FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wanda shine ahalin yanxu yafi kowani course a medical line wuyan sha’ani..ba kowa yake iya jure yinshi ba sai daddaya.

Burinsa arayuwa shine ya zamto “surgeon general” kamar yadda suke Æ™ira a a fannin sojoji.

Cos Thats when u wll be the most fast_fowarded physician,nd perfom life saving treatment while at war field.nd also combat diseases with immidiete effect so that soldiers will progress to the next health care level.

Bayan haka Kuma araywansa yana son yaga yay kudi,He really wants to be rich, ko dai ince to lead a peaceful nd comfortable life with his family.shiyasa aransa bai taÉ“a tunanin zai Æ™arayin wani aure ba dan kwata kwata baida ra’ayin auren mata biyu

Tun yana dan yaro ya kuÉ—urta hakan a zciyarshi kuma haryau wann burin nasa tana nan, Kullum insuna hira saiya fadawa mamansa shi mace daya kawai zai aura kamar dai yadda yaga baban sa
Qasimu yy,yaji ance mace daya babansa ya nema arayuwarsa kuma itace wannan mahaifyarsan daya aura.

…shikuma sai gashi abun Baiwanizo masa cikin sauki ba,gashi wai har yay auren,da kuma unkwn girl a lokacin da bai taÉ“a yin tsammani ba,ya dauka rayuwa zata aramai lokacin dazai tantance matar dayake so a zuciyarshi ne snn ya aureta suyi rayuwarsu mai tsananin dadi mai cikke da soyayya da sassanyar shakuwa.

Saidai tunda lamarin nan yafaru tsakaninsa da wasime tuni yafadawa zucyarshi weda he likes it or not wasimen ce dai kawai matarsa ta har abada.he most have to learn how to love her danshi gani yake kamar baida zcyar da zaiso mutane biyu equally..
Dan sosai ya fahimce kalar zuciyarsa,aganinsa zucyarsa wawiyace bata iya son abu ba,kamar yadda bata iya ɓoye ƙiyayya ba..zcyarsa inta tsane mutum toh fa bata sarara masa.

Shidai koma yayane shi zaiyi hkri da wannan qaddarar daya riga ya doreshi da wasimé ya kuma saka ta zamto tamkr rabin jikinshi.

He neva expected this but its ok..ai yarinyar ma is not dat bad ta fuska
Halayyarta ne kawai bazai iya cewa komi akai ba…Dama can shi baida wani babban buri ajikin Æ´a mace, baidamu da sai ya samu tsaleleya kyakkywa ko doguwa fara maya yar wace da wane ba

All he needs is a simple pretty girl dazata masa biyayya snn ta kula masa sosai da iyayensa ababen kaunarsa,shisam baidamu da kyan mace ba tundashi din kyakkwane sosai.

Ƙarfe biyu da rabi na dare yau yay bacci.bai farka ba sai wajen to six ƙarar alarm clock ya tadashi lokacin har an fito daga sallan subh,a cikin sauri ya tashi firgit ya shiga toilet ya doro alwala yazo ya gabatar da sallahn nashi a dakinshi
Shikadai

Yau da wani irin nishadi da murna wasime ta farka,yau zasuje yawo da amininta yaa saheeb,yau ji take kamar hajji za’a kaita ta shafo dakin ka’aba,tsabar doki da diddiri yau batayi wani gamsashen bacci ba.

tun ana kirar asubahin
Fari ta farka ta sauko daga kan gadonta ta kwashi kayan datay fitsari ta dukunkune su ta yo dasu hanyar fita waje ,acikin sanda take tafiya babu ko takalmi akafafunta.sadaf sadaf tasaci jiki don karma bilti taji motsinta ta farka ta bude kofar baya a hankli dan karya ƙara tayi waje,da sauri taje bakin tap ta kunna kan famfo sai shaaaa ruwa mai sanyi ya soma zuba,wani jan zcyarta tayi sama jin tsabar snyin ruwan,tsugunawa tayi awajen kamar yadda ta saba ta hau wanke kayan fitsarinta ta,saidai yau bata wani dade awajen ba ta dawo cikin gida.

Lkcin babu kowa koina yay shiru,dan Daga ido tay sama snn ta kalle agogo taga ana neman karfe bakwai na safiya ahnkli ta dawo cikin dakinsun toshe da bakinta sabida iska tana ɓari barin sanyi,jagwab ta jike jikinta da ruwan sanyi, numfashinta sai hawa da sauƙa yake ta kuma kakkame jikinta saboda muguwar sanyin ac dayake busa iska acikin dakin.

