FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka kawai ta bige da murmushi bayan ta gama tuno kaf abunda suka zanta,daga can wasime take hararta up nd down cike da salon rainin wayo tace”Ke kin wani shigo kintsaya wai baki gaisuwa ne? Dariyar mamaki najaha ta fashe dashi hannu tabe da bakinta tace.”lallai ma yarinyar nan kece zan gaishar kowa?to snnu uwar mata..

wasime bata amsataba ta dan dauke kai tare da tsuke bakinta tana karasowa daf da ita.

Da kasar idanunta take kallonta,Wani matsiyacin kallo tabi dressing din nata dashi tace”Yanxu karfe nawa ne harkin wani zo?ni wallh yanzu ma na tashi daga bacci babu abunda nayi a gidan.

Tana fadin hakan bata jira amsaba ta juya ta nemi wajen akan cushion ta zauna tare da kai milk dinta bakinta ta cigba da shan abunta a hankli.

Har inda take najaha ta biyota ta tsaya akanta tanata kallon ta “ita dai wann rigar dake jikin wasime shiya gama tsole mata ido.. acikin ranta balain so take tay mata magana akanshi amma duk sai taji ta kasa furta komi.

Ajiyar zuciya ta sauƙe abun na cinta aranta tace
Ke Wallhi wasimé bakida mutunci,yau kuma wani sabuwar iskanci ne akanki kike mana yawo tsirara amma dai wannan ba rigar ki bace ko?..
hmm Ke ko kunya ma bakiji,kin wani dauko rigar yayanki kinsaka ajikinki kina yawo dashi a tsakar gida kamar wani sa’arki…

Cikin rolling eyes Wasime tace eh,kuma dai babu ruwanki da kayan jikina nan fa gidan mu ne zanyi abunda nake so,yo ai gwara ni bana saka gantalallun kaya ina fitowa waje dashi kinga iyakana cikin gida, kuma ina daidai dana saka rigar yaya na,da can uwar waye zai saka kayanshi inbani ba?

Shiru najaha tayi batace komi ba dan tasan suka cigaba da maganan zasu iya batawa juna rai.
Kyabe bakinta kawai tayi snn tace hmmmm cikin furzan iska.

tsaki wasime taja snn ta aje cup din soya milk din akam centr table,ta dan kwakwlo murmushi”
“toh sannu da zuwa badan halinki ba,yau kuma dame dame aka zo mana?Cike da rangwaÉ—i da rawar kai najaha ta karaso daf da ita cikin rage muryanta kasa kasa
Tace”Yaya na yana ciki ne?Halama ma ko tashi daga bacci baiyi ba ko?

Wani kallon debar albarka wasime tay mata game da tsane fuska taja baya kadan snn ta kalleta up nd down.tsaki taja..”ke kuma wa kika samu agidan nan kike kirashi yayanki?

…baki galala najaha tace kaaiiiii wasime…hmm chabdi yo aini nadauka dani dake munzama daya, yayanki ai yayana ne…wasime batace komi ba ta kyabe baki irin ai saikiyi..snn tace”toh ansamu missd cal nima dana tashi abacci bangansa acikin gidan nan ba,..

kusan a hargitse najaha
Tace mene?kina nufin wai asubanci yay ya fita
Yo ina yake zuwa da sassafen nan?Cikin tsareta wasime tace
Ke nifa bansan komi ba
Nide nasan jiya da dare munazaune dashi anan muna kallo toh da safe sai kuma Na farka naga bayanan, Hala yau bazaijima ba saiki ga ya dawo..

Cikin sauƙe ajiyan zucya Najaha tace ohh Allah yasa yau kuma me zamu dafa mishi?

Cikin sosai gefen kunne wasime tace “i dnt knw yet,Nide kizauna anan kijirani bari naje sama na dan kimtsa ciki kafin na dawo sai muyi magana feel free kizauna mana tana fadin hakan tanai mata nuni da kujera

Wani Tsandar dar najaga ta hargitso tace inxauna fa kikace?chab di wallahy saidai mu tafi duk inda zakije din tare. Ni fa ba yar gadinki bace.

Mikewa wasime tay tana dariyarta tace”hmmm kya ji dashi,toh muje cikin..

Sama suka dosa a tare wasime takaita harcikin’ dakinta suna shiga najaha ta tsaya tun daga bakin kofa tana karewa koina kallo, bata iya boye maitar kishinta ba ta dinga kalle kalle tana kyabe bakinta cikun ranta cewa take hmmm wannan katoton dakin duka wa ita daya..hmm lallai kam wasime tana cikin jin dadi,tana shanawa.karasowa bakin gadon tay lkcin wasime tanata magana bama jinta take ba Kallon gadon kawai take wanda akalla tasan ya doke wanda ita da maman ta suke kwanciya akai girma.

