FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Najaha ma tana ganin hakan saita biyota cikin sauri, wasime tana shiga itama tana shiga..dukan su biyun suka shigo kusan atare.

A can Bakin toilet suka tsince shi yanata kwaza aman tea din daya zuka

wani bangaje kafadun najaha wasime tayi ta kutsa kanta Cikin toilet din ta tsaya akan shi,aciki kulawa ta isa gareshi cikin salon makircin dabata san daga ina yazomata ba tahau tsugunawa tayi kusa dashi tasaka lallausan hannunta agadon bayansa gently tana patting din bayansa tanai masa sannu cikin sanyin murya mai nuna ta damu dashi sosai
Bata dena ba harsaida tarin yadan tsagaita masa.

Debar ruwa tay ta tsaya akanshi tana zubo masa ya amsa yana wanke fuskarshi da bakinsa.

Yana kammalawa tarin ya soma dawo masa kadan kadan,kan gadon sa ya nufa ya dan kwanta baice musu komi..

wasime ta wani harÉ—e fusknta tayo kan najaha game da jan hannunta a fusace kamar waccce zata figeta,a mugun fusace ta wurgo ta har can izuwa bakin kofa..

Harde hannunta tay akan kirjinta tace ke wai mikaka saka ma yayana ne acikin shayin nan naki

Najaha datay mugun tsorata da lamarin kirjinta na bugu tace wasime wallhy bansama sa komi ba.

Juyawa a hargitse najaha tay ta koma falo taje ta dauko tea din ta mika mata tace gashi kisha kiji ni wallahi ban sakamai komi ba.

Fauce tea din wasime tay a hannunta takai bakinta ta zuka kadan snn ta wani tofeshi da karfi
Akan fuskar najaha

Makaryaciya kawaiz azzzalumi najaha meye haka wannan wani irin sugar kika saka masa haka? innalilihai wa inna ilaihi rajiun najaha ashe kashe shi kikazo yi?..

Najaha dake krin yarce shayin da aka fetso kan fuskarta tun anan taji yawan sugar abakinta sai taji ta kara tsorata

Wani cakomo wuyarta wasime tayi ta dana mata maruka masu kyau akan fuskarta, cikin wani masifafyar diri tace
toh wallh tallahi sainaje na gaya masa kece azzaluman da kike so ki kashe shi.

munafuka kawai annamimiya…karbi tea dinki nikam Allah ya toni asirinki

Jiki na rawa Najaha ta amsa tea din ta kurba
Dan bazata iya tuna yaushe har ta loda ma taher suga a tea dinsa har yay yawa hakan ba

Ta inda wasime take shiga bata nan take fita
Sai diri take cikin masifa tana cewa”munafuka Ai kinsani sarai wallh dagan gan kikai,tun farko saida na fadamiki cewa baya son sugar amma saida kika saka masa danke azzalumace toh banda mugunta meyesa zaki loda masa yay yawa haka wato anga na banza ko?

Matsiyaciya kawai annanamiya Ai wallhi munafurci dodo ne maishi yakeci

Cikin kuka sosai najaha tace “ya isa haka wasime ya isa haka..ni wallahy bansaka mai wannan sugar ba,karya kike min..saidai in kece kika zago kika saka bansani ba.

Tureta wasimn tay ta fada har kasa cikib zafin rai tace kikace mene?
Dan ubanki sharri zakiy min..yaushe kika ganni ina aikata hakan?ko angayamiki ni makira makaryaciya irinki ce.,koda shike abunda ka sabayi ma wani aidole kay tunanin shi za’ayi maka…kin dauka bansan ke munafuka bace..
ubanwa ya baki lambar wayar yayana?in dafa abinci na dan ubanki ki kirasa awaya dan kin raina ni hardace masa ke ce kikayi?wallh akan haka saina miki shegen duka anan najaha inkin isa ki tambayeni

A fusace najaha ta tashi suka soma cacar baki kamar zasu daga gida suke haura kan juna da zage zage.

“Inke ba munafuka makira bace meye na boye ma yayana gaskiya
Kullum saiki karbe min abinci na kice za kikai masa,ashe makirci da sharrin ki kawai kike kullamin awajenshi
Toh Allah ya toni asirin ki
Na ganoki..duk wani abunda kikemin nasani
Kuma dagayau ke ba kawata bace dan bazanyi kawa da munafuka irinki ba.

Acikin haka kowa yake fidda abunda yake boye acikin ransa gabaki daya wasime saida tay kaca kaca da sirrikan najaha datake boye wa.

