FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zubewa awajen najaha tay, tsoron wasime fall cikin ranta ta tuma akasa taci kukanta ya ishe ta sann taja kafafunta ta isa gida,anan ma tana isa ta zube a tskar gidan su tana rabza kuka Can saiga maman ta ta fito daga wanka akanta ta tsaya da sigar mamaki tace ke najaha Waime ya sameki haka kiketa kuka wani abu ya farune?

Cikin bori da kuka ta juyo tace mama ba wasime bane tay min korar kare a gidansu Cewa take wai nazo ina musu mulki da karya shine tajani har waje ta koreni korar kare tace wai karna ƙara xuwa.

Kyabe baki maman tay ta ce “ita din ne ta gaya miki haka…gyada kai najaha tay cikin kuka,”murmushi maman nata tayi snn tace ke da Allah share hawayenki ki tashi mu shiga ciki waye kuma wasime da har zaki kyaleta zo muje Ai inta san wata bata san wata ba,,wata rana tana zaune haka zataga an kawo ki a matsayin amaryan yayan ta anan ne kuma zataga bakar mulki,jeki dauko min wayata kizo kiga wani abu itace zatasha kunya yau Intaga yayanta ya dawo dake gidansun dakanshi kin zauna daram, sai inga kuma ta inda zata kara samun daman koraki.

Share hawaye najaha tahauyi tanajin dadin abunda mamanta take furtawa,zcyarta cike da karfin gwiwa ta shiga daki ta dauko mata wayar ta kawo..

Scrolling tay zuwa tex messsage ta bude wani
Unknwn number daya turo mata da sakon lambar wayar taher

Copyin number tay ta mika ma najaha wayar tace wannan lambar wayansa ne kiyimin saving da sunan sa anjima kadan daf zai dawo kituna min saina turamai sako amma zanyi masa kamar kece kika rubuta kinji?.

Cike da mamakin salon mamn nata tace mama nikuma?to me zakice masa kenan..mama karkiyi abunda yay taheer zai ganomu kinsan shi ba baida mutunci wallh

Dariya maman ta saki cikin tsareta tana cewa kibarmin wannan yata
Kedai tashi ki shiga daga ciki ina zuwa yanzun nan zanzo in sameki sai mu rubuta saƙon tare.

Najaha batace uffan ba ta mike tayi ciki jikinta a matukar sanyaye

A fannin wasime kuwa Komawa cikin gidan tay tana tafiya fuuu kamar zata tashi sama, ranta ya mugun baci,a hargitse ta shigo bata tsaya koina ba direct ta wuce kitchen tahau yin firo da abubuwan da najahar ta sissiyo tanakaiwa waje

Abun baimata bama ta kwashe kayan duka taje ta watsasu a dustbin ranta ya baci sosai sai tanajin kamar ma ta tsane ganin fuskan najaha na har abada.

Bambami ta dingay ita kadai tana cewa
Yar iskan yarinya dan taga ina son koyar abu a wajenta ne shine zata na rainamin wayo tana hadamin munafurci tana wani bani oda nida da gidan mu?kut man uba lallai ma najaha ta balain raina min wayo taci kasuwarta akaina,amma wallhi saina nuna mata cewa badaga kauyen yaya kare na fito ba..nima ai na iya karya da munafuccin…tsaki ta dingaja tana huci dan wasime akwaita da zazzafan zuciya da riÆ™o.
Har wani tukikin haushin kanta takeji da tunda can bata dauki wani mataki ba tanamai jin mugun nadaman jawo najaha.

Duk tarasa me zatayi dan zuciyar ta ya dan sassauto yay sanyi tsintsiya da mopper ta dauko kawai ta Kara tsaftace gidan ko ina yay tsaf snn ta fetsa ma gidan turare.

Can anjima da ranta yadanyi sanyi sai ta dawo kitchen din ta fere doya ta tafasa snnn ta daka tayi musu wani hadadden brown yam balls mai flaked fish sann ta dafa yellowshi fried rice dinta dan dai Ta soya chicken wings
Din daya rage a frdge ta dora akai tay zobon dayaji kayan qamshi ta zuba a glass jug kominta ta kammala on time.

Shirya komi tay akan tray snn ta kawosu kan dinning table tay arrangin g dinsu neatly snn ta koma sama dakinta tayi wanka ta fito taxauna abakin gadonta tana bitan karatu.

