FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Fada suka dingayi even thou she is d one hurting so badly shikam baisan ma yanayin hakan ba
Shide yasan yace mata inhar zata zauna a matsayin matarsa toh lallai saita hakura ta zauna tareda raxia Abu.

Ya koma gida ya barta anan kuka da firgicin duniyan tayi,bata taba ficewa a hayyacinta kamar na wannan lokcin ba,kusan evry hour sai ciwonta ya tashi inhaler ya dawo mata tamkr jakar hannu bata iya rabuwa dashi.

Abu tun na kamar almara taga tun da ya tafi bai dawo ba,ita kadai take zama anan gidan kullum cikin kuka da firgici ga tsananin kishi yasa tanaji kamar za ta hadiye zuciyarta ta mutu.

COMPLETE DOCUMENT IS 500 VIA O152983148
MOHD SURAYYA SULE GTB CHAT 08060712446
7/30/22, 20:05 – Kawata: 76
Razia ta dawo zamanta a asalin dakin kwanansa saidai basa wani magana ko kasancewa waje guda,sabida duk karfin tsafinta bai hanashi yana sallah ba.

Saidai kawai bazaiyishi ne akan lokaci inda ya saba ba,amma yikam dolene saiyay.

Iyakar tsafinta yakanyi tasiri ne in tana son ya walakanta mamanshi ko matarsa kamar yadda saheeb yakeso din,but kwana biyu dataga dukan su babu wanda ya leko gidan yasaka tay nesa dashi,saidai yay wanka yaje aiki ya dawo yaci abincinshi awaje gabaki daya yamance da mahaifyarsa da kuma matarsa wasime.

Aka bar wasime dabin asibiti kusan kowani ranar Allah acikin rashin lpya take,saidai haryau bata farajin haushin mijinta ba tukuna gani take duk abubuwan da suke faruwa karya ne wann ba mijinta bane data sani ,taheer bazai taba walakanta ta ba bare kumaa mahaifiyarshi.

Ta kikkira prof awaya bata samunta harta gaji ta dena neman layinta tay mata uzuri,sosai taga tashin hanklin da bata taɓa gani ba awajen matar nan,bata tabbatar da cewa taheer shine rayuwar prof ba saida wannan abun ya faru dan kuwa tabbas ita tafi ta girgiza tafita jin zafi takuma fita borancewa.

A da can ma takanyi takatsantsan dan kar wasime ta rabata dashi saigashi yanzu a lokci guda wata banza karuwa tay mata mai kankat abunda takeji makanta tsoro kenan iyakar rayuwanta,randa xa’a ce mata wata Æ´a mace ce zata rabata da danta taheer,bata sani ba ashe qadadarren alamari ne wanda bata taÉ“a tsammanin zuwansa a lokacin daya zo mata ba.

Tsantsar zuciya da fushi da rikicewar tunani shiya tunzira prof ta tafi garinsu kogi,itama a ranan data isa ta ragwabe, jikinta ya dawo babu dadi uwar rikonta ne take fama da ita kullum suna kwance agadon asibiti sabida ciwon hawan jini da ta dorawa kanta.

Anan ma wasime bata rabuwa da inhalerta kullum yana hannunta tana rike dashi sabida yawan sarkafewan numfashi datake fama dashi.

Kullum ita kadaice a gidan,bata da kawaye na kut da kut wanda zata iya kai kukanta wajensu su koda su tayata rike nauyin wani abun,babu iyaye,babu kuma yan uwa bare ta samu wani makafa,innonon data sani tay mata nisan da kota nemeta ahalin yanzu hala bazataji ta nan kusa ba.Wa bilti kawai ta dinga turawa sako akan tana bukatar ganinta.

Yau kusan sati guda kenan bataga reply din biltin ba,abun duniya yabi ya isheta duk tabi ta cusa damuwa da bakinciki mai yawa acikin zuciyarta gashi haryau tanajin radadin tsananin zafin soyayyar mijinta acikin ranta wanda komin fushinta bazata iya yin yaki dashi ba.

Ranan asabar Bilti ta shigo garin kaduna,tana dawowa daga lagos din bata ko huta agida ba da yammaci ta iso gidan ta tarar da ita a daki lkcin ta gama kuka kenan ta shiga bathrum tana amai lkcin cikin jikinta nata na watansa na uku yana balain gigita mata yanayi.

Suna hade ido da bilti ta fixgo a guje ta fada ajikinta ta rungume gameda sake wani matsanancin kuka mai tsumayi…jikin bilti duk yabi yay sanyi duk dai ta karanta matsalar a cikin sakonninta amma bata yarda ba,saida tajita yanzu tana wann kukan mai mugun azabatrwa da saka tausayi.

