FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jikinta a sanyaye kanta na can kasa sai tarasa me wannan furucin nasa yake nufi,gudun karta bata masa lokaci cikin binne damuwarta tace “anything will do…kada kansa kawai yy cikin sauke ajiyar zuciya ya saka kai ya fice daga falon baice mata uffan ba.

Ta dade a zaune awajen yanayinta cikin rudani sai bin kofar dayayi da ido takeyi duk tarasa abunda yake mata dadi..can dai data gaji ta mike tahaura sama tay dakinsu.

Jiki a sanyaye ta bude ta shigo ciki..zama tay abakin gadon su ta rafka wani uban tagumi,Sam takasa samun nitsuwa acikin zucyarta, bincikawa tahau yi ko zataga bilti amma sai shiru,abun duniya yabi ya isheta acikin zucyarta,tana ta tunanin wayar dataji sunayi dazu da taheer,tarasa meyasa ya furta wayancan kalaman nacewa bilti tay hkuri ta dawo kuma meyasa bilti taketa kuka taba bashi hakuri,sosai hanklin ta ya tashi…
Bata iyayin komi a dakin ba,saukowa kasa tayi sai kuma tarasa mema ya sakata saukowa,gashi ya kulleta kirif acikin gidan babu wani hanyar da zata fito waje bare ta dan leka bakin gate.

Komawa dakin tay snn ta cire uniforms dinta takai ta zuba a loundry basket ta jawo dan karamin towel daidai rabin cinyarta ta dora ta fada wanka ta hada harda alwala..

tana fitowa ta zauna abakin madubi snda ta tsantsane jikinta tsaf snn ta mike tayi sallahn magrib tana zaune awajen tana zikri aka kira isha’i nanma ta mike tayi, tana cikin kai raka’a na Æ™arshe saigashi nan ya turo kofar cikin notsuwa.

kallonta ya tsaya yi tunda ga can bakin kofa,snn ya karaso ciki ya aje mata ledojin daya shigo dashi agefen gado yaja mata kofar yay waje.

Falo ya nufa ya zauna akan doguwar kujera gameda takure kanshi waje guda kamar wani marar lapya duk ilahirin jikinshi baiya masa dadi

This whole situation has changed his perception about trust,sai yanajin zafi da rauni mai tsanani yana ratsashi acikin zuciyarsa da kwakwalan sa.

Kwanan su biyu a gidan shikansa bai iya gane kansa ba, bare wasime datake ganin komi na gidan ya zanza mata, kamar wani kiftawar ido da bisimillahi taga suna rayuwarsu su biyu babu alamar bilti, taga har kayanta ma duk ta kwashe duka, ranan dataga hakan taci kuka bana kadan ba,zuciyarta yanason ya fahimtar da ita cewa bilti tafiya tay amma mind dinta sam sam ya kasa amincewa da faruwar komi,taga yanayin yadda mood din taher ma gaba daya ya sauya acikin gidan,sosai lamarin ya taba shi ya dawo wani shiru shiru sam bai son a damesa, magana ma inyay mata saidan ya tambayeta me zataci yaje ya siyo ya kawo mata.

Jiya ta kammala exams dinta batada wani abunyi a gidan,ita kenan cikin zullumi.. inzai fita nashi jarabawan haka zai kulleta agidan kamar wata prisoner tarasa abunda yake mata dadi,daga tayi kallo saita kwanta tayi bacci harsai taheer ya dawo.

Kokadan Ya kasa iya controlling din emotions dinsa,haryau baiji sha’awar yin magana da iyayensa ba kodan ya sanar dasu akan abunda ya faru, fushi yakeji dasu acikin ransa aganinsa ai duk laifin tasu ne da suka wofantar da komi na rayuwarsa,nasu rayuwar kawai suka saka agaba basu wani damu da halin da absence dinsu zai iya jefasa aciki ba.

Ya tabbata da suna yawan zama a gidan da tolu da musa bazasu soma kawo tunanin yin musu abunda suka aikata ba,the house was gallant nd almost free of charge,shi ba zama yakeyi ba. kullum dai bilti ne agidan kuma ita ba komi bace face mai aikin gida,and they are alwys indoors wani bin saitaci kwana biyu ma bata leka tsakar gidan ba.
..kodan ata dalilin haka yasan dole ne Wani acikin su ya dauki advantage yay abunda yaga dama agidan saidai baiyi tsammanin Abun zai kai har haka ba.