Wajajen karfe hudu da rabi na yamma taher ya dawo gida dakinshi ya wuce direct sabida ya bakaramin gajiya ya kwaso ajikinshi ba da kyar ma ya lallaba yay wanka snn ya shirya kansa tsaf cikin wata casual wear baki da fari ya saka simple takalmi
Na yawo a tsakar gida Yana kammala shirin sa ya dosu falo dan yau bakaramin yunwa yakeji ba,fitar safe yay baiko karya ba kuma harynzu bai samu daman sa wani abu wa cikinsa ba

Tafiya yakey adan gajiye yana tuno ababen da najaha ta rubuto masa a waya dazun data turamai tex message da wata bakon lamba,haryanzu yanajin mamaki yadda najaha ta same lambar wayarsa yasan dai basa haka da wasime,ce masa tay wai wayar na maman ta ne,dama ta rubuto ne kawai ta gaishe sa snn ta sanar dashi cewa tay masa girki mai dadi a gida Amma ita yanxu haka bata gidansun,wai sunje anguwa da mamanta ne sai gobe zata xo.

Mamaki yasa shi baiko yi replying tex din ba kawai ya basar yabarsa a matsayin shirme da son cusa kai irin na najaha

Sumtimes duk yakan dauki zumudi da rawan kan najaha a matsayin gigin yarinta da fallin balaga.
Shidai Haryau baitaba daukar abubuwan da takeyi akansa da wani mummunan fassara ba.
Daga ita har wasimen kallon yara yakey musu
Shiyasa Duk wani abunda takeyi din nan shi sam baya gani,is like tana left ne shikuma yana right da tunanin shi,a duk tunaninsa shakuwace irinta kawancen yarinta yasaka wasimé ta sake ma najaha ragamar komai har haka,thinking of dat yasaka shi ya bar falob ya haura sama dakin ta,ahankli ya turo kofar dauke da sallama abakinsa,hango yay acan bakin gado tana famar karatu,ajiyar zuciya ya sauke snn ya karaso ciki,suna hade ido cikin sanyi murya ta durkusa har kasa ta gaishe sa,amsa’ata yay a tsatsaye snn yace ashe kawarki ta tafi gida yau da wuri ..ta rasa daga ina yasan da labarin hakan, a hankli tace masa eh ta tafi.

Yace okay dats good
…toh ina abincin da tace ta girka din pls get down and serve me im xtremely farmished .

A hankli cikin bugub zuciyq wasime ta dago kanta da wani irin sigar mamaki ta dubeshi jin ya furta wani abu kamar almara..”girkin datayi?yaushe najaha tay wani girki…abun saiya daure mata kai ya kuma darsa ma zuciyanta wani rikitaccyar fargaba.

Hmmmm kawai tace acikin zucyarta tana mai karkada kanta,batace mai uffan ba ta tashi ta fice a dakin ya bita da kallo,direct tayi kan dinning area ranta na masifar tafarfasa taciki tahau serving dinsa abincin fuskanta a turmushe tanajin kamar ta fashe da kuka koda zataji sanyi aranta.

Tun daga can ya tsaya yanata kallon ta,ganib sauyin yanayi atattare da ita,She look dull nd gloomy yanayinta da fushi fushi da bacin rai

Tun bata kammala ba ya karasa saukowa yana zuwa ya zauna akan kujera snn ya dauk spoon ya rike A hannunsa yana satar kallonta.

Jug din Zobo mai sanyi ta dauka ta zubamai a kofin glass snn ta tura gabansa ta juya a hatsale zata kara da gaba.

Hannunta taji an riko badan taso ba ta dan juyo tana kallon sa,jikinshi ne yay snyi dayaga yadda kwayar idanunta ya cike da fushi

Ya basar yace And where r u upto Nace miki kibarnan ne?

Shiru tamasa bata amsa ba,sake hannunta yay cikin jan tsaki ya saka spoon dinsa acikin abincin ya deba yakai bakinsa ya faracin abincin cikin nitsuwa…

Sai dayaci kusan rabi snn ya juya ya kalleta,ganin haryanzu tana tsaye akanshi bata motsa ba kuma bata sake fuskanta ba,girgiza kansa yay cikin kyabe baki…”ciki ciki yace ai bansan kin dawo dogari ba,ko zaman ma sai ance miki kiyi…cant u just do things for ursef ?wato ke komenene bazakiyishi dan kankiba har sai angayamiki kafin kiyi..

Ta juyo tana tura baki tace”Yaa toh me zan maka,naga na tsaya bakacemin komi ba nifa karatu nakeyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button