FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Agaban maimunatu da mahaifinta garba maye komi ya faru,suna kallon wutar yanaci balbal suna dariyar mugunta tamkar ma zasu saka ruwa a ƙasa susha sabida su suka shirya komi ya tafi cikin samun nasara.
Duk wani abun da suka hanɗame na gonaki da dabbobi da rumbunan abincin hassan da badiatu dashi suka cikawa rigarsu iska tunma kafin mutanen anguwa su hanƙara da abunda suka aiƙata.

Daga kauyen ringin gana kuwa matar datake riƙe da jaririyar su ganin har safiya batagansu ba yasa jikinta yay mugun sanyi,dan tamkar ɗanta na cikinta haka takejin aliyu dik dama bata haifesa ba rainonsa kawai tayi, xuciyarta sosai ya bata cewa tabbas wani mummunan abune ya afku dasu wanda yay sanadin rashin dawowarsu ga ɗiyarsu, dan dama tasan da wuyane, su iya fidda kansu a ƙaidin shaharren matsafi kamar garba maye da shaidaniyar ƴarsa anmuna.

Bayan Æ™wana bakwai da afkuwar komi matar nan ta dauÆ™i jaririyar nan acikin mafi sirrikan lokacin dare suka yi hijira ixuwa garin jos,inda ta nemi haya acikin wata Æ™auyen makiyayan fulani ,anan tay zamanta ta raine Wasimé,har ta girma. ranar da wasimé ta cika shekaru 9 a duniya anan ta Æ™ara hada kayansu a jaka da zimman kaita inda xatayi rayuwarta na dindin din…..

SHARE SHARE PLS.

ATAIMAKA A SASSAKA SHI A GRPs Lovely fans💯💕🥰💃
7/25/22, 19:19 – Kawata: FITAR RANA…
……faduwarsa

BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.
2️⃣
Tun sassafe suka shirya suka bar garin jos suka dau hanyarsu wanda tadauÆ™esu tsawon awanni uku zuwa hudu ana tuÆ™asu,Jan Æ™ura irin nakan titin Æ™auye wanda baiga darajar samun gyara ko kwalta ba shiya bule jikin bus din gwamnati daya sauÆ™esu a baki titin wani kauye acan kusa da garin kaduna ana ce dashi mararrabar saminaka, masu saida fresh fresh kayan lambu da fruits sun cikke bakin titi anata hada hadan kasuwanci da saida da sayarwa,anan motar tasu tsaya ta sauÆ™esu suka sassauka kusa da wani mai saida karas da ganyayyaki,tafe wasimé take cikin nitsuwa dauÆ™e da jakar kayanta tana bibiyar matar data zame mata tamkar uwa da uba a bainar duniya wacce take Æ™ira da innono kotace mata anono,anma asalin sunan matar Fatsuma,saidai anfi saninta da hajiya fatu mai tuwo sabida tsohuwar sana’arta ne dafa abinci tana siyarwa danta samu kudi,Allah ya dafa mata ta shahara a manyan ma’aikatar gwamnati da manyan makarantu a matsayinta na chief cook,wato shugaban masu kula da harkokin girke girke na manyan makarantu da ma’aikata,tun tanacin kuruciyarta take wann sana’ar har shekarunta yaja ta tsofe, fatu mai tuwo farace sol tana da murmurarren jiki,itana kowace,kowa yasanta da halayyar son Æ™ulla zumunci da kyautatawa, da iya taimakon mutane, da son tallafawa naÆ™asa da ita koda kuwa bata sanka ba,fatu bazaurace mijinta ya rasu,amma tana da danta kwalli daya tilo datake kiransa da suna”Qasimu” wanda aynxu har ya kammala karatunsa na jamia yay kudin rufin asiri yay aurensa a garin kaduna,inda ya ajiye mata daya da dansu kwalli daya namiji.

Tsawon lokaci tabarsu acikin aminci Suna rayuwarsu acan ita kuma ta shiga uwa duniya yawon gwagwrmaya akan abunda ta saba na taimakon yan uwa marasa ƙarfi da galihu da kuma sada zumunci da dangi da abokai.

