FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Suna isa wajen wasime taja ta tsaya tana kallonshi,babban baho ya saukar ya dauraye ya saka abakin tap ya kunna ruwa yana zuba aciki,agefe ya lalobo omon so klin mai qamshi ya zuba acikin ruwan,yana kaiwa half ya kada snn ya kashe tap din yanemi waje ya zauna ya jawo bahon agabansa..

Wani matsiyacin harara ya bita dashi..batare da yace mata uffan ba tasha jinin jikinta ta kawo mishi kayan da bedsheet din hawayen tsoro ya gama wanke mata fuska

jikinta duk na rawa rawa a mugun tsorace ta mika masa,wani difff diff ruwan hawayen nata ya diga masa a hannun wani fauce kayan yy da karfi snda ta razana taja da baya …cikin zaro mata ido da comanding voice dinshi dake nuna isa da mulki yace “ki goge wannan abun kafin na wanka miki mari a fuskanki”..nace ki goge hawayenki kimin shiru ko?.. cikin sauri ta goge hawayen tas ta tsaya a tsaye kamar soja babu abunda takeyi sai jajjan zuciya,jikinta na rawa kamar mazari…

Tsayawa a bayansu Bilti tay tanamai lura da su.
Ta tuna yace mata karta kara shiga harkansa.
Kuma tafi kowa sanin halayarr taheer sarai,Sumtimes he can make her feel like she is nothing musamman in ransa yay matukar baci da ita..but still she can deny d fact dat koma meye zai faru baxata taba iya kyalesa ba yana abunda yaga dama ba domun kuwa kamar dan data haifa haka take jinson shi acikin zuciyarta.

Tausayin wasime ne ya kashe mata jikinta sosai tarasa ta ina zata fara tsoma musu baki.

Tsoma kayan yay acikin ruwan kumfa ya jika snn ya daga ido yana kallonta,sam bata iya hade idanunta dashi, atake ta nitsu tayi narai narai kamar wata yar baiwa ta sunkuyar da kanta can kasa tana sauke ajiyar zuciya..da gefen idanunshi ya harareta “Tun yaushe kike fitsarin kwance ko dan tsabar iskanci akan gado na kawai kikaga daman yi yau”…shiru tayi..ina miki magana kina min shiru ina wasa dake ne..?

Idanunta cike da hawaye masu ban tausayi ta dago zata gyada masa kai caraf suka hada ido saita tuna yace bayason hakan dakyar ta tattaro nitsuwarta muryanta na rawa sosai tace “..wallahi, tallahi na rantse…”shut ur mouth! Ya daka mata tsawa ya mike tsaye cikin masifa

Wannan rantsuwa duk na nemene ne?waya koya miki rantsuwa..just answer d damn question,nace tunda kikazo gidan nan kike fitsarin kwance koyaune kawai kikayi sabida kin rainani?

A rikirkice tana fidda sabbin hawaye tace a’a.
A’a Dama…dama…kuka ne yakeson kufce mata tay saurin toshe bakinta

Tsaye ya dada mikewa yana kallonta tayi saurin ja da baya a tsorace,tana cewa,zan fada zan fada
Kayi hkri wallhi zan fada

Banace kidena min rantsuwa ba.ke Na sakejin wallahi abakinki saina wanka miki mari.

Hawaye ta dinga saukewa duk jikinta yana rawa,motsi tajiyo ata bayanta ta juya tana hade ido da bilti ta ruga a guje taje ta rungumeta tare da sakin wani tsorataccen kuka

Jikin bilti yy sanyi idanunta sun cikka da ruwan tausayin wasime
Shafo kanta takeyi sosai tana rarrashinta kiyi shiru mama na…kiyi shiru abunki…cikin kuka gwanin tausayi tace bilti dan Allah ki cece ni. Nifa ba da sanni na nayi masa fitsari ba kema ai kinsani bana sonyi,yo ba shine yake zuwa dakashi ba,nifa bana so,banayi a garinmu ..ai nayi nayi na dena anan dinma amma yaki…wayyo Allah na na higga uku…bilti ki cece nim

Matsowa kusa dasu yay yace…”Are u done?
Dada kankame bilti yay
Babu kunya ayanayin sa yasaka hannu ya fincikota daga cikin bilti wani gigitaccen ihu ta sakar masa ya tattareta

Atake ta rude tana ihu tana neman fita hayyacinta.

“wayyo Allah na bilti ki cece ni,wayyo na higga uku,anono na anono na,
ÆŠahiru dan Allah kayi hakuri karka kasheni,É—ahiru kayahakuri Wallahi bazan kara ba.

