FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsayawa yay yanata kallon dariyarta,zai iya cewa ma tunda yake bai taɓa ganinta a cikin farin ciki da Annashuwa irin wannan ba,gabaki daya hanklinsa saiya koma kanta yana ta kallon annuri da nishadin dayake wanzuwa Akan kyakkwan fuskarta, haka kawai yaji ransa yay sanyi atake ya sauƙe wata ajiyar zuciyar daya sauƙe masa wata sabuwar nitsuwa.

Dan firgita yay jin anata calling attention dinsa atacikin wayarsa, adan harzarce yanamai dafe goshinsa yace oh im so sorry i got carried away me kace ma?Wanda suke wayar dashi yace “ok,i said next week insha Allah zan turo maka sauran kudinka idan sun shigo saika min magana…yace ok babu komi thanks..daga nan sai suka datse wayar..

ajiyar zuciya ya sauƙe da tunanin duk yadda zaiyi ya kashe kudadensa dake cikin acct da salaryn shi na wannan watar.

Yasan dai rabi akan Hidimar komawar wasime schl zai tafi sabidaa new session ne kusan komi da zai siya mata zai iya zamtowa sabo,and he needs to get some food stuffs a gidan
Tunda yaga kamar she is having so much intrest akan girka abincinta agida, har yau dai baiji duriyar iyayen sa ba barema su turo da normal upkeep da suka saba turowa a gidan.

Saukowa yay zuwa cikin falon atake iskan wajen ya gauraye da qamshin turarensa mai dadin qamshi,qamshin ne ya soma sanarda wasime zuwan sa,amma bata ko iya juya kanta ba ,a cikin nitsuwa tay saurin gintse sauran dariyarta tay shiru tana satar kallonsa harya ya karoso ciki.

Ko kallanta ba baiyi ba ,waje kawai ya samu ya zauna a one sitter baice mata komi ba ya fara latsa wayar sa,juyawa kadan tayi tadan sace kallonsa sai taga gabaki daya hanklinsa yanakan wayarsan me…duk saita rasa meyakeyi acikib wayar daya bada hanklinsa gabaki daya baiya ko kiftawa,Kamar da wasa tafarajin kamar bata da nitsuwa acikin zuciyarta sabida abunda yakeyi din.

wani lumui tay tana ta satar kallonshi ita Kawai tana son taga ya dena latsa wayar,inba haka ba kuma tana son sanin abunda ya dauke hanklin sa dayawa har haka aciki.

Da kyar dai ta kaucar da wannan yanayin a zuciyarta ta basar ta cigaba da kallonta jim kadan anayin wani part mai abin dariya bata iya controlling kanta ba ta wani tuntsire da wata mahaukaciyar dariya mai dan iskan karfi wanda yasa shi dauke kanda akan wayar game da dagowa atake,kirjinshi saida ya buga dayaji sautin dariyar, fuskan sa a dore ya dago kansa ya na kallonta,suna hade ido Wasime tay tsit game da kama bakinta bata kara yin wani motsi awajen ba.

Hade rai yy Cikin hararar ta,muryansa ciki ciki yace “ke zo nan!.

Sadaf sadaf ta tashi ta iso gareshi tare da rusunawa a gefen shi ta takune fuskanta tana dan turo bakinta gaba

fuskan sa a harde Ya juyo ya kalleta yace
.”are u mad?wann wani irin wawar dariyace da zakimin anan,kina hauka ne?

Kanta ta girgiza cikin sauri..ahankli tace a’a
Saitay shiru kuma bata basa hakuri ba abun saiya bashi haushi
Cikin Zare mata idanunshi yace”baki da bakine kike girgizamin kai?nace miki kidena girgiza min kai in ina miki magana..kafin ta amsa shi,ya wani ja baya yay wani irin resting bayanshi akan chair muryansa a shake snn yace “go der nd get on ur knees..

kirjinta ne ya buga da karfi batace komi ba ta mike cikin saibi taja can gefe tay kneeling tare da daga hannunta sama..

Shareta yay,can ya dauki Remote ya hau caccanza channels baiga wanda yay masa kawai ya tashi ya jona tvn da wayarsa ya saka wani film na daban mai shegen ban tsoro,suna film din “scream” babu abunda akeyi acikin film din face Æ™azamin kisa masu mugun rikitarwa da tsoratarwa.

tuni wasime tafarajin Kamar zuciyarta zai fito waje dan tsoro dakanta ta rufe idanunta danta dena kallon film din

Tafi minti 30 ahaka duk jikinta yana rawa rawa can ta soma sauke wasu makudan hawaye suna saukowa zirr akan fuskanta har izuwa kan kumatunta,gaba daya taji tagaji da komi ta rasa mesa batay baccin wuri yau ba.