Tsabar damuwa a kullum ya farka daga bacci ko ya dawo zai kwanta saiya tsaya ya neme layin bilti ko ya kira layin kawunta dan yaji kodama zata dan saussauto zuciyan ta yayi sanyi tace zata dawo,amma duk sanda ya kirata yawanci saidai yaji ance masa switchd off ko not reachable, case din malam musa kuwa tuni yakaiga wajen hukuma ynzu dai an kulleshi ne ana ta yan bincike ana tara shaidoji.

Yau kwana uku kenan da tafiyar bilti da kyar abubuwa suka soma yin sanyi a zucyar shi ya koma ga kan karatunsa.
Duk dama dauriya kawai yakeyi dan sosai yake fama da matsalar rashin nitsuwar zuci.
Wani bin ko ya daga takarda zaiyi karatu baiya iya concentrating he is eida thinking of yanayin abubuwan daya afku a gidan,ko bilti ko yadda zai zauna agidan shikadai da wasimé.

Fushi yasaka yayi alkwari makansa akan bazai taba neman kowa acikin iyayensa dan yay wani korafi ba,he thinks inyay hakan ma duk abanza ne, amsa kawai zasu bashi daga can suce shi ya daure ya kula da komi,hala ma bazasu making wani kyakkwaran effort dansu zo su gansu acikin wannan yanayin da suke ciki ba..
ya gama sanin halayyar iyayensa,inba wai dan son ransu bane zasu datse ayyukan su toh bazasu taba daukar lokaci domin zuwa kaduna haka nan kawai ba.

He rather do it all by himself for now gudun kar akara bata masa ransa,duk randa Allah ya kawosu yy alkwari zai fidda musu duk abunda yake cikin ranshi sabida ji yakey kamar yagaji da komi.

The feeling is very tiring nd depressing,duk a dame yake,ga tunani kala kala da suke kassara shi kullum acikin lissafe lissafen lokacinsa yake yana tambayar kansa yanzu kenan ya zaiyi da dawainiyar rayuwar sa wanda da can bilti ce take yawan dauke masa nauyin su akan shi danya nitsu yay karatun sa sosai,da can inzaiyi wani jarabawa mai muhimmanci a schl har wanki da guga da komi ita take dauke mishi shi baiya aikin komi har saiya samu hutu,yanzu kuma ga aikin kulawa da wasimé daya karu akansa yasan abun bazai zo masa da sauki ba sam sam,Kwana biyu dayake fita yake barinta a gida gaba baki daya baya cikin hayyacin sa,sam hanklinsa baiya cika zama ajikinshi,haka zai dinga tunanin halin datakeciki,ko wanda zata iya shiga ciki agida ita daya, abun na damun zucyarsa sosai saidai haryanzu bai gama yanke shawarar yadda zai tackling din issure din ba.

Karfe biyar da rabi na asuba wasime ta farka daga bacci,adduar farkawa daga bacci tayi sann ta sauka a nitse ta nufi toilet tayi alwala tazo ta gabatar da sallan ta,Kwanciya tayi akan sallayar tayi ruf da ciki tana rera kukanta a hankli zuciyarta cike da tsumayin kewar bilti,ita ba komi bane ma yafi karya mata zuciyarta ayanzu kamar zaman kadaicin ta somayi a gidan.

Kwana biyun nan haka take zamanta ita kadai batajin motsin kowa bata kuma magana da kowa haka zalika bata ganin kowa harsai taher ya dawo daga makarnta
Hatta abinci ma wanda ya sissiya mata kawai take iya ci babu halin yin wani canji ko dabara,duk zamanta anan kullum bilti ce mai kulawa dasu, duk dama wanibin takan koya mata yadda akeyin wasu abubuwan a kitchen saidai bata taba barinta ta gwada yin girki dakanta ba ,kuma shidin ba wani tsayawa yakeyi ya kula don yaji abun da takeji aranta na tsoron zama agidan ita kadai ba,abun duniya duk yabi ya isheta ta kasa samun nitsuwa da sukuni,kullum tunani take inama ace akwai makaranta tasan hala kawarta najaha zata iya debe mata kewa,..juye juye ta dingayi cikin wann tunanin duk ta rasa matakin da zata dauka wanda zai kawo mata maslaha da sassauci tana cikin haka Bacci barawo ya karayin awon gaba da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button