FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana tare sauran hawayen ta jikinta a sanyaye ta gyada kanta ma bilti jin lallamin nata ya dan kwantar mata da hankli,cikin sanyin murya tace toh shikenan bilti naji zanyi hakuri.Allah ya sa ya dawo da wuri..nide wallh inaso inga ya dawomin…yafa dade..

Murmushi bilti tay tace Ameen swthrt duk karki damu ai abun kamar gobe toh yanzu gyara
Fuskar ki muje can kinga harma sun tashi za’a fara shirin wucewa gida …lets go.

Shashhare fuskanta tay ta dan kikkimtsa snn suka dawo wajen su prof hotuna sukayi dukkan su kamar family daga nan basu wani dade awajen ba suka koma gida……
Its not freee,300 via 0152983148 mohd sule suraya GTB 08060712446
7/25/22, 19:20 – Kawata: 55#
Endseries2

Bayan kamar wata uku da gama scndry schl din wasime sosai taga abubuwa sun fara canjawa agidan,tsakanin anono da prof saidai taga suna ta kuskus sunata tsare tsaren abubuwan da haryau bata gane menene ba.

Itadai tasan da akwai wani mutumin da kullum yakezuwa gidan sunaa fita tare dashi itace dai kullum ake barinta a gida,wata na gaba na kamawa ranar Alhamis da sassafe bayan ta idar da sallanta kenan Anono take sanar mata da cewa gobe gobe zasu tashi a wann anguwar zasu koma wata sabuwar estate mai kyau da aka bude wanda yake can ta hanyar mai lane din shigowa garin just few kilmtrs away daga asalin cikin gari mamaki wasime ta dingasha amma sai batay wani dogon bincike akai ba.

Ranar basu wani zauna a gidan ba kowa yanata busy da kayayyakin sa anata kimtse kimtsen abubuwa ana saka su ajaka,Kafin washe har sun gama shirya komi.

Washe gari karfe 10 saura na safiya suka firfito bayan har sunci breakfast dinsu suna zazzaune sai can ga horn din madaidaicin company truck yazo kofar gidansu ya paker.

Mai gadinsu malam liman ne ya shigo ya sanar musu snn ya tayasu debar kayyakin su zuwa waje.

Just Few luggages da suke bukata suka tattara aka sassaka a truck din
excluding All the old fixtures Nd furnitures dake tsohon gidan,su gado da katifa cushions hardasu kayan kitchen ma basu taɓa komi ba, mafi akasari dai tarkacen kayan sawansu ne da yan tarkacen gidan da dabaza a rasa bukatarsu acan ba.

Anguwar da zasu koma na dan nisa,kusan tafiyar 1good hr ne yakai su har sabon anguwansu inda makaken gidansu da taheer yay munching musu yake,ba tsayawa ginasa yay ba kudinsa na farko daya soma samu a shekran farkon na aikin sa ya soma zubawa dukka akan familynsa.

Gidan ya soma siya musu nd He make sure ya saka musu komi na morewa rayuwa aciki duk dama da sunan mahaifinsa ya siya gidan bada nashi sunan ba.

Tundaga waje suke ta kallon yanayin tsarin anguwar cos is quite arranged nd peaceful street,irin anguwan nan ne da wuya kaga wulgawar mutune yawancin manyan gidaje ne masu dogayen katangu dq rantama rantaman gates,Irin anguwan nan ne da kowa yake minding business dinshi babu mai shiga harkan kowa.

Adede kwana Akayi wani babban masallacin juma’a daf da mashigin anguwar,daga shi sai police station ata gefen hannun hagu Ata bayan su kuma manyan plaza plaza ne masu dauke da mini super markets.

Agaban wata babban ash colour gate mai girma da tsayi motarsu yay horn malam liman mai gadinsu na can yazo ya bude musu gate suka shigo ciki..

Duplex ne babban gaske sai parking space gari guda dake gefe.Babban compound ne dake dauke da shuke shuke da bishiyoyi masu mugun daukar hankali,kana ganin tsakar gidan kasan naira ta murzu anan
,makeken tsakar gidan na dauke da sassa sassa har guda biyu masu design da fenti iri daya,fentin irin oily white colour din nan ne da touch of ash awasu sassa kalar nada matukar dauke ido wanda kallo daya kamasa kasan fentin gidan mai tsadar gaskece,.

