirin zafin da jikinshi ya dauka shiyake sashi yana fidda wata iriyar wahallaliyar nishi nishi irinta zazzabi mai tsananin zafin nan, tsam tay tana shako zazzafar numfashin shin dake saukowa a wahalce.

Gabanta taji ya fadi kirjinta na bugawa da tsananin karfi tay zaton wani abu ne ya riga ya sameshi ne,cike da rawar murya da fargaba tace yaya?bai barta ta karasa ba ya katse ta Numfashin sa mai nauyi wanda ya sauƙe hadi da sakinshi da dan karfi tanajin shi ahaka batasan sanda hanklinta yay mummunan tashi ba.

Muryanta a sarkafe cikin bugun zcya tace masa yaya lpyrka kuwa Are you okay?.

Lumsashun idanunshi ya
Bude muryansa na dan rawa Ahankli yace”cuty..?

langwabar da wuyanta tay batace komi ba dan rabonshi daya ambace sunanta acikin hayyacinshi haka tun wancan ranar.

a kasalance yana jin kansa kamar mai laifi agareta ya kuma cewa “cutie na har kin mance dani ko? Jin tay shiru yace..innayi miki laifi kiyi hkri kiyafeni..im sorry,im very very sorry pls forgive ur me..i wll neva love to hurt u insha Allah i promise u dat.
Tana share hawayenta da suka sauko cikin sakewar murya tace bakomi yaa babu wani laifi dakamin,yay saurin datsar numfashinta yace a’a..jikina na ban cewa laifi namiki kika shareni..shidai baisan dalilin dayasa yake furta hakan ba amma dai zuciyarsa tana gaya masa cewa yay laifi mai yawa wa matarsa.

lumshe ido Tay snn tay murmushi hawayenta na murna nakan sauÆ™owa kasa tayi saurin maidasu cikin dauriya,”tace A’a yaa na karkace haka,wllh ban mance dakai ba..bazan taba mancewa dakai ba yaya na abun kaunata,ka isa lpya ko?toh ya event din i knw u are alwys the best nd u will win surprises,murmushin dole yay bai amsa ba ya kara lumshe idonsa jin dadi da sanyin muryanta na shigewa har can cikin brain dinsa hadi da ratsa jini da jijiyarsa.

muryan sa can kasa kasa cikin hucin zazzabi yace “i really wish i can see u right now’..”im missing u badly wifey..so how is my bby doing?is my bby kicking ohhh i missed dat little flesh..

hawayenta datake dannewa take suka sauko kasa zirrrrrr tana tarewa dan yatsunta tana murmushi dan rabonshi daya tambayeta lpyar abun dake cikin tun bayan tafiyarsa club a wann daren da bata bukatar tunoshi har karshen rayuwanta..

tare da langwabar da murya tace lpyanmu kalau,bby is missing papa too..kaifa,honey are u okay?I wanna knw if ure okay,?Yaya naji muryan ka wani iri are u really okay pls tell me?Ta karashe magananta cikin nuna damuwarta akansa sosai zuciyanta na bugawa da muradin jin amsarsa.

Numfashi yaja tanajin sautinshi yana fita cikin rauni sosai,muryan sa a dan sarkafe kmr wanda zai sakar mata kuka ya runtse idonshi yay tsam kafin yace “i dont knw if am fine cuty”wallhi bana jin dadin jiki na..wasimé im,i am..Sai yay shiru jin ya kasa karasa sauran zancen..,can cikin rawan murya mai tafe da rudani yace..”Kaina ne”..i dnt knw whats happening to me but banajin kaina daidai yanzu,cute kina min addua kuwa?Im feeling really really weird about my self is like am lost or something..i dont knw whts wrong with me these days seriously..sai naji kamar da can bana duniyar yanzu ne na dawo cikinta,i feel like ive wronged u,i feel like am going into deep confussion nd mess nd i don’t seems to find all the answers right now.

Wasimé,are u angry with me?why im a feeling like i did sumtin to u,nd u hate me,Pls kifada min laifukan danayi miki zan baki hakuri.. u knw the last thing i wanna do in dis world is to hurt u cos ure my life..im deeply scared of loosing u.

..idanunta a lumshe harya gama furta maganganun nasa masu ficewa a numfashinsa tare da rikicewar tunani da rauni da kuma bayyana halin daya keciki na rashin jin dadin jikinshin sosai.

Cikeda lallabi da sauÆ™ar da murya tace “yaa na ka kwantar da hanklinka babu abunda ya faru kamanta ni na rako ka jiya har filin jirgi?pls dont think about anything anymore,u will be fine okay?..Muryansa a disashe tattare da damuwa yace.”U sure baby?gyada kanta tay tana taro hawayenta da suke diddiga a kasa tace “kayi alwala toh ka karanta qur’ani mana yaya na..im sure u will find the peace ure looking for kuma insha Allah zan cigaba da maka addua nima harsai ka fara jin daidai.

Jikinshi a muce cikin sanyin murya yace mata okay.

Daga nan suka fara dan hirarsu mai sanyin dadi wasime tana lallabashi at same time tana dada fahimtar cewa kamar yayanta kam yanzu ya dawo cikin hayyacinshi sosai.Duk dama he is sounding lost nd dumb founded aynzu bai hanata jin tsananin farinciki da Allah ya kwaco mata shi acikin halin daya shiga ciki ba.

Sun kusan kai asuba suna wayar kafin ya kyaleta ya tashi ya doro alwala yay salatul fajr yahau karanta qur’anin dake wayarsa har aka kira sallahn subhi
,wasime tana shigewa daki tay alwala tay sallah itama,daga nan bacci ne ya dan dauƙeta kadan.

Ba ita da farkawa ba sai wajajen karfe tara tana bude ido taga innono nakan shiryawa tana shirin zura hijabinta,tay firgit ta mike zaune tana mutsuka ido a mamakance tace ano ina zakije da sassafen nan kuma?innono tace Kirana akai acan gida,amma karki damu zanje ne na amshi aika kawai in dawo ai ban isa nay nesa da ke ba wasime ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button