“Bakinta taji an make da karfi saida yay jini..,cikin daka mata tsawa yace”kikace mene? Waye É—ahirun ki?Nace waye dahiru?

Matsowa bilti tay zuciyanta duk ya raunana da tausayin wasime

Taheer dan Allah kabita a hankli.

Dangwala wasimen yay a kasa batare da ya kalleta ba ya daure fuskansa tamau yace “babu ruwanki”.ni ki kyaleni.

Hannun wasimen yaja a sukurkuce ya tura keyanta zuwa inda yake wanki Ya tsayar da ita acan ta gabansa yana kallonta cikin harara

Neman waje yay ya zauna agaban bahon inda zai fara wanki snn ya umarceta data saka gwiwowinta a kasa snn ta daga hannunta sama

Jikinta na rawa ta aikata hakan…sai ruwan hawaye datake saukarwa
Hararta yay snn yace
“Close ur eyes..”
Batagane meyace ba.
Ahnkli cikin sanyin jiki Bilti tace yace ki rufe idonki”. Da sauri ta rufe idon..
Wani shiru wajen ya dauƙa ayayin da ya shiga wanke bedsheets din kansa a kasa baiko sparing one minutes danya dubi yanayinta ba.

Hakama bilti datake tsaye,zuciyanta duk ya mutu da tausayin wasime,she just cant find the caurage to leave her acikin wannan hali

Haka wasime taci kneeling hannayenta suka dau tsami,gaba ki daya idanunta rawa sukeyi gashi tasani bata isa ta budesu ba.

Ahaka har ya gama wankinsa ya dauraye yaje ya shanya a clothline snn ya dawo yamaida komi mazauninsa a yadda ya samu….

Plastic chair ya jawo ya zauna ata gabanta ya harde kafafun sa daya akan daya snn ya zaro wayarsa yacigaba da latsawa,bilti harta gaji da tsayuwa ta wuce jiki a sanyaye ta koma cikin gida tana hawayen tausayin wasime.

Yarinya ga yunwa,ga rashin lpya amma ace taheer baiyi duba da hakan ba?ji tayi kamar ta dauki wayarta ya kira mahaifiyarshi ta sanar da ita abunda ke faruwa,saidai kuma itakanta tasan yadda suke sangartashi ba lallai bane hakan yay wani amfani,domun kuwa iyayensa basa amincewa su amshi laifinsa haka kawai sumtimes harsai sungani da idanunsu ko ya aikata agabansu snn su amince
Barinma mahaifiyarshi datake tsoron bacin ransa,sam bata son taga danta ya bata rai fadama daurewa kawai takeyi tamasa amma badon wai tana so ba.

Daga waje kuwa wasime
Tagama galabaita da yunwa ,jikinta ya dau wani irin zafi sabida kuka da tashin hanklin datake ciki…tsabar taji babu dadi ajikinta bata san sanda tafara bashi hkri ba..da kyar ma ya hakura ya kalleta…snn ya umarceta data mike tsaye .”a dangale ta tsaya kafafunta da hannayenta duka suna mata wani irin nauyi da tsami.

Yace zaki sake fitsarin kwance,cikin kuka sosai tace A’a Wallah tallahi na dena

Tsaye ya mike kamar wanda zai sharara mata mari “menace miki akan rantsuwa”..sauri tayi ta kama bakinta muryanta na rawa tace “kayahakuri shima bazan kara ba.

Kunnenta ya kama ya ja ya kuma kafe ta ido ita kanta tasan bata isa tayi gigin yin wani kuka ba,a tsomare tayi tsamm da jikinta tana jan ajiyan zuciya yace “ke bakiji kunya ba katuwa dake kinai ma mutane fitsarin kwance?,wani irin sunkuyar dakanta tayi can kasa tanajin wani iri iri sosai acikin zucyarta gaba daya kunya da damuwa sun dagulamata kwakwalwa she is feeling soo awful abt her self…jikinta yay sanyi bana wasa ba.

Yace “toh daga yau sai yau,in na kara ji ko na gani kina fitsari saina miki shegen duka….
Snn na hanaki fitowa waje ko zuwa wani waje,daga yau sai yau babu ke babu saheeb kinji menace ko bakiji ba?zuciyanta a matukar karye tace naji,”yace menace?..dagowa tay a hankli cikin muryan kuka tace “kace karna sake fitsari, kar na fita waje snn babu ni babu yaa saheeb “yace good…
Toh ki aje wannan a kwakwalnki kinaji na ko?
cikin hanzari ta gyada mishi kanta snn tace eh naji..sake kunnentan yy ya tsaya yana kallonta snn yace “akwai sa’anki a gidan nan ne?..a hankli tace a’a babu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button