FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hmmm kawai yace snn ya miƙe tsaye adan daddafe sabida jikinshi dayake masa ciwo sosai
yace “Mariam u have a serious problem with ur self…Amma ni bazan ce miki komi ba..am going inside inkin gama masifar saiki sameni a ciki..Yana gama fadin hakan ya tafi ya barta zaune cikin sauke huci da jin haushi.

Har wajajen karfe 12 da rabi bata motsa ba,jira take taga saukowar wasime tay mata tas tas dan yanzu goben É—anta kawai take duba,inda taga kominshi ya soma
Tafiya daidai din nan kwanan nan zai kudance Maima zaiyi da wata kwaila?inba dan darajar miji da amanar dake tsakaninsu wallhy da yanzu ne kam bazata amince taheer ya aure village girl kuma yar ƙarama ba.kyanta aynzu da rayuwarsa zai canja din nan ace ya samu wayayya educated girl ya aura..saidai mai faruwa yariga ya faru.

Har karfe daya saura bata bar wajen sai can dataji shirun yay yawa snn tay miƙewarta ta shiga cikin partdinta.

Daga shigarta ko wani minti biyu baiyi ba saiga taheer ya sauko cikin tafiyar sa a hankli kamar wanda baison aji motsin sa a gida.

Guntun wando mai dan tsayi ya saka da wata rigar sanyi hoodie ya kifa hularta a kansa hannun sa dauke da ledan ice cream din bai tsaya ko inaba sai dakin wasime.

Ahankli ya turo kofar snn ya shigo ciki ganin ta a rigingine ta takure kanta waje guda da towel ajikinta alaman daga wanka tafito ko shafa mai batay ba bacci ya mata daukar bazata.

Rufe kofar yay snn ya shigo ciki ya zauna daf da ita yanata kallon small figurenta tana baccinta peacefully da alaman ta gaji yau sosai.

Yana shirin gyara mata kwanciyarta ta razana ta farka a tsorace.acikin gigin baci ta tashi zaune tana mutsuka ido.

Yana kallonta yace hey
Kinwani shanyani ashe baccinki kikeyi..

Cikin langwabr da wuya tanakan goge idonta tace
Yayaa ni ma bansan nay bacci ba…kyabe bakinsa yay Yace its ok,dauko lotion mu shafa sai ayi baccin toh…babu musu taje ta dauko.
Its not freee 08060712446
7/25/22, 19:20 – Kawata: 52#

Ɓari jikin taheer yakeyi ayayin da yake riƙe gam gam da gawan mahaifinsa a hannu yana kallon pale fuskansa mai dauƙe da murmushi haryanzu,lumshe idanunsa yay abzata jin duniyar ta dauƙe masa gaba daya ya dawo tamkar bayajin sautin komi.

Acikin sanyin yanayin jiki da bazai iya fassarawa ba ya sauke gawan mahaifinsa akan gadon
Wani irin faduwar gaba ne yake kaikawo atare dashi, jiri ne ya so ya kwashe shi wanda harya kusa sanadiyar fadowarsa kasa wasimé tay saurin riƙo hannunshi tanata kuka mai ban tausayi wanda kallonta dayay ne ma yasakashi dawowa cikin hayyaacinshi cikin gaggawa.

Tsayuwar cak prof tay yanayinta kamar bata numfashi sabida wani azaban shock din daya cakkke zuciyarta,sai tanaji kamar ba’a duniyar nan take ba,mummunan mafarki takeyi,jin kukan anono ne yaso ya dawo da ita tun tuni Anono ta durkushe awajen hannunta ta dore aka tana kuka mai tsanani tana cewa “hikenan duk sun tafi sun barni a duniya”..cikin kuka mai razani taje ta rungumi gawar danta qasimu tana cewa “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta cikin tsanani tashin hankali.

zamewa prof tayi akasa rigijib ta kwalla wata razananniyar qara mai sauti da tasa gabaki daya gidan ya amsa da sautinta,ji tay kamar ta haukace dan shock din yay mata yawa a jikinta da zucyarta haryana taÉ“a kwakwala,tana ihu ta zube kasa warwas tana kuka mai tsuma da birgima akasa kamar karamar yarinya,da sauri taheer ya saki hannun wasimé ya durkusa gabanta ya rikota gam jikinsa na rawa tamkar mazariÂ
muryansa na rawa sosai hawaye na diddiga a idanunsgi yace “mumy wat r u doing?kururuwa fa kike yi akan gawan baba…So kike a É—an É—ana masa azaba sanadiyarki?dada rungumeta yy gam shima yana kuka mai sanyi da sigar lallashi yace mumy pls get hold of urself Addua yake bukata ba kukan mu ,abba is gone lokacinshi yay bamu da yadda muka iya..Allah ya jiÆ™anshi yasa ya koma a sa’a…Allah ya bamu kyakkawan karshe irintashi..