Sunfi minti sha biyar rungeme da juna tsabar rawan da jikin wasime yake atake idanun bilti ya ciko da ruwan hawayen tausayin halin da wasime ta shiga ciki ya mamaye mata zuciya.

Da kyar ta bambarota ajikinta tajata sukayi bathrum ta wanke mata baki ta tsaftace wajen datay aman snn suka dawo dakin,zama bilti tay a bakin gado tare da jawo ta jikinta ta rungumeta izuwa kan kirjinta tana rarrashinta akan ta dena kuka ta gaya mata abunda ya faru.

Wasime tana kan kuka da kyar ma ta iya budan baki ta fara bawa bilti labari tiryan tiryan kusan sau biyu asthamnta na tashi tsabar damuwa da tsinkewat tunani da abubuwan suka zo mata dashi tanacikin bada labarin amma bata fasa sakin kuka sosai ba.

Ta karashe dacewa Bilti yaya na ba haka yake ba wallh ba haka yake ba..
Nasan bazaici amanata ba,bansan meyasa yaje yay aure kuma ya walaknta ni da momy akan matarsan ba.
Nide haryau inaji ajikina
Cewa zai dawo cikin hayyacinshi wannan ba halayayyr yaya na bane
Koda zai yi auren bazai taÉ“a walaknta momynshi ba..tunda ya tafi wajenta kofa kirata bayayi tunda ya tafi bai kara dubani bayan yasan ba lpya nake dashi ba…tana fadin hka tana kara fashewa da kuka sosai.

Ita kanta bilti rasa abunda zatace tay sabida abun ya balain daure mata kanta.

Batace komi ba ta lallabe wasime sosai tay sallah,da kyar tasaka ta taci abinci ta dinga mata aduoin har tay bacci.

Zama tay a gefenta tana ta tunanin magangunta anan itama ta kwana dan tausayin wasime bazai kyaleta taje koina ba, washe gari da sassafe ta dauki wayarta ta kikkira layin prof dakyar ta same ta,ganin wasime nakan bacci yasata taje can waje sukayi magana mai tsawo tana bata hakuri tanacewa da bata yanke hukuncin tafiya tabarsu acikin wnn halin ma

Cikin magiya tace Anty oyiza kituna fa wasime yarinyace karama kuma bata da kowa kema kin tafi kin kyaleta acikin wannn yanayin datake ciki gaskiya baki mata adalci ba..

Prof dake kan jin tsananin zafin abun tace ita babu ruwanta taheer ya gaya mata maganan da harta mutu baxata mance ba ,yace zaicu mutuncinta akan wata Æ´a mace dan haka dole ne ta cire hannunta akan dukkan abunda ya shafeshi,in wasime taga zata iya saita koma gidansa su kasheta ita bazata iya kallon rayuwar taheer ahaka ba.

Daga biltin har uwar rikonta nacan fada suke mata akan tay hkri ta fahimce abun ta nemawa danta mafita amma zuciyarta yay rauni sosai bata ma iya gane gaskiya acikin furucin kowa.

A haka har suka hakura suka kyaleta,ya zamto babu wani option wa bilti face ta zauna anan din tare da wasime kodan ta nema mata mafita.

Hakan kuwa akayi tana zama da ita abubuwa suka somayin sauki wajen wasime,kullum acikin nasiha take mata
Tana mata wa’azi akan jarabawar rayuwa da jarabawar aure wanda ko wacce Æ´a mace a duniya saitaci karo dashi bazai taÉ“a wuceta ba.

Tace mata ta dauka cewa wann qaddararren
Lamari ne,tay addua Allah yasa ta cinye wann jarabawar tata,snn tay biyayya ga abunda mijinta yace wata rana komi zai wuce sai labari.
Kullum suka zauna saita bata labarin rayuwanta yadda aurenta ya mutu bata da uwa bata da uba da tsananin tsangwama da wahalar datasha da rayuwa ta kuma fuskanci kaskanci,duk ta kwashe sirrinta ta gaya ma wasime ko dan ya zamto kamar wa’azi agareta.

Snn ta tursasa ta akan kara zage damtse wajen ibada da karatun qur’ani musammn ma a duk sanda taji hanklinta na tashi.

Kwana biyu wasime ta samu nitsuwa sosai atattare da bilti,har tana dan daurewa taci abinci sede duk hanklinta baiya jikinta,a duk inda taheer zai kasance bazai wuce yadda takejin presence dinshi a cikin zucyarta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button