FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Saidai wasime bata koma can ba, haryau a sashen age mates dinta take halarta dan babu wanda ta taɓa gaya masa cewa ita mtar aure ce,najaha ce kawai tasani amma tuni ta fice a islamiya section din tun suna shirin gama sashen boko ta dena zuwa ta tsunduma a business din mamanta tana tayata saida abinci a cikin kasuwa, acewarta kudin da akazo aka karan ne yayi musu yawa shiyasa bazasu iya biya ba.

Fannin wasime kuwa ba’a taba fashin biya mata kudin mrkntar ba,dacan dubu biyarne islamiyar amma da mkrntar ya samu cigaba sosai sai fees dinsu ya dawo dubu sha biyar amma kuma ilimin da ake basu is really worth the pay dan sosai suke samun fikra da wayewa a fannin addini.

Bata taba sani ba amma kominta taheer yake biya haryanzu, dan harwayau inya turo kudi a acct dinta yake sauka,toh batada waya barema tagani,anono ce zata cire kudin ta bata daga bisani ma dataga ta kara girma saita mallaka mata Atm dinta kawai a hannu, duk wani abunda take bukata wani bin kafin tayi makanta ma zataga prof har tay mata,mostly Kudin acct dinta ya kasance kawai na biyan schll fee ne amma babu abunda ta nema ta rasa a gidan haryanzu.

Ganin ba a taɓa barinta ta rike wayaba yasa ta cireshi ma aranta kwata kwata bata taba damuwa akan saita riƙe waya ba.

Tana zaune ita kadai a daki tana famar bitan ta,
Idanunta a lumshe tana tunoda karatun tana maimaitawa offhead kamar da wasa taji kishin ruwa na damunta sosai.

Bata aje qur’anin ba har saida takai karshen ayan dake bakinta snn ta diro a hankli,ta saka bedroom sleepers dinta ta bude kofar dakinta ta fito daga ita sai wata doguwar rigar atampa peach colour ta saka hula baki akanta tana tahowa a nitse, gabanta ne ya wani fadi Data hango mutane biyun da suke tsaye acikin falonsu suna magana da prof dake zaune akan kujera.

Ahankli take takawa harta iso wajen su da sallama abakinta,kallon dayan mutumin ta dingayi a sace tana kkrin tuno inda tasanshi cos his face looks really familiar to her amma kuma ta kasa tunoda inda ta taɓa haduwa shi.

Da alamar Aika suka kawo ganin wasu manya manyan boxes awajen ankillace su a manyan kwali irin wrap boxes din nan wanda ba’a cika ma amfanidasu anan kasar sosai ba.

Daidai isowarta wajen sukuma suna shirin yin ma prof sallama,babu yabo babu fallasa wasime ta gaisa dasu daddaya suka amsata da sakin fuska.

Daga nan bata tsayaba ta wuce ta nufi fridge din kitchen ta dauko gorar ruwan sanyi ta bude awajen tasha harsaida taji dadai,da goran ruwan a hannunta ta fito ganin ba kowa a falon yasaka tay sauri tay wucewarta dakinta.

Littafan islamiyar ta ta tattara duka ta ajesu a mazaunin su snn ta hau kikkimtsa dakin ta kade gadonta ta sake gyarawa
Ta share dakin ta rage gudun Acnta ya dawo low snn ta kunna ma dakin sassanyar qamshin turaren wuta hadin kasar sudan a incent burner,kafin kace wani abu tuni dakin ya gauraye da wani daddan qamshi mai bada wani irin yanayi mai sanya ma zuciya nitsuwa.

Ajiyar zuciya ta sauƙe snn idanunta ya kaiga kan Agogon dake manne a jikin bangon dakin
,karamin tsaki tay ganin karfe takwas da rabi ne kacal,tay xpecting ace irin taran nan yay dasai tay wanka kawai tabi lpyar gado, amma sai taga kamr lokcin ne baya tafiya sosai.

Dauke kanta awajen tay tanamai Kokarin rage kayan jikinta domin ta watsa ruwa,tana cikin hakan sai kuma tay saurin dakatawa jin kamar ana knocking ata bakin kofar dakin,cikin sauri ta maida rigar ta taho ta wajen kofar a yanayin cikin Nitsuwa,a hnkli ta bude kofar ganin prof ne atsaye awajen yasakata dan sunkuyar dakan ta kadan ta tsaya gefe da sanyin murya tace yes mumy
,murmushi prof tay snn ta miƙa mata heavy box madaidaici guda daya data taho dashi,tace karbi wann aikan ki ne

Amsa tay da sanyin murya tanamai cewa nagode momy,atake prof
Ta juya tana cewa okay gudnite,batama bata amsa ba taga harta bace awajen,wani irin nauyi boxe din yakedashi da kyar take kkrin ciciibarsa ajikinta.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallon jikin box din taga an manna postal adress na Washington Dc,shigowa dashi tay cikin dakin acikin sauri ta ajeshi akan gadonta tahau yayyaga seal tape din da akayi wrapping din jikin kwalin dashi.

