FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

,haka tay ta yawon bin gidajen abokai da dangi bayan kwana suma sai su koreta,ta zaga koro koro da cikin najaha tana neman taimako, hatta wajen mazajen datake harka dasu ta jejje amma kowa ce mata yake baiji ba baigani ba ciki banashi bane,gashi ita kanta maman najaha bata san uban da yay mata cikin ba,da kyar da wuya ta samu matsuguni a jojjogane harta haifeta snn suka dawo da zama a nan kaduna.

tun xamansu a anguwan su taheer babu wani mai taimakonsu sabida kusan kowa a anguwar ya san harkan da uwar takeyi kuma dashi suke surviving ita da yarta..
da wann harkan ta yi hayan gida da shago snn kuma take biyama najaha kudin makarnta.

Tun Najaha tana shekaru goma kasancewrta zololowa mai saurin girma gata da dan hasken fata, hakan yasa mamanta ta soma dora burirrika masu yawa da tsauri akanta,a ganinta najaha ce zata girma ta auri mai kudi kowani mutum wanda zai fiddasu a talauci da kunyar idon mutane.

Gashi tana matukar son ta samar ma yarta kima da asali saidai bata damu kota wani hali hakan zai samu ba.

Shiyasa a kullum yaumin take bibiyar labarin rayuwar mutane dantaji me suke dashi na kudi kuma wani irin Æ™ima familynsu suke dashi a idanun jama’a.

Duk wanda taga akwai ci ata wajensa toh ko ta halin kaka ne saita san inda zatayi ta cusa yarta najaha awajen wai koda za’a kulata ta samu mijin aure da wurwuwri asirinsu ya rufu..hakan yasha faruwa Amma haryau bataci nasara ba.

Daman gidansu taheer din ne kawai bata san sanda ta ina zata shige musu ba, sai caraf gashi kuwa ansako wasime a makarantansu najaha har kuma suka dawo kawayen juna..ita ta dinga zuga najaha akan lallai saitayi kawance da wasimé.

Mahaifyar najaha tana da kyakkawan labarin Rayuwar taheer da irin kudin da ake harsashen zaiyi anan gaba.

Sabida a kofufin professions likitocin sojoji bakaramin kudi suke debawa ba,mostly idan ka fita a babban likita monthly salarynka kawai yana iya kawai near to a million per month,dadin karawa da akace mata taheer is studyng the most sought out course wato neuro_sugeon bacin yana da ajiyayyen kwalinsa na karatum general surgery da yayi abaya.

Ko ayanxu ma dayake karatu tasan anan biyanshi kudi da suka kusa kai dubu dari biyu,ahakan ma banda allowances da wasu yan abubuwan da suke shigowa..

Being a neurosugeon and with a general surgery badge a nigeria tamkar wani babban matakala ce nayin arxiki,cos a iya neurosugry field FG xasuna biyanshi kimanin nine hundred thousands naira harda dan dauri per 3weeks..bare ma shi akasar waje zaije ya karkare Allah kadai yasan yawan kudin da zasuna biyanshi acan.

Gaba daya mahaifyar najaha ta zauce akan batun shgar da najaha rayuwar taheer,kamar dai inda hausawa suke cewa da zafi zafi ake bugan dutsi,shiyasa jiyan ta borance ma yarta datake son ta karaya sabida tausayin kawarta wasime.

Yau da duka da masifa ta
Tasheta abacci gameda jan kunnenta akan lallai saita kara bibiyar rayuwar wasime ta hanyar da zai kaisu ga yin nasara akan taheer.

Karasowa ciki najaha take yi a zciyarta tana tuno da dukkan abubuwan da mahaifiyar ta ta ce mata intazo yau tayi..tana kallon taheer dik saitaji ta karaya sabida dagsken gaske zuciyarta ya fara kamuwa da kaunarshi ta gaskiya,saitake ganin koda batabi salon makircii don mahaifiyar ta ba hala zata iyayi kodan kanta,saidai wani hanzari ba gudu ba. gabaki daya anguwarsun babu wanda yasan da cewa taheer already yay auren sa yanada mata.

Dadin karawa da basu san wacece wasime ba, ata dalilin makarantan daya sakata ne kawai yasaka mutane suka san da akwai karamar yarinya a gida…gaba ki daya anguwar sunai mata kallon karamar kanwarsa ce sabida mahaifinshi bakin fatane mamansa ne fara sol sosai sabida ita kabilar ebira ce.

