FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

A kwance ya ganta kan gado ta kife kanta akan pillow bayanta kawai yake hanga, a nitse ya karaso ciki kwayar idonshi gaba daya nakan yadda yaganta so neat daga ita har environment din datake tsaf tsaf abun saiya daure mai kai yaga kamar ba ita bace,ko jiya jiyan ka kalleta bazaka ce zata iya mikewa garau hartayi wani abu mai kamar haka ba.

Takawa yake ahankli cikin nisan tunani har yazo bakin gadon bata farga ba, jin mutum ya zauna kan gadon yasa ta saurin miƙewa zaune suna hade ido gabanta ya dan fadi matsawa tayi daga kusa dashi kanta na kallon ƙasa shima kallonta kawai yakey haka kawai ya samu kansa da sakar boyayyar murmushi mai sanyi yanajin kamar mafarki yakeyi ganin yadda wasime take dawowa wata mai hankli da nitsuwa.

Cikin nitsuwar ta dago fararen kwayar idanunta dake cike da maiko taga ita yake kallo, maza tay ta dauke nata idon acikin nashi, ta sulalo kasa cikin ladabi da biyayya da sanyin jiki da dan fuskarta na yaribta daa ba’a rabashi da fitinanyar shagwaba cikin sanyin murya..tace mishi “yaa ina kwana”.

A takaice ya bude lumsashun idon shi da suka rufe bazata yana kallonta girarsa na dage a can sama yace “good Morning!hmm Ashe kin iya tashi da wuri? Dan dauke kanta tayi batace mishi komi ba ta dada sunkuyar da kanta.
Wani shiru yay yanata kallon ta directly baiko kiftawa only god knws wat he is thinking,dataji shirun na shi yay yawa saita dan dago kanta a sace, gani tay kamar ma hanklinsa baijikinshi satan kallonsa ta shigayi can anjima suka kara hada ido ta dauke nata da sauri ta mike tsaye cikin dabur dabur ta tsaya cur kanta na kallon kasa kamar wata munafuka.

Bakinsa ya kyabe a hankli gameda dage kafadarsa yanami furzan iska ta bakinshi,muryan sa kasa kasa yace”toh ya jikin naki,..har kinsha maganin naki kenan?” ÆŠan turo masa baki tayi batare da ta sani ba ta juya masa baya tana wasa da yatsunta a lunyace,can dai ta daure cikin karyewar murya tace”am okay aina warke murmushin da bai san dalilinsa ba ya kufce masa

Bai kuma ce mata komai ba, ita ma bata juyo ba sai ji tayi an fixgota tay baya kamar wanda zata hantsalo ta fado kasa,gaban ta ne ya wani buga da karfi jin kanta akan cinyarsa,sulalewa take shirinyi ya wani jawota ta zauna daram akai,wani irin muguwar kallo mai tarin ma’anoni yabita dashi wanda atake kallon nashi ya hanata iya bude ido ta kara kallon shi.

Cikin murya mai sanyi irinta jiya daya sanya ya lallabata yace “ke kikayi dukkan wayannan aikin?
And How comes…..?

Ta dada runtse ido kamar batajishi ba shiko ya dada matsota jikin shi,rawa tawa jikinta yafarayi tanajin kamr zata saki fitsari dan tsoro is asif bazata taɓa iyayin kwakkwarn motsi ko magana dashi a yadda suke din nan yanzu ba

Qamshin jikinshi ma kawai is suffocating her mind with alots of nostalgia,aranta sai tanajin wani tukikin kasala wanda babu kamarsa wajen saukar da tsumayi mai sanyi
,ahalin yanzu babu abunda take sha’awa kamar tajita kwance akan faffadan kirjinshi ko taganta ta kwanta tay lifff tana shakar wannan dadaddan kamshin turaren nashi Dake fita ajikinshi gameda sakar ma zucyarta sabuwar shauki mai tattare da sabuwar nitsuwa..

,saketa yay ya kama hanyarsa yay waje ya koma falo,yana zama baifi da minti uku ba sai gata nan ta fito,kallo daya ya mata ya dauke kanshi ya cigaba da kalon tv abunsa..a kusa da shi daf ta rusuna cikin sanyin murya after like 2 scnds ta saci kallon sa tace”yaa zakaci abinci?..ya kalleta da Æ™asar ido muryansa kasa kasa cike da shan qamshi yace”wannan tayin rowar fa?..kije kici kayanci ni bazanci ba.