Agaggauce ta yayyaga su ta watsar a kasa

Masha Allahu tace jin wani matsanancin kamshi mai tsananin dadi daya bugi hancinta yanamai mata yawo har cikin kwakwalawa,zama tay agefen box batare da ta shirya ma hakan ba tanajin yadda gabanta ke faduwa kamar inta bude yayanta zata gani aciki

Atake idanunta suka kawo ruwa Wasu pack pack ta dinga gani acikin kwalin ajere kamar an mannasu da juna
hannunta ta dora akan neatly arranged parcels din,na farko data dauka ta bude taga set din kayan kwalliyane aciki na kamfanin mary kay da l’orels consisting of eye shadows,concelers,powders,primers,foundations,shimers nd contours
,gliters,pencils,liners,mascara..saida diffrent shades na lips gloss da lipsticks din Mac beauty,kyabe baki tay ta ajiye wann agefe,ta Æ™ara dauko wani parcel din ta bude anan ma taga differnt set of xpensive perfumes har guda uku,’black opium exclusive scent”,”rebelle’ by rihanna da kuma nude777, kowannen su acikin gidansa yake mai armashi,bude dayan parcel din tay yaga kayan su chokolates ne da candys,parcels mai dan girman tana budeshi taga white teddy bear mai tsananin kyau da pepper red necktie ta rike rose flower a hannunta da note din da aka rubuta “i miss u” da red heart ajiki,lui din idanunta dake lumshewa da budewa dakansa nakan rubutun ita kanta bata san sanda hawaye masu rauni suka soma tsilalo mata ba,dayan small box dake ciki ta daga,Da wani blue handky ta soma cin karo wanda yay kama da kamar ma manceshi akayi aciki..Bata bita kan handkyn ba ta bude dayan box din taga kwaline na Apple phone 13pro max kalar champaigne gold, wani irin gwalo idanunta tay waje Abaxata ganin ta riÆ™e abunda bata taÉ“a tsammanin sa ba

Acikin sauri da rudewa ta kai wayar kan hancinta tana shunshunawa jin kamar qamshin turaren sa daya saba shafawa ne ajikin wayar ya na tashi,tana kaiwa hancinta sai taji kamar ba ajikin wayar qamshin yake tashi ba,Sai can kamar wanda aka tsakureta ta kara kallon cikin box din sai ta saka hannu ta dauko handky din wanda tun daga dagoshi ta somajin daddan qamshin sa ajiki mai tsananin ratsa jiki da gigita kwakwalawa acikin wani yanayi mai nunnike da shauki ta rungume hankyn akan kirjinta tanajin kamar yayanta ta rungume

Wani tsamm tay da idanunta ayayinda hawaye masu yawan gaske suke tuttuluwa akan fuskarta suna saukowa yuuuuu bisa kumatun ta suna diddiga.

Sulalewa tay akan gadon da tsananin sacewar jiki tare da hankyn wanda ta riga ta manneshi kakkam akan kirjinta haryanzu idanunta dake lumshe babu abunda yake famar yi sai ambaliyar ruwan hawaye.jikinta a matukar muce ta jawo hankyn ahnli snn ta dora akan fuskarta ta rufe fuskrta dashi wasu kanunun nishi ne suka rinka kufce mata tareda sauke ƙakkarfan numfashi.

wani irin kasala ta dingaji yana dirarta mata wani irin feeling din body weakness na dada ragwabar mata da sassan jiki,a lokaci guda iskar datake shaÆ™a ya sauya salonsa gabaki daya ya zamto na zallan qamshin turaren sa mai kkrin zautar da ita ayayinda kowani kofofin sha’awa ya dinga buduwa wani abu ta dingaji na mata yawo yarrr yanabi tun daga tsakar kanta har izuwa tafin kafafunta tanajin matsanancin bugun zuciya mai azazzala rudani,har wani sanyi sanyi takeji ajikin ta kamar wanda ake mata fifita,Not only the room but the whole of her soul nd body is feeling his presence around her so so badly nd intense,kirjinta na bugawa da tsananin karfi harji take kamar tana bude lumsashun idanuwanta zata kalleshi a kusa da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button