Halayyarta na son mutane ya jawo take da mutanen data sani bila adadin, ta kuma shaÆ™u da dumbin mutanen ta akusan duk inda taje,bata da wani alaÆ™a ta jini kona yan uwantaka da hassan mahaifin wasimé,iyayensa yan gudun hijirane daga Æ™asar somalia,baban sa da mamansa sun gudo ne,lokcin da tsohon cikin sa suka yada zango agarin ringin gani,da sukazo garin bamai kallonsu bare ajega taimakon su,wata rana kwasam saiga fatu.anan ta tsincesu a bakin gaÉ“a lkcin ciwon naÆ™uda ya turneÆ™e mahaifiyar hassan,ita tayi ruwa tayi tsaki ta taimakesu har aka haifeshi lpya, aka samai sunan sa Aliyu haidar,sukamasa inkiya da hassan.,sosai iyayen hassan suka shaku da fatu,alokaci Æ™alilin suka saba,suka dawo tamkar wasu yan uwanjini sabida yadda tariÆ™esu take taimaka musu da zuciyarta daya take kuma taimakonsu da dukiyarta,Bayan watanni sha shida Allah yay ma mahaifyar hassan rasuwa,mahaifin sa kuma yabi bayanta randa ta cika kwana arba’ain da rasuwan,fatuce ta dauÆ™i dansu Aliyu ta cigaba da rainonshi tamkar danta na cikinta harya girma yay aure ya auro matarsa badiatu.Saidai izuwa yau kuma ga yadda qaddara ta juya tarihin rayuwarsu komi ya zamto tamkar wani mafarki.

Hannun wasimén taja suka shiga wani madaidaicin gida ginin block wanda baida wani tazara da bakin hanyar da suka sauÆ™a,kai tsaye innono ta kutso kai cikin gidan da sallama a bakinta”Asallama alaikum masu gidan suna nan kuwa? wata dattijuwar mata ce a tsakar gidan tana Æ™alkale saman cementi da tsintsiyar laushi a hannunta, jin muryan innonon yasata dagowa da fara’a akan fuskanta tana cewa..wa’alaikin sallam oyoyo oyoyo maraba da xuwa anononmu,barkanku da isowa…innono ta sauÆ™e ajiyar xcya”laraba ina mutan gidan haka naji koina yadau shiru kamar wani makabarta,tana kkrin karban kayansu tace suna nan sun dan zaga yin ta’axiyane a makwafta amma yanzu zasu dawo, kushigo ciki kuzauna kusha ruwa,lale marhaba da zuwa..daga fadin haka ta wuce dakinta agaggauce cikin sauri ta aje kayansu sann ta dawo hannunta dauÆ™e da babban tabarma,akan cementin kofar dakinta ta shimfida musu suka zazzauna,kujerar tsakar gida taja itama ta zauna
“Sannu,Ina kwana? Wasimé ta furta da sanyin muryanta mai cike da alkunya tana satan kallon matar

Matar tay murmushi ta dubeta ganin ta kyakkwaya saitaji ta shige mata har cikin ranta a bugu daya, tace lpya lau yan mata masha Allah,daganan wasime bata kara ce uffan ba ta maida kallonta Æ™asa ta kuma nitsu sabida bata taÉ“a xuwa wani waje ba arayuwanta duk sai tanajin kanta daban,matar tana satan kallonta tana washe baki cikin rada tace,uhumm innono kar ace nayi azarbabi karde wannan Æ´ar itace amaryan namu?Kyabe baki innono tayi murya Æ™asa kasa tana murmushi tace”Kede laraba da son jin gulma,aikya barni in huta kafin a tsunduma cikin sana’a ko,dariya matar tayi mai dan Æ™ara”kinsan goshi amare baya boya,masha Allah yarinya shar a Æ™auyen fulani wann ai amaryace,innono ta kyabe baki”..ni ynzu ina naga ta gulma yunwa fa nakeji ni banko Æ™arya ba ,laraba ki hanzarta ki kawomin abinci kyaji duk wani shauran bayani daganan,miÆ™ewa matar tay cikin tsokanarta ta wuce kitchen ta soma kkrin kawo musu abun taÉ“awa,lafiyayyan tuwon dawace da miyar kuka taji manja da busasshen kifi yanzun nan dama ta kwashesu ba ako yi rabo ba,a dan tray din silver ta saka musu tare da ruwa snn ta ajeshi agabansu
,nan da nan da innono suka sauƙa akai itada wasiménta datake cin abincin a hankli kamar bazata ci ba,kafin nan mata, da yan yara yara har sun daddawo sunciƙƙe gidan da surutansu,tray tray na tuwon nan an sakoshi agaba anajan lomomi
Ana hira,yara yan fici fici irin bini in bika nan kawai in ka kirga zasu iyakaiwa ashirin,iyayen ne a tsakiya su hudu casss kowaccce ta haÉ—e uwar ciki da teba, kallo daya zaka musu kasan Æ™unika akeyi agidan gadan gadan,banda sa’oin juna da wanda suka ba juna watanni akwai wanda aka turasu Æ™aratun allo acan yobe state,”Anono anono surutu ne da hatsaniyan tade tade ya cikke tsakar gidan,manya da yara Kowa na burin ta saurareshi,sai can da magidancin gidan ya shigo sannan kowa ya nitsu aka dan sarara daga nan Wani shiru gidan ya dauÆ™a, dan Kaf yaran gidan sun watse kowa ya fita neman nakai,aka bar manyan sukadai agida tareda wasimé data laÉ“e agefen innono tayi shiru tanajin tattaunawarsu wanda mafi akasari akanta ne.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button