FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cinyoyinsa a mammatse ya bar kofar gate din
Bayan babe din ta wuce

Tsabar jaraba Bayan gida ya wuce direct yay Wankan tsarki snn ya doro alwala yay sallah ya dan nemi waje ya kwanta amma duk da haka hanklnsa ya kasa kwanciya gabaki daya ruhinsa ta kwadaita da son samun macen da zata debe masa kewa shima,sai juye juyensa yakei shikadai yana tunanin ko shima yace ma tolu ya samo masa dirarriyar mace irin wannan ne yau shima yadan rage zafi da daddare,but no…zuciyarsa bilti kawai take so kuma take sha’awa..ji yake kamr inbai sauÆ™e niyyarsa akan bilti ba hala bazai taba samun gamsuwa ajikin kowata ya mace ba.

A fannin taher kuwa yana kammala tsayuwarsa agaban mirror ya shafe jikinshi da soft body lotion nd oil saboda yanayin wedan is queit cold,ahnkli ya bibbi jikinshi da dadadan turaruka masu sanyi marasa karfin qamshi,a nitse ya bude wadrobe dinsa yanamai karema jerin kayansa kallo.

Hannunsa yakai kan wata orange polo shirt ya cirota waje ya hadata da wata black pants na khaki sabida anjima kadan yasan zai iya wucewa wajen training acikin barracks dinsu.

Soft Canvas mai kyau ta kamfanin adidas ya saka akafafunsa ya karkare kwalliyarsa da saka agogo snn ya kimtsa dakinsa yayo waje.

Lumtsatsub Idanunshi nakan kowani sashe na gidan,gani yy Waje yay fes fes gwanin sha’awa ko ina yana kamshin turaren wuta, Kallon ko ina yy da gefen idonshi cikin nitsatsiyar takunshi mai daukar hankli snn ya nufi dakin bilti kai tsaye,tura kofar yay ya shige ciki kai tsaye baiyi wani sallama ba yaja ya tsaya daga nan yana kare ma wasime kallo ,lokacin wani uban juyi wasime takeyi cikin baccinta gabaki daya jikinta ya jike shatafff da fitsari nayauma saiyafi na koyaushe sabida ba sau daya ba ta tsula fitsarin ajikinta.

Daga idanunwan shi yy a miskilance ya kalli agogon bango,yaga karfe bakwai da rabi ya kusan wucewa tsaki yaja yanamaijin bakin cikin yadda bilti take kyaleta tayo bacci har i wannan lokcin da alaman ba a tursasa ta tayi ibada,ransa a dan bace ya karaso bakin gadon yadan tsaya kadan yanamai kallon kyakkwan fuskanta dats so innocent nd captivating .

Wani abu ya dingaji mai nauyi acikin zuciyarshi
Gabansa na faduwa a cikin sauri ya dauke idanunsa akanta snn ya kai hannunsa kan bargon a hankli yana shirin yayewa.

Yana dora hannun sa akai wasime tasoma juye juye jin inuwar mutum akanta da wani abu kamar qamshi qamshin turare mai bala’in dadi da ratsa zuciya, ahnkli ta kyallaro idanunta daya cikin gigin bacci sai caraf suka hade ido,suna hade idon kuwa tayi sauri ta rufe nata idon a tsorace kirjinta na wani bada sauti guf gufff yana bugawa da uban karfi,

Fasa yaye bargon yay ya koma ya tsaya gamida harde hannuwan shi asaman kirjinsa snn yaja baya ya tsura mata mayun idanunshi masu tsoratarwa ya cigaba da kallonta,so yake yaga ko zata tashi ne koko bazata tashi ba,gabanta ne ya dinga faduwa jikinta ya hau karkrwa, nan da nan ta matse idanunta gam gam gashin girarta sai rawa sukeyi dakansu, cikin rasa yadda zatayi ta bude idanuwan ta kawai ta kallesa fuskan ta a takune gwanin ban tausayi,wani babban tashin hanklin bai tashi ziyartan ba saida ta fahimci cewa ajike jagwab jilkinta yake da fitsari, aikuwa batasan san da idanuwanta suka soma saukar da ruwan hawaye ba”idon shi ya wara akanta snn ya dada turmusaa fuskan sa, yace ke?kankame jikinta tayi da bargon ta rushe masa da tsortaccen kuka,jan bargon yay ya watsar a Æ™asa,da uban gudu ta ja da baya baya ta koma can dungu ta takune kanta sosai tana rabza kuka….