So taheer ya dauko kamannin babansa ne amma kalar fatar sa gabaki daya na mahaifiyar sa ce

Duba da shekarun wasime babu wanda zaiyi saurin kawo tunanin cewa ita matar aure ce,snn ba a kaduna aka dora auren ba ma bare iyayensa su gayyace makwafta da abokan arziki koda za’a tayasu murna..yau auren su kusan shekara biyu kenan amma a anguwar ba wanda yaji wani labari akai.

Su asalin iyayen nasa ma bamasu lokacin shiga rayuwar mutane ba ne,sabida tsabgar rayuwa. ko gidansu ma sun kasa samun zama aciki bare ace sun zauna ana wani doguwar hira dasu awani waje.

Taheer na tsaye awajen dayake bai motsa ba.

yana lura da yanayin yadda najaha ta marairace fiska harta iso daf dashi snn ta tsaya, cikin sanyin murya tace.
“Salamu alaikum”.

Fuska ba yabo ba fallasa taher ya amsata ataikace
Tare da maida hannuwan sa cikin aljihu yana mata wani irin kastancaccen kallo.

shirin tsugunawa take
Zata gaishe sa sai caraf ga motsin fitowar wasimé daga kitchen

Wani tsalle zciyar najaha yay sabida tsoro acikin sauri ta haÉ—iye gaisuwar snn ta miÆ™e tsaye ta tsaya tana kame kame muryanta a sarkaÆ™e tace yaya na…

Bata ƙarasa ba taga wasime ta fito fuskarta a mugun daure ta zo ta lafe a gefensa suka tsaya suna kallonta atare..

Shiru ne ya ratsa wajen najaya tanata kallon su for a minute snn taheer yay cutting silence din yace”ke kuma wakika zo nema?gaban najaha take ya faÉ—i…zata matso kusa dashi wasime ta watsa mata wani wargajajjen kallon dayasaka taji gabanta yay mummunan fadi hade da jan tsaki mai tsayi da kauri,kamo hannunta taheer yay yana murzawa ahankli yanamai mata alaman da kartace komi awajen har saiya umarceta..

Atake atake kan najaha ya kulle ganinsu tare a wannan yanayin da bata gane ba sam,muryanta na matuÆ™ar rawa ta wani durkusa agabansa kamar munafuka cikin marraice murya tace yaya Uhm Dama…dama…yaya nazo ne in bawa wasime hakuri, saitay shiru ganin kamar hanklinsa bai kanta sai kan wasime.
Cikin dauriya ta matse tace yaya kasan me? jiya ana ruwan nan wasime tazo gidanmu tana ta fushi tana laka min sharrin waina yaudareta akanka shine nace toh baridai nazo gidan yau nabata hakuri nasan hala yanzu zuciyarta yay sanyi
Kuma zata fahimceni

Taheer yana kallonta wani iri Yace..”haka ko?toh gata nan ai saiki bata hakurin..

Kara bugawa zcyar najaha yay dan bataso yace hakan ba,taso ne
Yay ma wasime tsawa ya tuhumeta meyasa taje wajen

tsaye ta miÆ™e daga wajen ta dubi wasimé cikin kinibibi da kutungwila cikin matse murya tace kawata dan Allah kiyi hakri ki fahimceni ni duk abunda kikamin ban damu ba dan nide tsakani da Allah nake zaune da ke kuma har in mutu bazan iya cutar dake ba…

Tsaki wasime taja batace komi ba.

Taheer ya hade rai yace “to kingama?

Shiru tay tanadan mamakin yanayin yadda yake mata magana yau.

Muryan shine ya sake dawowa da ita tanajinshi ya dubi tsabar idanunta yace mata ok girl u have to leave right now ai tajiki…

Da wani irin makrtaccen salo ta kwabe fuskarta kamar na wanda xatay masa kuka tace haba yaya na Korata kakeyi yau a gidan?..

wasime ta fauce hannunta anashi dan gabaki daya iskancin najaha ya isheta wani matsiyacin kallo tabita da shi sn tace “ke mahaukaciya abce miki baisan ke munafuka bace?azzaluma makaryace to nariga na fada masa abunda jiya kika gayamin nacewa ke munaface,kuma kina son shi kuma sabida ya soki kike zuwa gidan nan kike daukar abincina kibashi danki hadamin munafurci awajen sa ke kuma yasoki…in karya nake miki saiki rantse agaban sa yaji…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button