FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bilti tace karka damu na jaddada masa hakan

..baice komi ba kallon wasimen yay da gefen idon shi shibaiyi gaba ba baiyi baya ba,bilti tana ganin haka ta mike tabasu waje tay kamar kitchen zata”..

Kamar dama jiran haka yake bilti tana bada baya ya tako ya iso daidai kanta ya tsaya,gabanta ne ya rinka faduwa,ji tayi an riko kunnenta a hankli,narai narai tayi da idanuwanta ta dago a kasalance ta kallesa da wata fitinanniyar fuskar shagwaba wanda atake yaji ta shige cikin gangan jikinshi,zuciyarsa na wani narkewa kominshi yanayin sanyi,lumshe idanuwansa yay batare da ya shirya ma yin hakan ba,yana budewa yaga ta tsura masa kyawawan idanunta tana kallon kyakyawan fuskan shi a zauce tamkar wacce take shirin hadiyeshi..shima kallon kyakkwan fuskanta ya dingayi yanajin wani irin
Feelings mai karfi da shigewa ruhi tare da ratsawa cikin kwakwalwa da gangan jiki.

Da kyar yay control kanshi snn ya”kafa mata wani federal warning akan ta nitsu tayi karatu sosai,snn yace tasani cewa duk abunda taje ta koya a aji saiya yazo ya tambayeta a gida, inbata gaya masa daidai ba saiya yanka ta…

Sosai ta tsorata da yadda ya ce zai yanka tan duk dama yau din tanajin sauyin yanayi akanshi tanaji aranta kamar yafara dan burgeta,cike da fargaba ta amshi maganganun nasa tare da masa alkwarin zatayi iya bakin kokarinta wajen ganin tayi karatu..harya saketa ya kama hanyar fita bata dena kallon bayansa ba.

Karamin ajiyar zciya ta sauƙe tanajin kamar ta koshi da abincin nata.
Tattarawa tayi tabi bayan bilti da su takai kitchen ta ajiyesu.

7:00 cass tay sallama da bilti suke fice agidan tare da tolu,acikin wata 506 ash colour da taheer ya bashi akan kullum dashi zaina kaita schl, agidan baya ta zauna ta make tayi kak kamar wata big madam,dauke kanta tayi tanata kallon bakin titi ta window har suka isa schl din batace ma tolu cikanka ba,yana ajeta ta sauka ta wuce cikin makaranta.

Aranar farko da bata saba da kowa bakaramin hawaye ta dingayi yi ba,duk tabi ta dagawa mai kulawa da ajinsu hankli,yara yan uwanta sai kallon shirmen ta sukeyi.

Aranar harsanda aka kaita gaban shugaban makaranta,dake mace ce harta dauka ko wasime batada lpyane take kuka, amma daga tace zata kira taheer saitaga tayi shiru ta nitsu..

Tunda shugaban makranta ta fahimce hakan, ana zuwa da case din cewa wasime taki zama a aji kotana kukan banza da wurwuri zatazo da waya tace zata kira taheer, shikenan kuma anyi maganinta Ahaka haka harta zo tayi abokai a ajin ta saba da karatunta ta mance da batun kuka.

After 3 months.

Fara zuwan wasime makaranta sosai yafara sauya mata hali ta dawo calm nd cool bata ma da lokacin shashanci ko wasa..and taheer was on her neck duk da baida lokacin kansa amma haka yake takurawa don yaga wasime ta nitsu tay karatu,kusan kullum saiya zakwalota ta masa bitan karatun da tayi a makarnta…both islamiya da boko,gashi tana bala’in jin tsoron sa bata iya yin garaje…within no time halayyar wasime gabaki daya suka soma sauyawa suka dawo masu kyau gwanin ban sha’awa…yanzu akwaita da basira da ilmi,tarbiya da nitsuwa kuwa sosai yake son ya shiga cikin jikinta.

A bangaren saheeb ma haryau bai hakura da qudirinsa na kwato wasime ba,sosai yasaka abun ransa kullum saiya daga makansa hankli da sake saken banza.

Tun zee bata ganewa harta tasoma ganoshi akan haka sukayi fada sosai ta dena shiga tsabgar sa duk dama ma haryau ma taheer kawai take daurawa laifin duk wani abunda ya afku da ita musamman tsakanin soyayyarsu da saheeb.

Ita gani take kamar tin farko taheer ne ya cusa ma saheeb son kanwarsa wasime.

Yanzu gashi ta dena gane kan saheeb saboda an rabasa da yarinyar.
Baida wani aiki sai tura men din babansa suna bibiyar rayuwar taheer dana wasime duk wani motsin su yana sane.

