FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani white plastic chair wasime ta hango ata bakin gate inda malam musa yafiye zama a da chan dayake musu aiki,daukowa tayi ta aje shi a daidai gindin bishiyar quava kwalli daya dake tsakar gidan a kusa da bakin famfo,nan tayi Zamanta a wajen wani iska mai sanyin dadi na ratsata tanajin dadi, cikin nitsuwa da kwakalo makanta kwanciyar hankli ta jingina bayanta ahankli ajikin kujerar tay shiru for a moment of peace of mind batare da ta sako tunanin kowa da komi acikin ranta ba.

Sai can dataji nitsuwa ya shigeta sosai snn ta soma kawo tunanin anono da kawayenta na can kauyensu da irin zaman da sukayi mai dadi,da kalar rayuwrsu da sukeyi adacan mai cike da yarinta da kwanciyar hankli game da saka annashuwa,sosai idanuwanta ya tara ruwa at same time wani sassanyar murmushi na wanzuwa akan kyakkwan fuskanta.

Ajiyar zuciya ta sauke tana ta tunanin ko hala Allah zai sake hadasu wata rana suga juna,aranta tana matukar sha’awan yuwar hakan
,innono kam ta riga tasan halinta da son yawo halama harse ta kara girma ta haihu Kafin tace zata zo dubata,daga kafarta tay cikin jin takaicin hakan aranta
,dan bazata iya tantance yawan kewarta datakeji acikin zuciyarta ba,kuma a duk sanda ta tuno da hakan sai taji wani irin ciwo da radadi acikin zuciyarta,ganin kamar zciyarta zai zurfafa acikin tunanin yasata ta yankeshi tare da miÆ™ewa tsaye cikin saibin jiki ta koma cikn gida, dakin ta ta nifa straight aftr like 10mins sai gata ta dawo dauke da littafan islamiyarta guda biyu a hannu daya qur’ani ne izu talatin daya kuma hadithi ne.

Zama tayi ta bude hifzul hadith dinta mai adadin hadisai yan kanana guda dari(100,)nan take ta naÉ—e kafafuwanta game da jingina bayanta ajikin chair din snn tayi relaxing da littafin nata a hannu tafara karantawa a nitse.

tun daga hadith number 1 tafara hartakai 100 inta biya su daddaya da littafi tayi fassaran shi, sai ta rufe littafin ta karance shi da ka.

Haka ta dingayi harsaida aka kira sallahn azahar nan ne ta tashi takoma cikin gida,alwala tayi snn tayi sallah tana zaune awajen datayi sallan ta bude qur’ani fara bitan surorin da tafi iyawa after some minutes aka kawo wutar nepa ko ina ya dau haske

kalmasa karatun tayi sann ta wuce falo ta kunna tv tadanyi kallo kadan tanayi bacci na satar debanta gyangyadi ta dingayi a wajen kafin nan bacci mai nauyi ya kwasheta mai gaba daya
Awajen ta kishingiÉ—a ta dinga debar baccin ta.

Ba ita da farkawa ba sai can wajajen karfe biyar saura, a kasalance ta tashi ta zauna kasala duk ya bi jikinta tanajin ilahirin jikinta a muce,yatsina fusknta tayi tashiga mutsuka idanuwanta cikinta na wani kugi yana kuka saboda yunwar dayakeso yaci karfinta tanajin kamar taci babu.

Ko tunanin yin sallahn asr batayi ba sabida yunwar,karshe kitchen ta nufa ta bude fridge sai yanzu ta lura da fresh fruits da danyen nama da fresh eggs da su gwaganayen canned foods da aka jejjera ciki.,kyabe bakinta tayi dan bata ma san sanda aka kawosu ba dan ko lura dasu batayi ba sai yanzu,gwalin five alive dinta kawai ta saka hannu ta jawo ta zuba dayawa a glass cup ta zauna tana sha har saida tadanji dama dama.

Kallon wajen girkin ta dingayi dan bata iya kunna gas ba,gashi tana matukar bukatan dumama abincinta dan babu abunda yake saurin tada mata zuciya kamar abinci mai sanyi.

