FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kullum wasime takan ji kishin razia sosai ganin ta farasol kyakkwa ga dogon suma tasan ma dolene kawai tafita matsayi awajen shi yanzu.

saida ta kammala shanyanta tsaf snn ta taho da kumshin ledan cikin gida ta wuce loundry dashi ta kada omo yay kumfa zata jika kayan duk a tunaninta bazai wuce hankys bane ganinsu a kumshe a leda tunda dai tagansu a dukunkune a dan karamin leda tasan ba wasu kayan azo agani bane…Allah Allah take ta wanke ta je ta huta dan gajiyar datakeji kwana biyu bata wani cin abinci isashe sabida hatta keys din store dana kitchen taheer ya karba ya bama razia,bakin ciki kadai yakan hanata zuwa karba
Sumtimes ta gwammaci ta aiki malam jafaru ya siyo mata abinci a waje ko kawai ta zauna da yunwa harsai anbata key

Tana bude ledar ta soma cin karo da wasu white panties duk stain din jini ajiki yay wani abun kazanta atake tay firo dashi da uban gudu tay rushing kanta izuwa toilet ta dinga kwaza amai sosai sabida tashin zuciya.

Da kyar aman ya tsagaita
Saboda tsaya mata da abun kazantar yay a ido,da kyar ta tattara ta maishe su ledan ta kulle sann tayo waje da shi.

Hanyar dakin razia ta nufa dashi ta kwankwasa kofa kamar ana jiran zuwanta akace ta shigo ciki,tana kutso kanta gabanta yay mummunan faduwa a kallo na farko datayi ma taheer dayake zaune da guntun wando da singlet raxiar ce daure da wani dan iskar towel wanda baima gama rife mata fararen cinyoyinta ba Ta wani kwanto ajikinshi Ta makalkaleshi ganin wasime yasakata ta dada narke mishi a kirji cikin salo tana nishi nishi kamar dai yadda saheeb ya umarceta

Wasime tafara jin kamar
Kanta na kuncewa kamar dauriyar ma bazata iya ba,da kyar ta nitsu kawai sai ta cije ta tsaya agabansu,taga baiko daga idanunsa sama ba bare ya san ta shigo cikinsu gabaki daya idanunshi nakan raxiya dataketa murkususu ajikinshi dan baiya sanin metake aikatawa dashi saidai yayta kallonta.

Cikeda manakisa ta makale murya a kasalance tana cewa Sister lpya kuwa naga kin shigo mana…tana maganan tana dada dora hannunta akan kirjinshi cikin salo tana dan shafashi…lokcin wasime harta binne idanuwanta a kasa jin hawayenta na kokrin fitowa waje

Muryanta dayakeson yy rawa ta matse shi ya dawo normal a hankli cikin hadiye bakincikinta tace.”Aunty kiyi hkri na dawo miki da kayanki bazan iya wankewa ba.

Mikewa zaune razia tayi cikin gwalo idanunta waje.tace haba sister wasime meyasa?!ko dan kinga panties ne?kefa mace ce kuma Hakuri fa na baki kinga banajin dadi ne…wuyanta a langwabe ta juya ta kalle taheer,wani fitinannen sautin shagwaba ta sako mishi ..”baby kaga fa tace wai baxata iya wankewa ba Dan Allah ka tayani rokonta cikina fa ciwo yakemin”..

Batare da ya daga kai ya kalleta ba yace kije ki wanke…

Hawayenta ta saka dannewa suka sauko muryanta na rawa tace
Yaya jinin al’adanta ne ajiki bazan iya wankewa ma yana daga min zuciya.

Tsaye ya miÆ™e da izza da masifa yace “nace kije ki wanke inbazaki wanke ba ki ajemin ni zan wanke ina abinda kikeso kenan.

Kuka ta fashe dashi batace komi ba ta fita da kayan takai machine ta zuba ta dauko stick din toilet ta daddana su dashi tanayi tana kuka sosai basu ko fita ba ta gama taje ta shanya mata su akan igiya daga nan dakinta ta nufa ta kwanta akan gadon tanata kuka can ta dauko qurani tana karantawa har Allah yasa taji sanyi ta bingire da bacci,da suka bushe ta tattaro ta kawo mata har dakinta lokcin taheer baya wajen,as usual ganin wasime ta hade rai ta biyota har daki

Sister dan Allah kiyi hakuri bason raina bane
Wallh badon ciwo ba zanyi abuna dakaina
Bani nace masa yay miki tsawa ba,karki damu na masa fada akan haka dan Allah karkiy fushi dani kinji?we r sisters in islam koda miji bai hadamu ba.

