FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Na kudine chat 08060712446

Jin shiru bai amsata ba tay wani rau rau da Idanunta a mugun tsorace, daf kwayar idanuntan sun hargitsa zasu tsilalo da ruwan hawaye kenan taheer ya bude lumsashun idanun sa da suka cikke da tsumayinta ya kalleta, Suna haɗe kwayar idanunsu waje daya wasime ta sauƙe kanta game da ajiye wani nannauyar ajiyar zuciya..

Zamowa tay daga kan kirjinsa ta dan harÉ—e fuskanta kadan tanamai sunkuyar da kanta kasa

murmushi taheer yay kafin ya dago sama tare da ita tana rungume ajikinshi bai sake ta va, ganin dagaske ne ta razanan yasaka ya kara jawo hannunta ta dada fadowa kan kirjinshi ya rungumeta da sigar lallashi yana dan jijjiga ta a hankli yana cewa afuwan afuwan am so sorry i scared u…

Takune fuskanta tay game da turo mishi Bakinta gaba gaba tana mai sauke masa wasu sakaltaccen pouts masu razani…

Samab kugunta ya shafa ta zabura game da jin wani yarrr ajikinta,cikin dage mata girarsa sama ya dube ta yace “wai bakison in mutu miki ne kike wani bata rai?

Langwabar masa wuya tay,snn ta jingina kanta akan kirjinshi tay lamo cikin wani shagwabben murya mai sanyi, tace bakaine saika na wani rufe ido kamar ka mutu ba…nifa bana son ka mutu ka barni. Ai ..Ai..zanyita kuka.
Hakama ranan anono tay tafyarta ta kyaleni,bilti ma ta gudu ta barni wallhy kai kam ka mutu saina bika.. .

Fashewa da dariyar yadda tay maganan cike da yarinta da shagwaba taheer yay, ya dade baiy dariya mai dan tsayi kamar na yanzu ba..

kumatunta yaja painlessly yace Au da gaske kike zaki bini lahiran wai? Shiru tay kanta na kallon kan kirjnshi ahankli ta gyada mishi kai tana sakar masa wasu sakaltattun pouts Muryanta mai shaÆ™e da shagwaba tace “eh,ka tafi ka gani wallh nikam saina bika.

Yar Dariya ya kara yi cikin taÉ“e baki yace lallai ma yarinyar nan amma badai kibini kabari na ba,bakijin tsoro ko…hmm by the time walakiri ya capke ki ai zaki masa bayanin abunda ya kawoki

Idonta ta lumshe tana dada shigewa jikinshi
Cikin turo baki ahnkli tace “yo ai hikenan,basai nace masa kaina biyo ba..gintse dariyarsa yay “yace ni wa?me zakice masa, wajen wa kenan kikazo tell me uhmm?..ya fada yana dago habarta sama don su hada ido, gani yay haryanzu idanun nata a kulle suke gam gam ya dan kyabe baki.

a cikin rawan murya ta cuna baki tana cewa
“Ai..ai..aifa…kai miji na ne,sai kawai ince masa ai mijina ne ya mutu shine nima nabiyoshi .

Kasa controling dariyar sa yay ya kara fashewa da dariya mai dan kara yana dada rungumeta ajikinshi yana cewa..”oh my good god”cute babe, so u cant leave witout me? Cikin jin matsancin kunyarsa idonta na kumshen ta gyada mishi kanta da alaman eh..,yana murmushi sosai ya matso ya dora mata hadadden kiss asaman goshinta muryansa mai dadi da taushi ya saka,yana shafa lallausar fuskarta yace”karki damu i cant live witout u too kina mutuwa zan biki!..
Yabi jikinta da wani iri romantic looks yana hasasho kalan cute babies din da za’ay making anan da kalar nitsuwa da jin dadin da zai kwasa ajikinta,cikin salon zolaya yay gyaran murya yace ammmmm
amma dai bayanzu za’ay mutuwar nan bako?

Dariya ta danyi, snn ta bude idonta tana mai sake masa wani irin fitinanniyar kallon soyayya mai aika sako har can cikib kwakwalwa a hnli cikin sanyin murya tace toh ai kaine kafara..

Ya lumshe idonsa akanta ya kuma budewa yace “toh ai kece kika kusa kasheni da wancan abun..Tace wani abu kenan,bai amsa ba gefen kuncinta ya duba snn ya sauke mata nashi kiss din mezafi wanda yay kusan zautar da ita, Rufe idanunta tay cikin sauri ta matse su da tafukan hannunta bata kara sanin inda mind din yake ba saiji tayi an dagata sama cak an rungumeta ahaka har suka shigo cikin gidan tare.