Tun daga kan karbe mata abinci har izuwa karyan da tayi mishi jiya akan ita dafa abinci.

Wasime was very upset
Masifa da hargagi take kamar wata zaki mari da yakushi babu wanda najaha bata karba awajen ta ba

Har najaha ta gaji da kare kanta ta soma amsar duk wani laifukan datayi tana fadin duk wani makircin data shirya akan wasime dakanta danta cusawa wasime bakin ciki

Basu sani ba Ashe taheer ya fito tuntuni yana labe abakin kofar falon yanajinsu,sabida yanayin
Fitarsun dazu bai yadda da shi ba..aikuwa yana isowa wajen yagane ma idonsa halin da suke ciki

Bayan najaha ta gama tonan asirin kanta,ganin wasime bata girgiza ba saitaji tsoro ta soma rokon wasime akan tay hakuri ta saurare dalilinta.

A tunaninta kawai gwara ta fada mata son taheer takeyi,shiyasa ma take mata hakan danta samu shiga awajen sa amma badaniyar bata ta awajen shi takeyin hakan ba

Kishi da fushi da bori duk ya rufe idanun wasime
Haka taki fir ta saurare dalilinta.

..kowacce acikin su tana kuka,wani turata wasime takeyi waje tana janta tana kuma figar kanta kamar mahaukaciya

“Allah saiya sakamin Najaha,ashe halin ki kenan! ananmimiya kawai munafuka dani dake har abada get out kuma Karna kara ganin kafarki a gidanmu..har waje ta kaita ta turata kasa sanda tay tumble ta gurje hannunta.

Jan gate din tay a fusace ta saka lock ta ciki wani fuuuuuu ta doshi hanyar shiga cikin gidan tanakan gunjin kuka..

Tin Kafin ta shigo ciki taheer yabar jikin kofar yaje ya zauna akan kujera yay kamar baisan meya afku ba

A bakin kofa ta tsaya ta share hawayenta tsaf danma kar gane, kamar batay kuka ba haka ta shigo ciki, kanta a kasa tay sallama ta bude labulen falon a sadade,gabanta ne ya fadi data gansa xaune awajen, batare da ta kallesa ba ta dauke kanta ta kara dagaba cikin sauri zatahau matakala ta wuce sama
Dakinta

Lumshe idanunsa yay snn ya bude muryansa a shaƙe ya kira sunanta yace ke wasime zo nan

bata ranta tay ta dawo
Zuwa gareshi ta dan rusuna

Batare da ya jira ba yace “ina kawarki najaha?

Kirjinta ne ya buga ta dada harde ranta tace nima bansani ba..

Wani Tsawa taji ya daka mata saida ta razana ayayin da yake mikewa tsaye “Yace bazaki fadamin gaskiya ba?

Kuka ne ya kufce mata tace Toh ba tafiyarta tayi ba..toh ni mezan mata
Ai itace tay tafiyarta..

Kallon ta ya dingayi After sum min ya fizgota tsaye yace “Kizo nan..
janta yayi suka kama hanyar dakinsa..Pls ayi hakuri da typing errors na dare ma zai danja lokaci but i wll surely update biiznilla
Na kudine 300₦ via 0152983148 mohd sule surayya GTB ur evidence 08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: #SURAYYAHMSFR37

Desperate13:not a sister but wife!

Is not free contact please 08060712446 to subscribe.

Suna isa dakin ya sake mata hannu rusunawa tay har kasa kanta na kallon na kasan tiles din dakin,kirjinta sai bugu yake yana fat fat dan bata taɓa daura ma wani sharri ko makirci arayuwanta kamar yadda tay ma najaha ayau ba,saida ta aikata abun snn ya soma damun zuciyarta tafara jin tsoro da mummunan faduwar gaba.

tsayuwa taheer yay akanta fuskan sa a matukar dore yace ki fadamin fadar me kukeyi dazu awaje?kiyimin bayani and be fast abt it.

langwabar da wuya wasime tay cikin sanyin murya,tace ni? nifa banyi fada da kowa ba.

“Yace ohh karya zakimin,ke ni sa’arki ne?

Hade ranta tay cikin kukkuni tace nifa ba abunda nayi..kawai tafyarta tay, yaya ni wani fada zanyi da najaha kuma..

…a zafafe ya hargitso kanta kamar zai mareta
Yace “wull you stop lying to me,kifada min gaskiya nace Meyafaru tskaninku snn kiyi gaggawar sanar da ni akan meyada kikace mata ta tafi gidan su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button