Hatta sakata a makarnta da akayi duk yaji labari,ranar dayaji sunan schl dinma wuni yy yana jan tsaki yanajin haushi taheer aransa wai taheer ya saka wasimen sa a makaranta yayan talakawa Bai sakata ana masu hannu da shuni wanda ya dace da ita ba

Shi da can so yake asakata a wani babban private schl mai aji irinsu turkish ko nile da sauransu inda za’ana biyan makudan kudin makaranta dantayi karatunta acikin yaran masu kudi wayayyu itama tay ilimi ta waye daidai da ajinshi.

Nan makarntar al’iman da taheer ya sakata normal private schll ne, school fees dinsu is just 85 thousand naira harda islamiya session kuma babu laifi ingantaccen ilimi da tarbiya suke bawa yara.amma saheeb shi duk wannan bai masa ba,yama za ayi ace matar da zai aura in the future ce zatayi makarantan yayan talakawa irin wannan,haryau haushin taheer yakeji kamar ya kashe shi,sam ya kasa danne xuciyarsa
Gani yake kamar taher ya cuce rayuwarshi daya raba sa da wasime dan har iyanzu zuciyarsa bata amince da cewa akwai aure a tsakanin su ba.

Haka ya tursasa kawun sa yaje makarantar batare da sannin kowa ba,yasa kawun nasa yakai musu tayin cin hanci na makudan kudi akan cewa su saka
Hannu suce wasime ta samu free schorlaship daga hannun wani attajiri daga haka sai su canza mata makarantar da ransu yake so.

Saidai basuci sa’ar samun hakan ba, haka firr shugaban makaranta yaki amince musu yace shi babu ruwan sa indai baza a involving guidance in yarinya acikin maganan ba bazai saka hannu a canza mata makaranta ba,kuma sukansu sunsan wasime bata da wani jagora arayuwarta sai taheer din da suke so suyi abunsun batare da masaniyarsa ba,babu yadda ba suyi da hukumar makarntar ba, sun kawo kudi,ga kyautar mota akan tayimusu abunnan cikin sirri amma haka zancen ta lalace.

A É“oye saheeb yakan zo makarantar ya tsaya a bakin gate don ya kalleta kodama haklinsa zai kwanta,babu irin kulle kullen da baiyi a xcyarsa na son dauketa ba,kuma kusan duk sanda yazo yana ganintan amma baya yarda ta ganshi sabida akasan zucyarsa yana mummunan shakkar zuciyar taheer.
Yasan karon su na gaba bazatayi masa dadi ba.

Wani bi haka zai dingajin kamar ya saceta kawai a tunaninshi yasan wasime zata fahimce shi,amma kafin yace zaiyi wani abu akan hakan saiyaga wai har tolu yazo daukarta dan suna balain tsoron take dokar taher matuka, sumtimes kafin a tashe su zakaga har tolu ya iso da mota yana jiranta a bakin gate kusan kullum itace farkon tafiya gida

Ahaka Har saheeb yagaji ya dena zuwa kofar makarntar,karfin addua da saka idon da taheer yay akan rayuwar wasime sosai yayi tasiri wajen kareta daga dukkan wani munanan abubuwan da saheeb yake shiryawa akansu

Haryau wasimevBata mance saheeb aranta ba,amma dashike babu wani abunda ta nema ta rasa a gidan komi taher yana yi yasa tunanin shi yay sanyi acikin zcyarta…

…inyana da kudi haka zai bada dubu goma a ajiye ana tsakura ana bata 100 naira ko fiye da haka tana rikewa a hannunta koda zataji kwadayin wani abu ta siya,snn kuma ba a fashin saka mata abinci isasshe acikin schl lunch box dinta..hakan yasaka lamarin saheeb yay sanyi fidis A mind dinta jefi jefi haka yake dan fado mata aranta amma ba kamar da can ba,yanzu karatunta kawai ta saka agaba sabida tsoron masifar taheer.

Taheer dayaga jajircewan ta yaji dadi aransa sosai
Ahankli harya soma daga mata kafa sai ya soma nunawa kamar karatunsa ne suke shan masa kai yasaka baida lokacinta sosai,a yanzu bako yaushe zakaga yana tuhumanta ba sai time to time haka, Kuma he is impressed Da kaifin basiranta dan sosai ta iya mathematics Da computer science
“turanci ne kawai dai take dan tafka shirme” zokaga bullet in yace ta karanta masa passage” nan zakaji ana kwabawa ana cewa.. is was,i go i come,i see i saw “the monkey capke the igiya”….hada kalaman english na matukar bata wuya,wani bin haryaji kamar yy dariya..fannin islamiyama sosai take kokartawa dan tamkar yadda tasaka ranta akan wasa haka ta maida naciyar ya dawo kan karatun qur’ani,tafison shi fiye da boko sabida akwai competition kuma batason a barta a baya
takanyi bita sosai harsai bacci ya dauketa da littafinta a hannu..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button