Dan shiru tayi can ta takune fuskanta kamar zatayi kuka duk ta rasa na cewa a sannu a hankli ta dora hannunta akan idonta tana mutsukawa a sakalce”..yana satar kallonta yace “ke!! wai meye haka kikeyi?yau kuma kin dawo karamar yarinya ne?take ya hade fuska..”yace..kije kici abincinki mana Allah sa dai bazamu koma asibiti yau ba…”bata ce mishi komi ba ta miÆ™e tsaye tafara tafiya yabita da kallo,har sanda taje ta kan dinning din ta zauna lokacin hanklin sa baiya wajen,tea mai kauri ta hada mishi tasaka komi dan daidai dan taji sarai bilti tana fadin cewa shi baiyason too much sugar
Amma yanashan madara sosai dan haka ta tula masa milk tasaka sugar dan kadan wanda baifi spoon daya ba,lokcin idonsa nakan tv yana lura da lokaci sai gata ta dawo..agabansa ta aje tea din,taja gefe ta tsaya fuskanta a takune kamar wata mai aikinsa ta tsaya Kallon tea din yy snn ya daga ido ya dubeta da mamaki ayanyin sa yace”
..wannan fa?..dada takune fuskan ta tayi tace uhmm ruwan zafine kawai…tunda kace ban iya wancan ba ai zakasha ruwan zafin ko..?mamakin guts dinta yadingaji har cikin ransa.
Snn ya kyabe baki ya hade rai yace toh wayace miki ma zansha? Bawai zakiyi baƙi yau ba ai saiki ajiye musu abin naki,Rau rau tayi da idanunta Ta makalkale wuya kamar ma batasan dashi take wannan fiilin ba
Tace “Yaa nine fa zan soma zuwa musu, amma toh mesa bazaka sha tea din ba?Hararata yay yace”comn get out of my sight…adan tsorace ta juya zata bar wajen.
Ya kara tamke fusknsa
Yace “with ur tea!
Dawowa tay a hanzarce ta rusuna tana daukewa agabansa ta fashe mishi da wata sassanyar kuka.

Dauke kansa yy kamar baiji kukan nata harcikin zuciyrshi ba, baice mata komi ba harta wuce ta koma dinning din ta zauna yana binta da ido yaga ta dangwala shayin a fusace alaman taji haushi zama tay ta wani bata rai ta zubo taliyarta a plate tanacin abunta..

Kafadarsa ya dage ya shareta yaci gaba da bawa tv attention dinsa
Sai cin taliyarta takeyi kamar an aikota Can Yaji kamar bazai iya daurewa ba ya taso ya iso har wajen ya dada kare ma taliyar kallo,yaga dai is not dat bad kuma yana gamshi amma haryanzu zuciyarsa bata gama amincewa akai ba..girar sa na sama a dage yace”..are sure this is not gonna hurt u? Kafin ta amsa yace…ke kibar cin wannan abun zan siya miki wasu yanzu inna fita…dan turo bakinta gaba tay cikin kukuni tace nide shi nakeson ci,ai wancan dinne ya sakamin ciwon ciki ai nawa ma yafi nasu dadi nishi kawai zanci..babu bata lokaci yaja doguwar tsaki yace to kici kayanki…and better round up befor i get down, yanzu zamu fita ko kin fasa zuwa gidan kawarkin ne…tsaye ta mike zumbur tana cewa “a’a yaya banfasa ba..toh bari inje in..

Wani Tsawa ya daka mata “Will u shup up nd sit down?Kinji menace miki kuwa?

Tsilli tsilli tayi da idanu ayayin da ta koma wajen zamanta ta zauna a sudade yace.”Kici abincin ki nace,wato daga magana caraf har kin tashi tsaye zakije ki shirya zakije ne kizuba musu ido da yunwa acikinki dan ace gidanku ba a baki abinci ko?

..cikin sanyin jiki ta girgigza kanta snn ta jawo plate din a hankli ta soma ci tukun ta dan dubesa tace “kay hkri yaya ai zanci.Kafin na dawo kin gama Ya fadi hakan yana haurawa sama agaggauce.Sama sama taci taliyar snn ta tattara sauran ta saka a coolern ta haura sama ta dauko takalminta da dan karamin veil tayafa akanta daidai lokcin shima yana saukowa kenan da jakar laptop dinsa a hannu sai gata”
..exchanging kallo sukayi tun daga can sama snn ya dauke kansa.

Har sun fita can waje ya sakata ta dawo ta dauki
Cooler abincin yace mata dashi zata tafi can.

Basuce wa junansu uffan ba har suka kai bakin gate din gidansu najaha..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button