Tsakanin ko wani sassa na gidan akwai tazara mai dan tsayi tsakaninsa da dayan sassan,sashin farko wanda shi xaka fara cin karo dashi bayan shigowar ka daga gate din shine kamar asalin main house din,sashen badai girma ba don sashin ya fi dayan sashin girma sosai.

Dayan sashen dake gefenshi shine na anono,sashin madaidaici ne mai dauke da one room,one palour kitchen mai hade da store nd two toilets daya a daki,daya kuma a falo,Sashin anonon anyishi ne a matsayin muhallin mutum daya,already fankacecen palonta har an cancadeshi da one and half set na dark orange nd black colour leather cushions kalarsa irin kalar cutairns din dake zagaye da palon,an sassaka mata kayan kallo, madaidacin tv plasma sai babban black colour chinesse carpet da center table Da water dispenser.Babban daki guda dayane a site din shima an gyarasa yay fes gwanain ban sha’awa da sabbin furnitures,
set din Madaidaicin italian designers gado da mirror da wardrobe nd lockers,daga wayannan Babu wani tarkace a dakin hakan yasa daki yakarayin kyau bana kadan ba.

Babban sashin kuma shine inda prof oyiza zatay occupying,saidai shi bakamar na anono bane shashen yana da girma da fadi Site biyune manya aciki,nd each site is self contain yana da room nd palo da kitchen da kominshi aciki,sai one single room inbtween d two sites, inda ya kasance dakin wasime ne ita kadai,dayan site din daya kasance na taheer ne shikam a kulle yake basu budeshi ba.

An kawata babban falon gidan ne da 14 set of golden colour nd purple royal cushions,kowane set din kujera da guda bakwai inshi, da wasu hadaddun kayayyakin ado na zamani with exotic show glasses nd chandeliers.Sai babban dinning tables 35 inches mai kujeru shabiyu, da wall papers masu kyau da daukar hankli..sai daidai kun kayan ado na alatu wanda bazasu kirgu ba.

Hakama personal site din prof oyiza shima sosai aka narka nera awajen tsarashi domin kuwa an zuba mata wasu irin tsadadun lumtsatsun Arabian lush designers ne masu shegen kyau kyau da daukar ido komai na sashen ta is
Red nd black colour yanayin tsarin kayan nata kamar na Gidan sarauta.

Kamar yadda komi na gidan yake sabo kal kal
Haka ma Wasime ta fada room dinta da sabuwar zumudi tahau shirya kayayyakinta a 3 sides wardrobe dinta dan madaidaici komi na dakin ta is milk nd brown colour itama italian designers ne amma gadon ta bamai girma bane irin gadon nan ne na turawa mai tsananin laushi da tudu mai iya daukar mutum biyu kacal.

Yau kowa yana busy a site dinsa basu wani zauna ba har sai washe gari da suka hadu wajen karyawa,anan wasime takejin bayanin cewa taheer ne ya canza musu gidansu yasaka suka dawo nan..imagining take haryaushe ya samu kudi mai shegen yawa haka daya siya musu babban gida mai shegen kyau da aji kamar wani gidan gwamna

Kowa is so comfortable
Nd content a gidan masha Allah komai na gidan a wadace yake.
Ga 24hr ruwa ga wuta ga babban filin shawagi da jera motoci.

Bayan sati guda da komawarsu sabon gida wasime na kwance akan sofa a dakinta tana kan kkrin haddace suratul isra’i da aka bata haddar shafi uku daga ciki wanda shi za’a karba ran asabar da sassafe in sunzo..

haryau wasime bata kammala karatun ta na islamiya ba,dake an inganta ilimin da ake basu a Al’iman islamya session syllabus din islamiyar sai ya dena tafiya adede dana bokon,zai iya yuwa ka gama boko ba ka gama islmiyar ba,dan yanzu ana hada musu ne da littafai da programs programs daban daban na addini wanda manyan malamai suke zuwa su koyar dasu tauhidi,tarihi da hukunce hukunce har ma an bude sashen matan aure.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button