,hannayenta dake kallon sama kamar an doresu da igiya haka ta dingajin su “cikin shesshekar kuka muryanta a sanyaye tace” yaa im sorry.

Yi yay kamar baiji ba,ta sake furtawa nan ma ya shareta,ganin kamar bazai ma kulata ba yasata fashewa da matsanancin kuka yaa dan Allah kay hakuri bazan kara ba..nan ya dage idonsa cike da kasaita kamar wani dan sarki yana mai jefo mata wani siririn kallo,kallon ta yake har saida kallon ya isheshi snn ya kauda kansa ya kara shareta..
“shiru yay idon sa nakan tv yanata kallon sa, sai can ya saci kallonta yaga tana ta zubda hawaye gwanin ban tausayi duk jikinta rawa yake bata ma son ta bude idonta bare ta kalli horror film din da ake kalla a tvn,kamar daga sama taji ance “come here ..da kyar ta bude idonta tana budewa kuwa suka hada idanunsu waje guda cikin hanzari ta dauÆ™e nata acikin nashi ta soma kallon sa.

Da kyar ta tsaya a tsaye tsabar tsamin da jikin ta ya dauka har wani dingishi dingishi takeyi tanajan kafafunta da kyar,a dan wahalce ta iso gareshi tana famar share sauran hawayen ta dake kin saukowa.

Tana isowa daf yay mata nuni da gefenshi Yace zauna anan..

a hankli ta zauna kanta na can kasa,ya dore fuskan shi cikib sigar masifa yace “wato bakida aikinyi saidai kisa abun dariya kina cikama mutane kunne ko?…
“when last have u revised ur books?..ahnkli ta dago cikin sanyin murya tace
“Tun lastweek,ya kada kansa yace hmm yayi miki kyau,and wen are u resuming schl?cikin sanyin murya still tace masa “next week monday.!

“Ince dai kin iya abincin yanzu?ko kawarkin ne zata cigaba da zuwa tana miki kinaci?.dan shiru tay cikin tunanin amsar daya dace ta bashi,Can saita girgiza kanta a hankli tace mishi “ni zanyi dakaina,shidai baice mata uffan ba..saidaga baya ya dan dubeta yace”write down all the list of wat u need for schll saiki kawomin ingani,cikin ajiyar zuciya daya kufce mata tace mishi toh.

Zata miƙe tabar wajen cikin sauri ya dallara mata harara yace ke dawo nan ki zauna,wai ina zakije dama?A sadade ta dawo ta zauna din tare da yin shiru,tana zama ya tashi tsaye ya barta a falon ya shiga kitchen after like 10 mins saiga shinan ya dawo hannun sa dauke da 2 cups of steamy coffe yana dosowa qamshin sa mai dadi yawani gauraye wajen..

mika mata one cup yay ta amsa, snn ya zauna agefenta ya fara sipping nashi a hankli har ya shanye Itakam da kyarma takai rabi,can Bayan sun kammala wasime ta tattara cups din takai kitchen ta dawo tay zamanta agefensa tana kallon film din dayake kalla,daf ana fadar karshe ne so Ba’a wani dade ba yaga ta fado akan cinyarsa juyata yay kadan yaga har jikinta ya sace gabaki daya tana famar tikar bacci..

Gyara mata kwanciya kawai yay batare da yayi yunkurin dagata akan cinyarsa ba.

12am na dare nayi ya somajin kamar anfara iska mai karfi tawaje,dan lekawa yy ta window ganin yadda gari yay gum ya hargitse yanayin garin kamar dai za’ayi ruwa,hakan yasa ya kashe tv snn ya kulle koina yana dawowa ya sunkuceta yahaura can sama dakinshi tare da ita..

Akan lafiyayyar gadonshi ya sauƙeta A hankli haryanzu idon sa nakanta,gently ya aje kanta akan lallausar filonshi snn ya gyara mata kwanciya,ya hau rage mata kayan jikinta rigarta ya soma cirewa snn ya kyaleta daga ita sai yar vest da sket din dake jikinta,bayan nan tashi yayi yaje wajen swicht yanamai rage musu gudun A.cn snn yadawo yaja bargon sa mai tsananin laushi ya lullubeta da shi har wajen wuyarta snn ya kyaleta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button