Wasime tay karamin yake batace mata komi ba harta tashi tay waje.

A satin bata gama warkewa da abunda tay matan ba sai ga wata kawarta ashanty wai taxo gidan weeknds

Haka zasu wuni suna Shagalinsu da abinci suna almubazaranci da duk abunda yake akwai acikin gidan,kwai in zasu soya sai anfasa guda ashirin fiye da rabin crate aci abar saura a zuba awajen wanke wanke.
Hakama irish ko kifi worst of all madara da kayan shayi sunci uban su dan kuwa rabin gwangani ake juye ayi amfani dashi kuma bazasu tana shanyewa ba zasukai mata sink

wasime tagaji sosai da ganin abunda akeyi da dukiyar mijinta,luckily enough a satin taheer yay tafiya bayanan,suna fita yawonsu da kawarta ta sace key din store ta kwashe abincin ta boye ta batar da key tayi maganinsu sukaxo suka sha bakar azabar yunwa na ranar gashi taheer bayanan.

Ranan daya dawo wasime kawai ya tarar agidan,duk dama baya kulata amma awajenta yabar jakar kudinsa akan ta aje masa,koda razia ta dawo taji yana batun kudin a waya ta sace jiki taje ta tura kawarta dakin wasime shigarta wanka kenan kawartan ta
Shigo dakin ta kwashe jakar kudin ta boye haka wasime taci neman kudi nan bata gani ba..

koda ta fadamishi baice mata komi ba ransa a bace ya shirya ya fito kan dinning ya zauna yana jiranta da abincn safiyar sa.

Jikinta a sanyaye Ta shirya tsaf cikin green atamfa,abincin datay duka suna kitchen ta wuce zataje ta debosu ahnyarta na shiga kitchen din caraf ta kamasu razia tare da kawar da jakar kudin a hannunsu suna gulmanta
Tsayawa tay tajisu tsaf
Tana shigowa suka raxana sai suka fuske suka bata jakar kudin kowacce ta kama gabanta suka dawo dinning din suka sameshi suka zazzauna kamar babu abunda ya faru.

Ran wasime sosai ya riga ya baci jin abunda kawar take fadawa razia nacewa ta dauki jakarne danta kullawa mata sharri a saketa,so bayan ta kawo masa abinci ne ta zo masa da jakar kudin ta gaggaya masa yadda Akayi agaban su razian sunaji.

Memakon ya dauki mataki kawai sai ya dau plate din abinci ya kwarara mata ajiki yabita da masifa cewa ta cika kananan magana tana damunsa da fitina shi babu ruwansa da karyan datakeyi.

Ranta abace ta rushe da kuka tace yaya itace fa tay maka sata ni menayi maka da zaka watsa min abinci ajikina?

Tsaki yaja ya tashi da jakar kudinsa a hannu yana cewa toh saiki min duka ki kwato amsarki..yana fadin hakan ya barta wajen a tsaye.

Ta mugun gudu ta juya tabar wajen ta wuce dakinta tana kuka dariya su razia suka tuntsire dashi suka tafa,suna kallo wasime ta fito sanye da hijabinta ta bar gidan,wajen bilti ta nufa ta zauna awajenta jin bazata iya daurewa yau ba.har can yamma bata dawo ba da kyar bilti ta rarrasheta tace mata ta koma gida tun kafin yasan tana fitowa batare da izininsa ba hakan ya kara dawo musu wani sabon rikici.

Duk yadda taso ta kwana anan koda ma zataji sauki aranta amma hakan bilti taki mata sam
Ta rakota har kofar gida ta shiga ciki.

Lokcin ana neman karfe takwas na dare jin babu motsin kowa a gidan yasata shiga dakinta tabar kofarta a bude ta can around 11pm jin ta kasa bacci yasa ta tashi ta daura towel ta shiga wanka.

Ruwan shower mai dumi ta sakar ma ilahirin jikin hadi da lumshe ido tana tuna last sex dinsu was in d bathroom duk memoryn hakan saida ya wanzu acikin idanunta tanajin kamar tsinka mata jijiyonta akeyi da reza tsabar zafi da radadin kishinsa daya dabaibayeta.

Ta gama kukanta acikin showar ta share hawayenta cos duk sanda ta kalle baby bomp dinta takandanji kamar wani halitta na tare daita a kowani lokaci so she wont feel loney nd cold anymore .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button