Tsoron kunna gas din ya sakata barin wajen ta nufi dakinta ta dauro alwala ta gabatar da sallan asr lokacin ana neman biyar da rabi na yanma,dada mikewa tay awajen a kasa ta kwanta a rigingine tana juye juye duk yunwa yabi ya isheta,can dataji ta kasa daurewa kawai tay zuciya ta mike tsaye,jiri jiri ta dingaji kanta na neman mata ciwo,kuma duk tasan bazai wuce yunwar bane yake sakata jin haka, a sadade ta sauko kasa ta nufi hanyar kitchen din direct tsugunawa tayi agaban drawer ta bude drawer tsakiya ahankli ata bench din kasarshi ta dauko dan karamin tukunyar non stick da murfinshi Ta wuce dashi gaban sink
daurayewa tay da ruwa abakin sink din, snn ta jawo park din brown jollof spaghtin ta zuba aciki ta cakuda da miyarsa na busashen kifin snn ta zuba masa ruwa dan kadan daidai wanda zai isheta dumamawa…

kirjinta ne ya dinga bugu ayayin data doso kan gas din,koda ta iso saida taci kusan minti goma tana tsaye ciki jin shakkar tabawa duk tsoro da fargaba ya dabaibayeta sai zazzare idanunta takeyi kamar wanda taci kudin aika,dan runtse idanunta tayi hannuwan ta na rawa rawa dan bilti tasha gaya mata cewa gas nayin bomb ya kona mutane,wani diffff tayi da nunfashin ta tare da kankame jikinta ta rike wajen dataga an rubata on,a nitse cikin kulawa sosai ta murda wajen da kyau saiga nan wuta ya kawo, Wani tukikin ajiyar zuciya ne ya kufce mata sann tay saurin dauko tukunyar game da dorashi akan gas din,nan ta koma gefe can ta tsaya tana sauraran sa har saida ya soma kauri kaurin kona.acikin sauri ta jawo towel ta sauke abincin kasa sai kuma ta rasa yadda akeyi aka kashe,dabur dabur ta dingayi tana zagaye cikin tunani gaba ki daya ta mance inda tayi ta murda dazu ya kawo wuta bare ta gwada yin reversing ya dauke,ga wuta naci bal bal danko iya rageshi ya dawo low bata iyayi ba, Da kyar cikin karfin hali ta sake kai hannunta wajen snn ta murda shi left da dan karfi sai taga wutan ya dauke cak
,ajiyar zuciya ne ya kufce mata for the second time ta tsuguna agaban tukunyar a nitse ta bude tahau gaurayawa.

Abincin bai wani dumu ba konewa kawai yay dake bal bala masa wuta kawai tayi..haka ta juyeshi a plate ta nemi waje ta zauna ta cinyeshi tass harsanda taji ta koshi dam.

Tattara wajen tay ta aje
Dirty dish din akan sink
Snn ta sha ruwa mai sanyi tay waje..

dakita ta nufa ta zauna calmly tajikin window tare da dan lafewa tana kallon baƙin haddarin dake neman ya mamaye sararin samaniya,anan ta zauna tanata kallon sama har aka kira sallan magrib snn ta mike ta gabatar lokacin ne taji alaman taher ya dawo dagajin karar bude gate ta waje.Yana kammala parking motarsa ya kulle koina dan yasan ba kara fita waje zaiyi ba,agajiye yake tafiya bai tsaya koina ba sai dakin datake
Ya tura door din ahankli acan ya hangeta tana sallah snn ya juya ya tafi.

Bayan nan sau daya ya kara zagowa yazo dan ya dubata,still yazo ya samu lokacin tana kan gabatar da sallahn ishai.. motsin shi kawai taji abayanta yana tsaye ya kafeta da mayun idanunshi yana obseving dinta,saida yafi minti biyu a tsaye yana kallonta kafin nan taji yaja mata kofarta yay waje,tanayin sallama ta juyo a hanzarce ta dinga bin kofar da wani irin sassanyar kallo.

Dakinshi ya nufa duk ya gaji,acikin yanayin kasala ya kwanta akan gadonshi yana shan mamakin yadda yaga ta tsaftace wajen yay kyau kamar wata babba,a mind dinsa he neva expected her to know how to do anything at this age,she is just 13 probably goin to 14 yasha ganin yan 20yrs ma da basu iya yin aikin komi ba. Da wannan tunanin aranshi ya dinga
Juye juye yana mirginawa ,wasime kuwa wanka kawai ta fada bayan ta idar da sallanta
Tana kammala wankan ta fito tahau shafa lotion dinta a dukkan ilahirin jikinta tana bin koina a nitse tana shafawa ahnkli kamar wanda bata da jini ajiki,dadaddan qamshin manta na palmers coco butter mai kyau da saka taushin fatar jiki tuni ya mamaye ta,daga nan bata kara shafa komi ba ta wuce wardrob dinta tahau bincika kayan bacci wani madaidicin nity ta zaro blue colour mai zanen mickey mouse ata gaban ta zura ajikinta nan da nan ta dale kan gadonta ta kwanta a rigingine tanajin wani sanyi sanyi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button