FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ita dai tasan Hanklinta yana kwanciya inyana mata nasiha akan datay hakuri akan tafiyar da bilti tay tabarsu,duk da haka wasime kullum sai tay masa kukan banza.
shiyasa gabaki daya ciwonta ya fiye tashi akai akai, shi tun anan ya fahimce cewa Yarinyar tana da riƙo da kuma zuciya mai zafi.
saidai Kuma kowani salonshi nayin tasiri mai girma acikin zuciyarta.

Wani bin har mamakinsa take sha acikin ranta dan Bata taɓa tsammanin
Ya iya dadin baki da lallashi ba har saida ta shiga wannan yanayi
,kowani dawowar sai ya kawo mata soyayyen kaza ko grilled fish da juice ko wani shawarma koma ya siya mata kala da kala na vanilla and chokolate ice creams da sauransu.

Inya kawo abinci taci a washe gari haka zai tashi tun asubahin farin duk gudun wai kartana taɓa ruwa kar ciwonta ya tashi,haka zai daure yay mata wanke wanke,yay moping snn ya wanke kayayykin su yay mata komi na aikin gida.
Bai iya komi ba kam amma dan dole ya koya makansa.

Kwana biyu Sam Baya barinta tana aikin komi musamn aikin daya shafi ruwan sanyi da kuma ƙura,daga ta zauna shiru sai kaga tana karatu sai kuma kwanciya da kallo,ahaka har saida ciwon nata ya rabu da ita ya lafa mata sosai ya dena tashi akai akai.

Kafin sati ya kare Kukan banzan Ma duk ta rusuna ta dena yinshi,duk dama haryau zaka ganta shiru shiru sam bata walwala sosai kamar kwanakin baya da suka wuce

Ranar lahadi da taheer baije koina ba bayan ya sissiya mata kayan dadi taci ta koshi,tana tsaye tana kallonsa ya tsaftace gidan.sann yasata taje tay wanka daga nan Suka dan fita gari tare,.

yau har barracks dinsu ya zaga da ita,suka kai har wajen hostel din female soldiers wajen wata course mates dinshi elizabeth daya fiye taimaka mata acikin exams hall in abubuwa suka cirke mata..
tana respecting din taheer sosai sabida bata taɓajin ya bazata ko ya tona mata asirinta awani waje ba.

Sau daya ya taɓa cin karo da ita tanayiwa co inmates dinta kitso kamar da wasa yace mata zai kawo kanwar sa tayi mata aikuwa ta takura masa harsaida ya mata alkwarin zai kawo wasime ranar sunday.

Sosai tay murnan ganin su wajenta cos she have been looking for a slightest way to repay his kindness towards her,barracks wasnt a fun environment,sojoji riƙeda bindigogi da ta dinga cin karo dasu yasa duk ta tsorata tazama shiru shiru,duk yadda suka so wasime ta saki jikinta da su ta kasa yin hakan Tsabar jin tsoro da fargaba,haka taki kowa ya taɓa mata kanta ta dinga narke mishi tana bori wai saida ya mata kitson dakanshi, haka ya cire girman kai ya zaunar da ita awajen ya tsefe mata kan ya barta ta taje dakanta.Shidai baisan ya ake kitso ba,wayo yy mata ya sabule jikinshi ya fita da waya a kunnen sa yace mata ana kiransa ne yanzun nan zai dawo.

Da kyar ta tsaya su elizabeth suka wanke mata kanta tass
Dan gani take kamar cinyeta zasuyi

Awaje wajen gindin bishiyar hostel za’ayi kitson,sai can da kan wasime ya bushe snn soldier elizabeth ta fito waje tare da ita da wani babban tabarma,a under shade din gaban hostel dinsun ta shimfida tare da ababen yin kitson ta masu kyau da mayukan gashinta masu qamshi da tsada.

Wasime bata ce komi ba cos yadda tay da fuska kamar wacce ake shirin rataye ta yasaka suke ta binta ahankli..duk hanklin ta ya tashi da haryanzu bataga dawowar taheer wajen ba fusknta a takune yake kamar wanda aka tabata kadan zata barke da kuka.

Wani biscuits mai madara matar ta kawo mata bata ko ci ba ta rike a hannunta snn aka soma cancaÉ—a mata kitso ,Wata shegiyar two steps mai zubewa ta gaba ta tsala mata shi mai zig zag style takuma yishi kanana kowa ya wulga tawajen sai ya tsaya yana yana kal’on kan wasime cikin cewa wow wat a beautiful hair style.

