FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Share pls

Na kudine
Its 300# please subcribe

via 0152983148
Mohd surayya sule
GTB,nd send ur evidence to 08060712446
Or mtn Pin.
7/25/22, 19:19 – Kawata: FITAR RANA…
……faduwarsa

BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.

No 7

Da uban sauri malam musa ya doshi hanyar bakin famfon yanamai
kwallara ma tolu ƙira kamar wnda ya kama barawon daya dade yana nema,wajen da suke tsaye ya dosa yana jefa kafafunsa cikin gaggawa tamkar wani babban almari ya hasasho.

tunkafun ya tsaya yafara azazzala wa wasimé masifa yana cewa:
“ke yar bilti me kikeyi anan?maza wuce kiyi gida, ahhhhhh kagane mini shashashar Æ´a.wani rau rau da idanunta tayi kamar wacce zata fashe mishi da kuka ta zumburo Æ™aramin bakinta gaba jin yace mata shashasha aranta kanbu?”bzaki wuce kiyi gida ba..adan tsomare ta tsaya snn ta amsa “nifa wanki nakeyi ai bangama ba.Cikin yanayin tsawa da hantara Malam musa yace”Ke yimin shiru awajen wani wanki ke kika iya?,ki wuce ki bar nan wajen nacemiki. na tabbata bilti batada masaniya akan fitowarki, ahaka ne ake wankin kinfito ba kaya ajikinki..?

kallon kanta ta shigayi jin yace babu kaya ajikinta bacin ga zani ta dora a kirjinta wani tsaki taja acikin zcyarta ta zumburo bakinta ta haÉ—e ranta sosai,ganin ya zare mata ido taja tay tsinin baki,batace uffan ba cike da saiÉ“i ta dauki bokitinta da sauran kayanta ta barsu a wajen suna tsaye suna kallonta harta bace maganin su..,”

Tolu daya tsaya galala yana kallon musa cikin yanayin mamaki yace ..”musa!na why u kon dey shout ontop dis small girl metayi maka?Tolu ya tambayeshi a mamakance.

malam musa dake tuÆ™a masa wani tuwon harara bai tsaya amsa shi ba ya shiga nunasa da yar yatsa ransa a mugun bace sabida a duniya babu wanda malam musa yake bala’in dreaming samu arayuwarshi kamar bilti,ya É—ade yana kaunarta acikin zcyarsa amma haryau babu wanda ya fahimce shi sabida ko a ido bilti ba sa’arsa bane bare ma a shekaru..

Iya inda zaka ganosa Daga zaran Abu ya shafi bilti sai kaga ransa ya harzuka ya baci,hararar tolu yakeyi kamar zai haÉ—iyeshi,yace
“Kai wallhy ka shiga taitayinka..katon banza katon wofi kawai.. kai mai kakeyi anan din?

tolu zaiyi magana ya datse sa da wani irin kallon baraxana
…tolu zaka fara halin naka ko?

girgiza kai tolu yay cikin dago abunda musa yake nufi snn yaja wata doguwar sautin ohhhhhh ya dora hannu a kugu

Hararsa shima yay,snn ya soma cewa “musa “musa, musa,wato saboda kamaida ni dan iska,harni zaka..so u think i came to toast dis cunkuli girl.?u dey mad?
U no dey reason..oloshi
Kaci ubanka..

malam musa bai kyalesa ya karasa zagin ba yace”Eh mana,zuwa kayi ka ruÉ—eta danta soma shiga dakinki,yo me za’a fasa wai kunu awani gida.. tolu waye baisanka ba, har kananan yara irinta kana kwamushe su da jarabarka hakane ko ba haka ba?ka amsa ni jarababbe!

“tsabar haushi tolu bai tsaya amsawar ba yakai hannu zai doke hancinsa da sauri malam musa yaja da baya .yana huci yace “Sai nace maka abunda ya kawoni nan kenan?

cike da izgilanci malam musa ya amsa”..i dontu kiya wat bring u por hiya…toh dai ahir dinka da yarnan…Wannan tafi karfinka ta gidace wallahy kayarda naga kadorata akan cinyarka ko kana matseta nida kaina saina tona maka asiri! duk abunda kake aikatawa agidan nan saina fadawa oga taheer.

