FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kalilin lokacin suka tsaftace kansu da diyarsu wacce taci sunanta..”WASIMÉ”
Ma’ana wani kyautar karramawa mai girma kuma ta musamman daga wajen ubangiji,
kalman “wasimé” yana nufin “the mercy of God”, as distinguished from His justice;a divine love or pardon,a state of acceptance with God.

Tare da dayar ma’anarsa dayake nufin “Sa’a,(fortune)or someone who helps odas selflessly,divine beauty or lets say graceful nd preety..

in greek philosopy wasimé is a historical name of 3 beautiful sister goddesses
(Aglaia,euphrosyne,and thalia) represnted by ancient writers for apollo nd ofteners of venus and are regarded as inspirers of good qualities like wisdom, love nd social spirits.Kalman wasimé har ila yau kalmace mafi daraja ga masarautar england as thy often refer to their dukes nd dutchesss with its kinds.

Sunan da suma suka zabarwa yarsu kenan sabida su nuna wa Allah godiyarsu,Saidai ciwon ciki da xubar jini shiyaci ƙarfin badiatu ayanzu,
babu yadda malam hassan baiyi dan subar wajen akan lokci ba amma ina duk kkrinsa yaci tura gashi malam ya gargadesa da suyi maza subar gidan kafun anmuna ta hankaro
,Saidai akowani dakikanln wucewar lokaci jikin na badiatu dada rakwabewa yake daÉ—ayi…”yarinyarsu wasimé da suka nannade acikin zani tana baiwa nono ta fincikota a hankli tana kallonta idanunta na fidda kwalla ta damka masa ita a hannunsa ,É“ari hannunta yake alamun ta jikata muryanta na fita a rarrabe cikin wahaliyar
Tace”Ali…Al…iyu ka tsira tare da wasimé,kayi sauri..sauri kuje kakaita matsera sann kadawo gareni…Aliyu ka..kkaje bamu da lokaci..kar mumm..mujefa rayuwar yarmu da batasan komi ba acikin ukubar maimunatu,kanaji na kuwa Aliyuhhhh?..Ya rasa abun da zaice mata sai kukan zuci dayake rabzawa,ahnkli ya rungume Æ´arsa a kafadun sa hannunsa saÆ™ale dana matarsa yana murzawa a hnkli
duk jikinshi na rawa,can ya miƙe tsaye kamar an tsakureshi yanata kallonta da raunatattun idanunshi wanda sukayi naso da kaunarta yanaji kamar zai hadiyeta,wani wawan shauki ya kuma yunkuro da shi ya gurfana ajikinta kamar sabon mahaukaci wanda baiya cikin hayyacinsa Tare da sakar mata wata shaukakkiyar runguma mai tsuna yanamai sumbatar koina ajikinta araunane
“..muryan sa a dishe yake cewa’..Badiatu kiyimin alkwarin zaki jirani kinji?…bazan daÉ—e ba wannan karon zan dawo gareki badi’atu..nayi miki alkwari rabin raina…kijirani anan kinji badi’atu na…ta gyada kanta a hankli tana sumbatar sa,wani
Murmushi mai taushi suka sakar ma juna sannan ya share fuskarsa ya share mata nata itama,nan yay ta maza ya saɓi jinjirarsu a kafadunsa ya shafa musu turaren sannan suka doshi hanyar yamma..,lkcin ana neman ƙarfe 2:00 na dare
Cikin murkususun ciwon cikin badiatu ta kasancel mai tsananin azabtarwa.

Malam hassan kuwa bai tsaya ba tafiya kawai yakey acikin jeji burinsa baifi yaga ya iso wani dan ƙaramin gari da ake ƙira Ringin gana ba.

yadda ya rungume jinjirar babu abunda yake jansa sai amon sautin murya matarsa dake yawo akansa yana ƙara ma zciyarsaa rauni da ƙarsashi.

Hudu da rabi shaura na dare ya iso ƙofar wani gidan ƙasa wanda ya samu kofar zaurenta a buɗe shiga yayi cikin sauri zuciyarsa tamkar zatay tsalle ta fice daga kirjinsa,direct kofar wani rumfa ya shiga ya kwankwasa sau daya sai gashi an buɗe kofar.

Wata matace sanye da hijabi dogo har Æ™asa,ta fito hannunta riÆ™e da carbi,da kuma fitilar obasanjo ya gaza tana mai Æ™are mai kallo cikin mamakin ganin yanayin sa..muryanta kamar na wacce zatayi kuka ganinsa da jaririya a hannu ta dada kwalo idanunta waje tace “Tubarkallahu masha Allah Aliyu har badiatu ta sauÆ™a? kun iso ne toh ina ita badia’atun take?
..gani tayi yay shiru dik ya kasa furta wata magana lkcin numfashin shi ma sama sama yakei kamar zai dauÆ™e ya rabu da jikinshi, da kyar maganan ya kufce masa bacin kuka mai tsuma da tsofuwar ta sakar ganin duk ya gigice. Aliyu lpya kuwa?a hnkli yace”umma na ki riÆ™e mana wasimé amana ni zanje in dauÆ™o badiatu a shammo!!
Umma nabar badiatu cikin ciwo…umma saina dawo!!!…”gyada kanta kawai take tana hawaye tanacewa toh toh toh Aliyu kayi maza ka jeka Aliyu Allah ya Æ™areku gabadayanku ya dawomin daku lpya.
Allah yay ma wasimé Albarka tana magana tana kuka sosai…harya juya zai bar wajen sai taga ya juyo ya riko hannayenta tare dana babyn Ahnkli yace “umma inbaki ganmu ba Wasimé takice har abada mun barmiki ita amana!!umma kiyafe min dukkan kuskuren dana aikata miki arashin sani ki kuma yafewa matata badia,!!kanta take girgizawa cikin kuka”zaku dawo Aliyu,kadena fadar haka kaje ka dauÆ™o badia insha Allahu zaku cinye wann jarabawar,baice komi ba ,tanata magana harya bar wajen bata sani ba sabida kuka mai taÉ“a zuciya da tausayinsu da ya mamayeta.