Bai direta a ko ina ba sai dakinshi akan gadonsa data kimtsa mishi yay bala’in kyau ya ajiyeta ahankli kamar yar jinjira,daga tsaye ya tsaya cikin nitsuwa yana kallon lumshashun idanunta yana sauke boyayyun ajiyar zuciya

Rangwafowa yay snn ya dora mata kyakkwan kiss a saman goshinta snn ya kyaleta Yahau rage kayan jikinshi ya shiga bathrum domin yin wanka.

Harsaida taji rufewar kofar bathrum dinsa snn ta bude idanunta kirjinta na bugu cikin saukar da wasu sanssanyar numfashi..

Kofar bathrum din ta kalla kadan snn ta sauko kasa cikin sanÉ—a tay waje ta koma dakinta
Dukansu basu sauko kasa ba har saida aka kira magrib wasime ta gabatar da sallanta ta fito tana duba abincin tagama ashe bai taɓa ba,tana daga kanta ta gansa acan yana kkrin turo kofa jikinshi sanye da kananan kaya dadai lokacin ya dawo kenan daga masallaci

Tana tsaye agaban dinning din kanta na kallon kasa har ya iso gareta fuskan shi dauke da sassanyar murmushi cheek dinta yadan ja snn yace “mrs taheer yay ne?

Ji takeyi kamar zata sume dayace mata haka

Tsabagen kunyarshi datakeji aranta dakyar ta iya dagowa suka hade idanunsu waje guda ..

ACikin ladabi da nuna girmama ta masa barka da yammaci”snn ta dan saci kallon kan dinning din tace “yaya yau Bazaka ci abinci na bane?..hannunta ya jawo izuwa gareshi game da dora fuskarshi agefen wuyarta snn yace “i wll
Eat definately..so nake sai nayi ishai so that baza a cika min cikina in kasa tashi ba,kinsan yau fa hannu na yana ciwo amma kece zaki ban abincin ko?

Cikin sauri ta kalle hannun nasa Da shirmen yarintarta duk ta dauka da gaske yakeyi yaji ciwon duk da bata gani ba amma sosai taji tausayinshi,cikin jin tausayinshin aranta tace
“Meya same ka?Yay murmushi ya shafa gefen fuskarta yace mata Babu komi sai munxo cin abincin zan fadamiki Ajiyar zuciya tay kamar da gaske tace okay

After 30 mins lokacin harya sauya kayan jikinshi izuwa jallabiya ya koma masallaci domin gabatar da sallan ishai

8pm dot ya dawo gidan riƙe da wasu madaidatan ledojin shoping a hannunsa an rubuta queen haileys delicasies nd suya..

Yana ajewa tunkan ta karaso wajen ta somajin wani daddan qamshin gasashen kaza na tashi
Dayan ledar kuma bata san ko menene aciki ba.

Kallonta yay daga can yace kizauna anan ina zuwa..yana fadin haka ya wuce sama dakinshi atakaice tabishi da sassanyar kallo har ya bace ma ganinta

Wajen ledan ta nufa ta zauna snn ta bude ciki taga gasashen kaza ne da wani abu kamar balangu a kumshe acikin jarida,kyabe bakinta tay ta rufe snn ta jawo dayan
Taga water cress ne da turlips da stater na mixed jollof of fruits sai katoton goran skimmed milk mai bala’in sanyi…

Rufewa tay kirif snn ta koma ta zauna tana kallon tv can saigashi ya sauƙo jikinshi na fidda wani irin qamshi mai dadi dagashi thick black colour body hug vest da gajeren wando fari.

Gabaki daya fatar jikinshi
Yay wani freshhh acikin
Rigar dake fatar jikinshi yana da balain haske sosai.

Satar kallonshi ta dingayi haryazo ya tsaya akanta
Hannunsa ya mika mata baice mata uffan ba tana miƙa masa nata hannun ya jawota sama sukayi waje suna tafiyarsu ta masoya yana rungume da ita agefen shi.

Gaban motarsa suka tsaya ya saketa ya bude gidan baya ya tattaro jakar laptop dinsa da few stuffs da ya manta dazu acikin motar ta tayashi rike wasu suka koma cikin gida,amsar kayan yay duka a hannunta yace mata ta sauko da abinci kasa ta kawosu tsakiyar falon anan zasuci ba akan dinning ba.

Yana wucewa dakinsa da kayan wasime ta juya tahau tattaro kayan dake saman dinning din duka ta sauko da su kasa ta jerasu kusa da inda suke yawan zama in zasuci abinci tare .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button