Hannunshi ya saka a aljihu snn ya tsaya a tsaye cikin daka mata tsawa yace “ohhhhhh wato kin karayin fitsarin kenan ko?…cikin firgita da tsoro ta girgigza kanta tana cewa “a’a..
A’a…ban . .wallhi ban sani ba…yo ba shine ya fito ba,.. nifa bansan nayi ba…dan Allah kaya hakuri karka bugeni..kuka sosai takeyi tana maganan Uwa har anbugetan.

Ya bata ransa yace.
“Sauko nan..
Tafara jan jikinta ahnkli cikin saibi wani tsawa ya kara daka mata yace “are u mad? ma ubanwa kike batawa lokaci,”a hanzarce ta zube a kasa ta tsuguna jikinta duka na rawa rawa.

Ki tashi ki tattara kayan nan duka ki biyoni dashi
And stop dat nonsense ki dena cikimin kunnne na da kukan banza kinaji ko? Me aka miki da kike bude wa mutane baki? Wato kin raina ni ko? Yi yay kamar zai wanka mata mari a fuskanra,da gudu taja baya a gigice nan da nan ta shiga goge hawayen nata tanamai hadiye kukan dan dole.

Da rawar jiki ta mike tsaye snn ta aikata duk wani abunda ya umarceta datayi,.ta fito da kayan fitsarin ta hada da bedsheet dinta ta rike jikinta sai bari kawai yakeyi

Zubasu anan kije kiyi wanka kiyi alwala.

Cikin sauri ta zubasu awajen ta koma bathrum agaggauce tayi wanka sharp sharp tanakan shirin yin alwala saigashi ya bude bathrum din ya shigo.

Wani faduwa gabanta ya karayi tanajin kamar ta hadiye ranta ta mutu dan tsoro,”haka akeyin alwalan? Daga inda ya tsaya ya jefo mata tambayar snn ya karaso fuu kamar zai hadiyeta.

Ji take kamar zata rusa ihu

Yace “Tambayarki nakeyi!

Wani sassanyar Kuka ta zakar masa cikin sheshehka tarasa mema zatace kawai sai tace
“Yaa banfa iya bane…shiru yy baice Mata uffan ba..har sanda ya tara ruwa a fetcher.
Snn ya juyo yace mata
Me ake farayi kafun ayi alwala,dan shiru tayi snn ta makale wuyarta a sanyaye tace tsarki”
Ya dago kai yana kallon cikin idanunta yace yaya ake tsarkin,kanta ta sauke can ƙasa tana mai fidgeting fingers dinta jikin jin tsoro da kunya
Ganin haryanzu bai dena kallonta ba ta dago kanta ahakli cikin dauriya tace
“Bayan kayi fi..fffitsari..
saika wanke wajen da ruwa…ya hade rai yace sau nawa.Hannunta ta kama tana wasa dashi yana lura yaga ta kirga sau uku,baice uffan ba can Snn ya dauke kansa akanta yace daga nan kuma sai yaya?.tsuru tsuru tayi da idanunta alaman bata sani ba.

Kunnenta ya kama slighty..yace”Kinaji na ko? Da muryan kuka mai ban tausayi ta amsa da eh yace Daga yau idan kinzo tsarki nitsuwa zakiyi.Ki wanke wajen da isashen ruwa sau uku sannan kibashi secnd uku sann ki tashi ki wanke hannunki saiki debo ruwan alwala…

Kin ma iya alwalan kuwa? Girgiza kanta tayi cikin tsananin tsoronsa snn tace “eh,ta kuma cewa a’a”…nan ma ya koya mata shi tsala tsala verbally and practically saida tayi alwala agaban sa kusan sau takwas yaji ya gamsu sann suka fito.

Zani ta dora akan towel din ta dauko hijab ta saka sann ta yaye towel din ta ciki ta ajeshi akan gado,kafin nan harya shimfida mata sallaya
Yana tsaye harta kammala sallan ta raka’a biyu,sallan safiya,.
tanayin sallama suka hade ido yace na baki minti biyu kisaka kaya kizo yanzun nan ki same abakin tanki.

Yana juya baya ta mike tsaye cikin gaggawa wani irin rawa jikinta yakeyi tsabar axaban tsoron sa datakeji acikin zcyarta ,agaggauce ta shafa mai ta saka wankakken pants dinta tabita zura doguwar rigan atamfa A shape,snn ta kwaso kayan fitsarinta da zanin gadon a gurguje taje wajen ta same shi.

Samu tayi harya karkada omo acikin ruwa yana zaune yana jiranta,koda ta iso wajen ko kallanta baiyi ba ,jikinta a mugun sanyaye ta karaso gaban sa ta ajiye mishi kayan fitsarin ahankli ..”

“Jeki can ki tsaya, ya
Mata nuni da can gefe inda rana yasoma haskawa da kadan kadan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button