Kayan jikinta ta sauya cikin sauri izuwa towel snn ta miƙe wai zata shiga wanka,a daidai lokcin bilti tay juyi cikin bacci daga kanta keda wuya ta hango wasime na sauri sauri zata shiga cikin bathrum
A cikin gigin bacci bilti ta daka mata tsawa tace”Ke wasime?

..tsayawa cakkk tayi daga bakin kofar tana zazaxxare idanuwanta waje kamar wadda taci kudin aika.

Bilti ta dada murmusa ido ta kalleta da kyau snn tace”wai me zakiyi da safen nan?kinma yi sallah kuwa?

Girgiza kanta tayi cikin zumburo baki tace
‘Nifa banyi ba tukun,ince wanka zanyi kafin ya iso!.
Cikeda sakalci ta karashe mgann tana wasa da yatsun hannunta.

Tashi bilti tayi ta zauna
“Kinci kaniyarki wasimé.
Kizo nan marar kunya kawai,da sassafen nan ne zaki tashi ko gaida ubangijinki bakiyi ba zaki ce wai zakiyi wankan jiran wani saheeb?Shi saheeb din ne yace miki asubanci zaiyi.Yanzu halama yana can yana baccinsa kuma bazai karaso ba sai can wajen karfe goma…ki wuce kije kiyi alola kizo kiyi sallah.Inba haka ba babu inda zakije.

Batasan sanda tafara bubbuga kafafunta akasa ba…murya kamar mai shirin yin kuka tace
Haba bilti,haba bilti
“ÆŠan wankan ma?kaiiii bilti..warin fitsari fa nakeyi,..yanzu da kike cewa bazaizo ba inyay batan kai yay asubanci yazo faaa, basai kawai na saka sabuwar atamfata da matar Qasimu ta siya min in bishi ba?

Tsaye bilti ta miƙe sann ta capko hannayenta gameda buge mata baki
“Kewai meyasa bakida kunya?kina kirar sunayen mutane gatsau babu respect ko?uban waye kikaji yanace mata matar Qasimu?ehhh

Hannu ta dora akan fuskarta cikin muryan kuka dik tabi ta firgita
Amma bakin dai bai mutu ba”yo ni ai bansan sunanta ba..mezance mata!

Bilti ta dungureta
“Kice mata “mama” mana!Ita sa’arki ne? toh Wallh zamu saka kafar wando daya dake agidan nan inbaki shiga taitayinki ba wasime

Wani Zirrr hawayenta suka zubo kasa batace komi taja tayi shiru

Kije kiyi alwala kixo kiyi sallah,ahankli tace Toh snn ta ja kafafunta kamar mai ciwon aljanu ta shige cikin bayi ta kulle kofar da dan karfi ,kada kai bilti tayi snn ta bar wajen..sharp sharp wasime tayi alwala ta fito ta samu babu bilti
Dan haka batayi sallahn ba kawai ta shafa’a ta bude jakarta tahau fidda sabbin kayanta na dinkin sallah waje..

da akwai takalmin kwas kwas ma da jaka da aka siya mata,ita duk sanda ta debo su tana kalla sai ta dada shafasu..
Lallai matar Qasimun nan akwaita da kokari
Ai bilti tariga ta gayamata cewa itace tayi mata dinkin sallahn ta har kalaloli biyar,masu dan karan kyau.,tsadarsu ma bai dameta kamar yawansu ba.

Yatsarta ta cusa a bakinta tana ciza cikeda da tunanin zuci mai yawa
“Wayyoo Inaga yanzu tana can Æ™auyensu cikin kawayenta su hansatutu da indodo da kuluwa dasu yar ficcika?,aiko da anga wankar cakarewa da caku gaye,wannan irin kaya masu hegen kyau haka?yo Kaff kauyensu tasan baza a yi mai irinsa ba,yau farinciki fall ranta..Ta shafasu ta dada shafasu fuskarta cikke da murmushin jin dadi,yau duk ta rasa wani irin ma kwalliya yakamata tayi ma fuskarta dake tana tsantsar natural beauty mai daukar hankli so bata saba da yin kwalliya ba” ..saidai fa yau din na daban ne acikin zcyarta.

Yaune ranar da zata soma ganin garin kaduna
..sosai ta zaƙu ta kuma saka komi a ranta,musmm sabawa datayi da irin labaran da saheeb yake bata akan inside town da yadda abubuwan nishadi na yara ke gudana..yau gashi Allah yay itama zata leƙa taje tagani da idanuwanta

Jin motsin bude kofa yasata firgita a firgit ta kama sallahn Æ™arya kanta babu ko dankwali…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button