Wani ihu tolu yasaka game da dora hannunsa akansa..”Ah ahhh now musa haba!!Wannan wani irin wasa ne kake yimini haka aah ahh na, Kaima kasan bana son wannan yarinya..i no wan toast her na cry cry girl she bi..inda kaganni anan akwei babban dalili daya kawoni..,hannunshi ya kama sigar lallami ya soma jansa suka nufi ta bakin gate Yana cewa..’u seee baa Inkanaso infada maka guluma kazo muje room dina,i sweara gwad I get shicken nd juice for u i knw say my man go chop am she bi?…

wara idanu malam musa yay jin ance kaza tuni miyau dinsa ya kawo, da gaske kakeyi akwai kaza da jus dakinka?wani hamma ya doka tunkan ma tolu ya amsa,dan malam musa baƙaramin maitar kwadayi Allah ya zuba masa ba ,shi weak point dinsa kenan kahadasa da kayan kwamulashe shiyasa tunda tolu yagane hakan ya samu lakarsa yana sheƙe ayarsa da yanmata son ransa agidan..haka suka wuce dakin tare sunata surutai sauran kazar dayay amfani dashi ya lallabi yarinyarsa jiya ya bawa musa badon yaso ba musa kuwa yazauna ya cinye tasssss yabar masa ledar awajen yay gaba.

Kafin nan suna cikin daki wasime ta salalo cikin sanda ta cigaba da wankinta,daga cikin gida kuwa har bakwai shaura snn bilti ta shigo dakinta dubata,da bata ganta ba yasata yiyuwa waje cikin sauri.tasan dai babu inda wasime take iya zuwa acikin gidan sabida tsoron taheer

Hangenta datayi Tana durƙufe agaban tap tana ta shafa kayanta sai abun ya bata mamaki,cikin sauri ta ƙaraso har ta tsaya akanta bata hanƙara ba sabida zuciyarta yay nitso sosai acikin tunanin kawayenta na kauye.

“Wasime mekikeyi anan?
Barin wankin tay ta juyo adan razane,ganin bilti yasata sauke ajiyan zcya Har Æ™asa ta rusuna cike da biyayya tace “ina kwana bilti?amshe bokitin da kayan dake hannunta bilti tay snn tace lpya lau tanayi tana dan dudduba kayan adabarance, taga dai ba laifi sun dan fita,kanta na can Æ™asa.. bilti ta dubeta tace”ke kikayi wankin ne?a hnkli ta gyada kai snn tace eh..amma dai kinsan bakida lpya kika fito nan sassafe kina taba ruwa ko? ashe dai bakiso akaiki wajen anononki”…da sauri ta dago kanta ta kalli biltin cikin langwabe wuya,tace “ahhh inaso…dama ai ita tacemin ina yin aikina kuma naga acan kauyen mu ina yin wanki.. ki duba aina iya ko..shine nace…bilti ta ce to ya isa haka abar labarin muje ciki kawai gashi duk kin jike jikinki..batayi musu ba ta wuce ciki bilti ta nufi inda clothline yake ta karasa shanya mata kayan sann ta shigo gidan itama

samunta tay harta cire jikakken zanin jikinta ta ratayasa ajikin kofa da daga ita sai yar panties dinta tana zaune abakin gado,bathrum bilti ta shiga sann ta dauko dan karamin towel daidai size dinta ta bata dakanta ta dorashi a kirjinta.

Hakama wajen wanka taganta da axamanta tana tayata yin komi
Da wasa wasa kwana biyun nan bilti ta soma fahimtar cewa da akwai home traininig sosai ajikin wasimé duk da kasancewarta yar karama amma da alama ta iya abubuwa dakanta.

Fahimtar hakan yasa ta fara kyaleta da wasu abubuwan kamar share room dinta,dan wanke wanken da yay shaura saita bata ta wanke hartazo ta soma sabawa sosai wani abunma basai angaya mata ba.

Agidan bilti became her best friend nd mother
Dashike bakasafai ake cin karo da Alhj qasimu da matarsa ba,bare ma ajega dansu dahiru dayanzu baiyason ma shigowa gidan sai can cikin dare,he is alwys occupy da karatunshi.
Rayuwarshi Daga school sai hospital barinma da ake hada musu harda military training a school din nasu yanzu.

Hanklin wasimé na kwance, saidai fitsarin kwancen datakeyi ne yafi daga mata hankli,wani bin kunya takeji sosai acikin ranta musamman in matar gidan ne taxo dubata ta tsinceta a haka to ranar wuni zatayi tana jin nauyinta a kirji.

Tasha kokawa bilti damuwarta akan fitsarin datakeyin amma haryau basu fahimce cewa Sanyin A.cn ne yake sakata acikin wann yanayin ba.

Gata ta kasance yarinyace mai balain son tsafta,haka zata lailaya gadonta ta share dakinsun fess,kuma tasowa datayi acikin fulani yasa take da wannan alhininsu na yawan jin kunya gata da kawaici sosai..in bilti ta fito wanka haka take sulalewa tayi waje ta tsaya a bakin ƙofa harse ta kammala saka kayan snn ita zakaga ta shigo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button