Wasime tana da cikar suma, gashi natural ne kuma baki wuluk,duk da gashinta baida wani tsayin azo agani amma bakaramin kyau kitson nan ya kankaro mata ba.

Kowa ya gani saiya yaba
Ta samu kyauta sosai ahannun yan matan da suke crushing akansa acikin hostel,tunda akaji cewa kanwarsa yan mata maso hyping dinshi suke haba haba da ita,haka suka dawo gida da hilimi guda na kayan kwamulashe harda tukuici na kudi

Ga elizabeth ma bata bari sun rabu haka nan kawai ba saida ta dafa musu haddadiyar jollof din spaghetti wanda ya soyu yaji mangyada da uban tsokokin kifi.

Taheer harya rasa bakin godiya gaba daya ma kunya abin ya dinga ba shi…

Abincin suka ci da wasime a gida sukayi dam,yau kusan kwana yay yana kallon kitson nan,dan bai taba sanin iya kitso kawai yakan fidda kyaun mace ba sai yanzu.

Bayan kwana biyu kominsu ya dawo normal
Wasime ta koma kan normal activites dinta na gida.zancen bilti na zuciyarta amma kwana biyu zafin datakeji a zcyrta yadan ragu.

A fannin najaha kuwa kullum kirga kwanaki takeyi domin ta samu ta fara zuwa gidansu.

Zuciyar wasime ya riga ya fara sabawa da na taheer,yana fita a gidan saita somajin wani irin damuwa tana dagawa kanta hankli.

Ana washe gari najaha zata zo ta sanar dashi,baice mata komi
Dan baiya son yanzu yana takura ma rayuwanta gashi hutun ta na schl yay kusan karewa Allah Allah yake yagama exams dinsa domin ya samu cikakken lokacinta a wannan lokcin.

washegari sassafe kamar yadda ta tashi jiya haka yau ma tayi,tun daga kan dakin ta ta tsaftace yy fes tay wanka snn ta fito.

wani riga da wando ta saka na pakistan ta sauƙo kitchen ta shiga haɗa musu tea dan tana tunani at any moment najaha zata iya shigowa.

Tsugunowa kasa tay agaban drwer tana bude buden cupboard tana dudduba abubuwan da aka ajiye aciki can taci karo da flour mai yawa an killace shi a transparent container.

Yar yatsanta taciza yau Ina ma da ace ta iyayin panke aida ta kwaɓa musu sunci da dan shayinsu ,tunanin yadda taga akeyin ta tsayayi thinking of weda to try it or not,a jikinta taji kamar ana kallonta daga bakin ƙofa,a tsorace ta farga ta juyo ta kalli bakin ƙofan jin motsi motsi wani irin ƙara ta saki ta mike a tsure zata bi ƙofan baya ta fita ta gudu Tana waigowa kadan sai ta ganshi a tsaye bakin kofar ya nannade hannunshi akirjinshi yanata kallonta.

Tsayawa tayi kirjinta na bugawa hannunta sai rawa rawa yakeyi dan bakaramin tsorata tay ba

Acikin nitsuwa ya ƙaraso cikin kitchen ɗin yayi maza ya kamota jikin shi, lkcin babu abinda jikinta yakeyi sai rawa gashi ta kasa dena kallonsa

a hankali ya dada jawota jikinshi ya rungumeta tsam ganin ta tsoratan sosai, patting bayanta ya shiga yi tay wani lamo yana raÉ—a mata sorry cikin kunne..

Wani lafewa tay ajikinshi sosai tana sauke ajiyan zcya ahankli, har sai da yaga rawan da jikinta keyi ya ragu sannan ya sassauta riÆ™on da yayi mata yana kallon kyakkyawan fuskarta da hawaye ya ziraro,kitson ta daya zubo ta gaba yana dan rufe mata gefen ido yasaka hannun shi gently yy gefe dashi yace”ina zakije da kika sa gudu?ko kamanni na ne yau ya canja miki?

Shiru tay bata amsa shi ba ta maida kanta ƙasa a hankl yatsanshi yasa yana share mata hawayen da suke bata mata fuska

Dan karamin bakinta ta turo gaba snn ta É—ago kanta ta kalleshi da sanyin murya tace”
“Nifa ba tsoro naji ba,cemaka zanyi ina kwana.?

dariya maganartan yaso ya bashi amma ya dake tare da dago fuskarta da ta saukar yace” im fine!jiya ma daidai wannan lkcin kika tashi?gyaÉ—a mishi kai kawai tay.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button