FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari sassafe ita da momy suka wuce kaduna sukabar taheer din a abuja sabida case din..Ana tafiya da saheeb gida baifi da awa ba aka watsa breaking news cewa an disqualifying doctorship licenced na doc saheeb kuma an dakatar dashi a aikin likitanci till futher notice,akabi aka laka masa ciwon hauka don a sassauta rade raden jama’a akanshi na cewa da suke a media wai dama can shan giya da bibiyar mata halayayyarsa ce.
COMPLETE DOCUMENT IS 500 VIA O152983148
MOHD SURAYYA SULE GTB CHAT 08060712446
7/31/22, 22:08 – Kawata: FINALE.

A ranar Iyayen saheeb sun shiga tashin hanklin da basu taÉ“a shiga arayuwansu ba kan babanshi tamkar zai buÉ—e,haka ya kikkira abokan harkansa naa siyasa akan suyi wani abu cikin gaggawa akan kwace licenced din dansa saheeb da disqualifying dinshi a matsayin likita da akayi amma haryanzu bai samu wani kakkwaran assurance ba daga baya ma akace masa dawowa da lasisin saheeb a matsayin medical doctor abune mai wuya sabida dumbin shaidar jama’a daya rataya akan wuyanshi.

bakaramin bakin ciki baban nasa yaji ba musamman inya juya ya kalli dansa a kwance kamar asara sojoji sun gama daidaitashi sun bata masa kamannin sa da duka baya ko iyayin kwakkwaran motsi.

Da sassafen ranan prof da momy oma suka isa tsohon gidansu domin su gana da innono. Suna isa suka sameta tanakan shiri zata wuce tasha zuwa garinsu, ganinsu ne yasata zaunawa
Suka bude sabowar shafn tattaunawa.

Kafin afara zancen komi saida prof ta tsuguna ta nemi gafarar inno akan Abunda tayi,inno tay mata fada kam amma bata wani ja maganan ba aganin ta dukan su masu laifi ne ga yaran itama taji takaicin abunda ya faru da taheer da wasime,amma tabarshi ne a matsayin qaddara da ishara garesu duka.

Wann zancen ne ya dago su prof sukaji labarin duk abubuwan da taheer da wasime suka fuskanta a hannun razia da saheeb innono bata boye musu duk yadda akayi ba.

Kowa awajen jikinshi saida yay sanyi,snn inno ta soma gaya musu dalilin ta na tafiyar gaggawa a wancan lokcin shine acan kauyensu ne aka turo mata da sakon cewa wasu mutane su biyu mace da namiji sunxo nemanta akan suna nemanta da yarsu mai suna wasime.

Inno tace abinne yazo mata kamar wani Almara a iya sanin ta dai iyayen wasime basa duniya.

Shiyasa da labari yazo mata tay marmaza ta koma kauyensu ta xauna tana bibiyar labarin koda wata rana zata ci karo dasu ko kuma su sake dawowa.

Bayan tsawon watanni data dauka tana neman su a kauyuka bincikenta ya tabbatar mata da cewa tabbas iyayen wasimen ne,suna raye din kuma sun fito suna neman yarsu ne.

Koda tay tambaya ta bibbi gidajen malaman kauye kowa ce mata yakeyi hakan ba abun mamaki bane danko da gidan nasu ya kone anyi duba amma ba a samu gawarsu ba,amma a lokcin anyi zaton sun zamo toka ne.

Cikin ikon Allah ashe maganin da hassan ya nemo musu ne ya batar dasu suka billa awani gari na daban wanda basu sani ba,jejin fulani ne anan ma suka samu wasu mutanen kirki da suka taimakesu,Aliyu hassan yay jinyar matarsa badiatu na tsawon lokaci kafin nan ta warke suka kama gina sabuwar rayuwarsu cike da kewar yarsu wasime.

Lokaci zuwa lokaci sunsha fita garuruwa neman anono amma basu taÉ“acin sa’ar samun taba,yanxu haka komawarta na wann karon ance mata anji labarinsu ne wai suna can wani gari acikin Garin abuja,ata wajajen da fulanin abujan suka yada zango, kuma ance cikin kankanin lokaci Allah ya maido musu da arzikinsu sun bunkasa a harkan kiwon dabbobi da noma dan haka suna saida tsabar abinci agarin abuja kamar su masara,gero, dawa, wake,alkama shinkafa da su doya da gyada ance har gonan albasa sunayi da sauransu.

Inno batasha mamakin jin hakan ba danko da can ma tasan su masu kashin arziki ne duk abunda suka taɓa bi ixinalllah yakanyi albarka sosai..