Wani gauron ajiyar zuciya ta sauƙe..
tana dada fahimtar harsashen mahaifyarta
Tasan inhar ta aure taheer rayuwarsu gabaki daya zai zanja…wannan uban gata da ake bawa wasime datake matsayin kanwarsa yo inaga ita intashigo a matsayin matar gida?

Wasime ce ta juyo cikin raha tace toh yaa kawata yaya kikaga daki na?yay kyau kuwa?..najaha tana kallon ta cikin yake tace “uhum kawata daki yay kyau.”Toh ina dakin yayanki yake?…

Batare da ta kalleta ba tace “mezakiyi dashi?

“Kai wasime ke badama’ mutum ya dan tambayeki?

Rau tay ido tace ai naga babu alakarki ne dayin wannan tambyar…
anyways dakinshi yana can ta waje dayan bangaren daga na gama gyaran nawa dakin nashi zanje in gyara yanzu

Cike da rawar kai Najaha tace “Allah?..toh mai zamuyi anan din pls lets do it sharp sharp saimuje chan din ko?..wasime batace mata uffan ba harsaida najaha ta gama sakar jikinta ta taimaka mata sukayi aikin tare suka wanke toilet suka gyara gado sukayi shara snn suka fetsa turaren qamshi.

Bayan sun gama suka fito suka kama hanyar zuwa dakin taheer.
Wasime tana gaba najaha na bayanta sai Allah Allah take sukai dakinshin tagani kodan ta samu rahoto mai dumi dazata kaiwa mamanta wayasani hala yau ma ta bata wasu shawarwari gameda hakan wanda zai iya dada jawo kusancinta tare dashi.

Har sukakai bakin kofar wasime bata juyo ta kalleta ba,sai suna daf zasu bude su shiga wasime ta sa fuska ta wani harde ranta tay banga banga a bakin kofar ta toshe hanyar wucewa da kafafunta ta hade rai”da mamaki najaha tabita da wani irin kallo”ke kuma meye haka?Murkuda bakinta tahauyi”nide wallh ki dan tsaya anan.Yaya na ai bazai ji dadi inya sameki anan ba…

Najaha bata san sanda taja tsaki ba tace akan me?…ke wasime wallhy bana son walakanci da iskanci da Allah kiban wuri

Dada toshe kofar wasime tay ta karayin banga banga tanacewa “yo akan me zaki shiga nan fa dakin yayana ne ai saida nace miki kizauna a falo innagama ai zaanzo muyi abubuwar mu….

haushi take ya kular da najaha muryanta a dagule da fushi tace ke ni bana son iskanci,kefa dramar ki tanada yawa.

Tace
“Drama ko? Hmm yau zaki ga drama kuwa in baki koma kasa kinjirani ba,wai ma dolene sai kinbini ha’aaa..nace miki yaya na bayason ana shigar masa daki ko?..kawai kije ki kasa…mtssss

Turus Najaha take kallon ta tanajin kamar ta shaketa kota kamata tamata shegen duka sosai iskancin wasime yasoma kaita makura
muryanta kamr na wanda zata saki kuka tace “kai Wasime wai gori zakiyi min sabida nazo gaban dakin yayanki?

cikeda bushe ido wasime tace yo ni Gorin me namiki anan?dan kawai nace bayaso ai bani nace ba shine ya fada…

Najaha dakejin kamar zata fashe cikin haushi tace “kai makaryaciya yaushe yace miki hakan

Kikkifata idanunta tayi tace ai ba dole bane kisani.

wani shiru nahaja tayi da’ fuska kalar tausayi can cikin kyabe baki tace Hmmm to ai shikenan.
Allah ya jikanmu muda bamuda yaya. .wasime ba damuwa kicinye dakin kicinye harda yayankin ai dama kekam ba a abun arziki dake dama can naga kamar walakntani kawai kike so kiyi hmm danma nazo gidanku ina son na taimaka miki..ba damuwa ni kawai zanyi tafiyata . ..

Tsaki mai tsayi wasime
Ta ja tana kikkifta idanu cikin turo bakinta gaba tace…ke toh da Allah kiyi hkri,nide ban walakntaki ba..yo aikece da shegen son bibiyar mutum kamar wata jela wai duk inda naje kema sai kinje?mtsww..tooh muje cikin amma nide karki taÉ“a masa komi bana son yaya yazo yamin fada.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button