Kuka prof takeyi sosai kamar ranta zai fita yabar gangar jikinta ta mike tsaye arude ta soma tafiya cikin tsananin tashin hankli da niyyar zata je kan gawar mijinta amma tsabar gigicewa hanyar toilet ta nufa.

Cikin sauri taheer ya biyota da hanzari ya fixgota da karfi ya mannata akan faffadan kirjinsa, kankameta yay sosai ajikinsa duk yabi ya rude ya gigice sai rawa jikinsu yakey atare.

Da kyar ta dawo hayyacin ta tana tambayarsa cikin kuka shin dagske ne qasim ya mutu yabarta?
Bai iya amsawa ba ya sunkuyar dakanshi can kasa,snn ta juya ahankli ta isa wajen gawanshin tanata kallon innono data kankame hannunshi acikin wata tsumammiyar yanayin bakin ciki irinta uwa tana mai zubda hawayen ta masu tsananin rauni da zafi, wasime ne a manne a agefen ta itama tana kuka ta jingina da jikinta yanayinta a tsorace.

Durkushewa kan giwarta tay tanata kallon fuskar shi hawaye masu tsananin rauni suna kufce mata bakomi take tunawa face nasihohin daya rinƙa mata kwana biyun nan dayadda shakuwarsu da soyayyarsu ta dada yin
nisa acikin lokaci kalilin

A sukawane ta fashe da kuka aranta tana cewa “mijina ashe tafiya zakayi kabarni?,..innalilh
Wa inna ilaihi rajiun mijina bazan iya rayuwa batare dakai ba..dan Allah ka tashi…juyawa tay ta kalli anono tace Ano kimasa magana ko zaiji ki ya tashi,nasan kwana biyun nan na bashi ciwon kai hala bazaiji tausayi na ya tashi ba…ke ki masa magana inada bukatar mijina ya tashi..bazan iya rayuwa babushi ba.

Cikin tsananin jin tausayin ta anono ta soma cewa Kiyi hkri mariyamu qasimu sa’i yayi…cikin kuka tace ma anono “a’ah kedai ki gwada cema sa ya tashi,zai tashi..nasan zai tashi mijina bazai mutu fa ya barni ba..taheer ne ya matso kusa ya rikota suka mike tsaye Jin ta fara zaucewa tana shirin ficewa ahayyacinta.

Da kyar ya iya danne zuciyarshi yajanye ta daga dakin mai gabaki daya yayo da ita waje.

Ahnkli anono ta zare jikinta ana wasime ta isa gareshi tana kallon fusknsa,bargon dake jikinshi ta jawo tana masa addu’oi harta gama rufeshi da shi snn suma suka fito waje tare da wasime,anan suka samu prof shimfide akan kujera a inda taheer ya barta,jiki a sanyaye du kansu sukayi zaune awajen kowa da kalar jimaminsa.

A cikin kankanin lokaci labarin mutuwar sa ya baza anguwa,dumbin mutanen da suka sanshi da wanda ma basu sanshi ba,wasu ma labarinshi kawai sukeji agari na yadda yake da halin gaskiya da gujewa haramun,shikansa taheer baiyi tsammanin ganin taron mutane masu yawa awajen jana’izar mahaifinsa har haka ba.
Haka kawai dumbin mutane sukaji mutuwar sa acikin ransu kusan kowa saida yaji tausayi duk dama dayawansu basusan yana jinya ba.

Amma wasu kalilan sun sani,snn ciki harda ma wanda suke son ganin bayansa wanda dasu aka hade baki aka cutardashi har abun ya kaiga rasa rayuwarsa.

Bayan Ankaishi makwancinsa taheer baisamu zama ba yana ta amsar ta’aziya daga wajen mutanen dake zuwa masa daga nisan waje.

Hakama matan anguwa da few relatives din prof da na innono duka sun hallara an cikke cikin gidan ana musu ta’aziya.

Zazzabi ne ya dinga luguiguita jikin taher,dan tun daga kan bayan sallahn jumu’a sai bai gane kanshi ba,haka yy ta fama yanayi yana dauriya sabida mutane ga kuma mahaifyrshi datake cikin wani irin yanayi na gushewar hankli haryanzu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button