Ayanxu sun tara arxikin sai ga tsufa ya fara kamasu, abunda ya rage musu a duniya shine su gana da yarsu wasime da Allah ya albarkacesu da ita wanda ayanzu basu ma san kamanninta ba.

Innono tace bata so ne ta ziyarce su ita kadai shiyasa ta nemeta suje din tare,aganinta taheer ne dama yafi cancanta aje dashi amma yanxu dake baiya cikin hayyacin shi sosai da wuyane wannan tafiyar yayu tare dashi.

Bakaramin jinjina ma wnn lamarin prof tay ba,a wani fannin kuma ta xubda hawayen murna da farinciki ma wasime
Imagining takey ya zataji in akace yau ga iyayenta araye wanda tay tsawon shekaru tana maraicinsu?..aganinta wasime ta cancanci samun duk wata ni’ima daga ubangiji dan asaninta da yarinyar bata taÉ“a raina maraicinta ba kuma ta amshe qaddararta kuma tay hakuri da yanayin rayuwa.

Babu bata lokaci prof tace suje sunemesu din momy oma tace itama zata bisu baza’ayi haka batare da ita ba.

Su ukunsu suka kama hanyar Abuja,kirjin inno na matukar bugawa tana Adduar Allah yasa harsashen su haka ne.

Ata bangaren wasime kuwa sassafe ta fito babu imani ta watso ma razia ruwan sanyi aka ta farka agigice,nan ta umarceta da tahau aikin gida tun asubahi raxia tahau goge goge da shara tay wanke wanke da guga wasu abubuwan ma bata taɓayi arayuwanta ba.

Wasime nakanta da bulalan dorina tace in batayi aikin me kyau ba bazata warkan da ita ba..

Haka raxia taci aiki duk girman gidan haka ta sakata share dukkan compound dinsa har aski ma flower da ban ruwa saida razia tayi.

Yunwa ya galabaitata har layi takeyi intana tafiya jikinta na rawa rawa tsabar azaba.

Tana kammala ayyukan ta wasime ta umarceta data zauna akasa a falo ta jirata.

Breakfast ta debo a kwano ta bata tahauci ham ham itama wasimen tazauna
Tanacin nata,tanaci wasime tana zaginta tana cewa “mayya kawai bake kin iya tsafe mutane kici ubansu ba…kin mance bahaushe yace gaba da gabansa ko? da can kin dauka kowa jaki ne da zaki hau kansa harki wuce abanxa ba aci ubanki ba,toh wallh tsafinki yay karya akaina,dan hakin da kika raina itace zata cigaba da tsole miki ido,uban da ya kawoki gidana kina claiming mijina ubanda zaisa kici ubanki a hannun na,kuma dan ga mahalukin da yau zaizo nan ya ceceki,shegiya kawai dan tsabar rainin wayo har kina kwana da mijina kina umartansa yana maidani baiwarki ance miki ni mahaukaciya ce bansan abunda ya kawoni duniya ba?ke acikin matsafan ma ke yar rainin hankli ne amma zaki gane bambacin aya da tsakuwa barima sai mijina ya dawo zansa ya lakada miki dukan tsiya ya kasheki da duka nan ne zaki san kin debo ruwan dafa kanki ..
Bayan ta gama masifan tabi ta da matsiya cin harara taja tsaki mai kauri.

Rike da kwano abinci kamar almajira razia ta sake baki galala tana kallon wasime tana zubda hawaye,jin ance taheer zai dawo yaci ubanta nan da tafara magiya tanacewa anty wasime dan Allah kiyi hkri kiyafemin,wallh sakani akayi in cutar da rayuwar taheer bayi na bane walhi saheeb ne.

Kuma Nayi hakan sabida ya aureni amma ni asali ma bansanki ba ban kuma san taheer ba,shiyace min inna cutar da taheer na rabaki dashi zai aure ni..

Wasime ta doka shewa cikin dago kan zancen tace “tabdi jam..kaji
asararriya, lallai,..razia kike ko wa?ke babbar asarriyace.

wato kina masa aiki ne don ya aureki ko?Amma fa kin ban mamaki yo duk tsafin kin nan baki hango zuciyar saheeb din naki ba?toh bari inji in gaya maki wasa ya buga akanki dan kuwa saheeb baida wani burin auren wata ya mace a duniya face ni,hala yay amfani dakene kawai danya cimma muguwar burin shi akaina..amma fa bance ki yarda dani ba sede zanso ki binciko hakan dakanki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button