Malam Hassan ya kasa hakuri yayi tafiya bisa sawunsa aguje kamar sabon mahaukaci
Ya yanka cikin jeji duk jikinshi babu guzari amma shaukin son ya tseratar da matarsa yasa yakejin kanshi kamar su wani lafiyayyen doki,
Idanunshi da suka sauya suka dawo jajawur suna fidda sassanyar kwalla,
Babu abinda yake ambata sai Allah sai badiatunsa..

Daf Ƙetowar alfijir Allah yay isowarsa shammo ganin cincirindon ciyayi a kofar gidansa bai hanasa ƙarasawa ciki,bai hadu da kowa baa har ya iske badiatu zaune akan tabarma ta jingina bayanta da bango tana layi cikin wani mayuyacin hali,baiy wata wata ba ya dauƙeta cak ya saɓa ta a bayanshi ya goyeta da murmushi akan fuskanta ganin ya dawo mata, ta kuma san ƴarta wasime ta tsira kenan na har abada,lafewa tayi a bayanshin tayi lamo banda sunansa babu abunda take firtawa acikin numfashinta, yana kaiwa bakin kofa da zasu fita sai kofar ta kullesu kirif taciki.Tun yana kkrin budewa da badiatu a bayansa harya gaji ya sauƙeta ƙasa yay iyayinsa amma kofar sam taki buduwa ya rasa abunda yake masa dadi, jin da yay kmar ana riƙe masa kafafunsa ta baya yasaka shi ya juyo gani yay badiatu ta riƙe kafafunsa kamar mai neman gafararsa.

Cikin wata wahalliyar yanayin nishi da murya dake fitowa da kyar tace “Aliyu kashe mu zatayi..Aliyu kashe mu zasuyi ita da baba garba…kabar wahaldakan ka kaxo muyi wa Allah godiya akan ni’imomin sa daya dora akanmu,ko kasan jarabawa nadaga alamar soyayyarsa?Aliyu inaa fatan nay rayuwa ta dakai a aljanna,kai namijin kwaraine abun alfahari,Ina fatan Allah ya bamu wata kamar Æ´armu acikin aljanna, Allah ya sa muyi kyakkyawan Æ™arshe Aliyu.
Jikinshi a ragwabe ya zuÉ“e Æ™asa kanta a gurfane ya rungumeta ya kuma dukunkuneta ajikinshi suka gamutsa tare Shida ita a waje daya.cikin muryan lallashi Yace’Badiatu karki cire ranki mana ga rahman ubangiji,ikon Allah fa da girma yake wani mutum ko aljan bai isa ya dau ranmu bada san ran ubangijn mu ba,shiya fidda ibrahima acikin wuta,ya ceci musa daga kaidin fir auna sannan yonousa ya rayu bayan kifi ta haÉ—iyeshi.
To ke kuma Tsoron me kikeji badiatu?..”
numfashinta ta fetsar waje”aliyu ba tsoro nakeji ba jiki na ne yake bani cewa hala bazamu iya kufcewa wnn
Qaddarar ba..”zata Æ™ara furta wani kalman taga ya yunkuro ya rufe bakinta idanunsu cikin na juna yace”kiyi shiru karki Æ™arar da ruwan jikinki,kina bukatar Æ™arfi badiatu,kanta ta gyada sann ya kwantar da ita akan faffadan kirjinshi ta dan lafe tana maida numfashi,sunfi minti uku ahakan snn ya dagota a hankli ya miÆ™e ixuwa baki kofar dan ya Æ™ara jarrabawa koxai budu
Kalman shahada ya rinƙa maimaitawa yana ambaton Allah a fili da acikin zuciyarsa,
Bismilllahi ya furta yanamai miƙa hannunsa ixuwa taɓa mamurdin kofar,cikin kiftawar ido da bisimilla wata ƙara mai gigitarwa kamar na nakiyar bomb ta cillar dashi baya ya fado ragwab ajikin badiatun sa matacce,lumshe idunuwanta tayi tana kkrin furta kalman shahadar itama ayayin da shauran ginin wajen daya bangaro sakamakon girgixan da dakin yy ya ragaxo mata akai ya ƙarasa ta, bayan haka hayakine da gobarar wuta ta gamutse wajen suka ƙone kurmus.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button