FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Within some minutes saigashi ya dawo yana zuwa ya nemi waje akasa akan chineese capert ya zauna gameda nannade kafafunsa idanunshi nakanta yace
“Bismillah serve us quickly am farmished ke sharifiyace bakijin yunwa ko?..murmushi tay ta girgiza kai batace mai uffan ba ta mika hannu zata bude cooler abincin
Ji tay ya riko hannun yana ce mata “ya baki bude ledojin ba aima ke na kawo su yakamata kidan bude nima sai intayaki ci..tabishi da sassanyar kallo tace ok barito na bude,tadan kwace hannunta tafara budewa bata hankara ba harya dau serving spoon ya jawo cooler gabansa zai bude,satar kallonshi takeyi da gefen idon ta batace mishi uffan ba
Ganin woww reaction din daya bayar da face dinshi at the sight of abincin,”tanata satar kallon sa da wayo taga kamar ya bita da kallon irin anya ke kika dafa wannan abincin kuwa?daga baya kuma sai taga yana wani kayataccen murmushi .

A nitse ya zuba musu irish poridge din snn ya bude flask din ya dan leka kadan turirin gamshin kunan madarar ce ta wani doki kofar hancin shi a bazata ya kyabe bakin sa yace Masha Allah…kiris ya rage tay dariya sai taji kamar ya dan tsakure ta, juyowa tay suka hade ido taga harya langwabr mata da fuskaa yace baki sauri fa ko intayaki ne?..cikin sanyin murya tace no yanzu zan gama
Kusan komi dake wajen saida yasa ta budeshi snn suka soma cin abincin daki daki yana bata abaki tana bashi har suka cika ckinsu sukayi dam suka kasa tashi awajen,sai can arnd 9:30pm suka tashi sukahau tattara wajen zasu kai empty dishes din kitchen,sauran poridge din ne kawai yace abarshi yana tunanin anjima zai kara tabawa.

Bayan nan komi sun tattara sun kai kitchen yana tsaye daga bayanta yana kallonta ta tattara sauran kaza da basu cinye ba tayi storing dinshi a fridge da shi da sauran mixed jollof fruits wanda basu taɓa ba da sauran skimmed milk din,roba biyu ya siyo ba fruits amma guda daya kawai suka sha saita aje musu sauran,kominta tayi shi ne acikin tattali.

Sun dade a falo suna kallon wani american film na marvel kafin wasime ta xame jikinra anashi tay hanyar dakinta ta kwanta tayi bacci,shima yau dakinsan ya je ya malala akan babban gadonsa ya kwanta in a comfortble mood just to reliev his stress na exams da aiki da gabobin jikinshi ya kwasa.

Washe gari haka ya tashi da tunanin iyayensa acikin ransa,duk fishin sa dasu hakan baiya hanasa jin kewarsu a zicyrsa he misses them alots har kasan ranshi yana muradin sake kasancewa tare dasu yana son kallon fiskokinsu.

Haryaje yay sallah ya dawo bai dena kawo tunanin iyayensa aransa ba, da tunaninsu aranshi har wani baccin ya sake daukarsa bai farka ba sai wajen 10am na safiya.

Jikinshi a watsake ya tashi dan bai saba samun bacci mai yawa har zuwa wannan lokcin ba Gashi yau baida wani exams tension akanshi bare wani aiki sabida anbasa hutun sati biyu dan ya dan huta ma jikinshi kafin result dinsu ya fito.

Wanka ya fada,ya dade yana wankan cikin tunanin yadda zai soma kashe kudadensa wanda suka shigo jiya dan harynzu bai taɓa ko sisi aciki ba.

Bayan ya fito a wankan ya shafe jikinshi da manshi mai qamshi ya saka normal kaya na shan iska snn yay sauko

Samu yay ko ina fes harta farka,yay murmushi jin dadi ganin harta tsaftace wajen ta dafa paten macroni tay sauce dan kadan da sauran kazar da jiya ya rage basuci ba sai dan mango juice dinta shima datay duka ta aje mishi akan dinning ta koma dakinta tay dan bacci abunta.

Dakinta ya nufa ya taso ta suka sauƙo kasa tare,a nitse suka zauna cin abincin anan yake tambayar ta Mesa yau batay tea ba danya lura kamar tana mugun son yin tea, anan ne yake fahimtar cewa kusan komi na abincin gidan ya dan ja baya.

Bayan rage kudin cefane da najaha takeyi ita kanta wasime haryanxu bata san da cewa najaha takan kwashe abubuwan amfaninsu da abinci tana boyewa acikin hijabinta tanakaiwa har gidansu ba.

Taheer baice komi ba har saida suka kammala cin abincinsu tare acikin notsuwa ,yau ma hakan ya tayata tattara empty dishes din suka kai kitchen ta tsaya wanke plates din yana tayata daurayewa dan baison tana taɓa ruwa sosai.

Sunayi suna yar hirarsu ta soyaya,da na abubuwan da zasu je su sissiya a kasuwa,bayan sun gama wasime ta tsaftace kitchen din suka dawo falo suka zauna tana masa lissafin abubuwan shikuma yana rubutawa harda abunda take bukata na komawa makaranta.

Bayan sallah azhar haka suka shirya sukayi kyau shi yasaka sky blue half jumfa da hula ita kuma ta sako riga da zani na A class cote d’voire brown colour mai shegen kyau da black veil,hannunta sakale da nashi suka fice a gidan sukaje babban kasuwar garin wasime yau murna kamar zai zaucar da itaz dan tunda tazo kaduna yau shekarunta biyu kenan amma banda makaranta asibiti da gidan su najaha data jejje bata taÉ“a zuwa ko ina ba,taheer yana ta kallon ta tanata zumudin ta har suka sisissiya abubuwan da basuda shi na store din abincin gida da duk wani abun bukata su madara kifin Gwangani, babu abunda basu siya ba etc

Bayan nan haka yakaita
Super market wajen siyan kayan sawa danta zabi wasu kayayyakib datake so shima ba a barsa abaya ba hakan ya zage ya zaba mata wasu kayan ganin ita kadan kadan ma take daukawa
Kuma Bata da wani wayon sanin abu mai quality.

Shiyay aikin debo mata atamfofi masu kyau da tsada guda takwas da golden nd black abayas kala kala har guda biyar ,ya siya mata normal abaya gowns da jallabiyar mata, grey colour, maroon da purple sai da bakake guda biyu.

Hakama veils da takalma da jakan gayu dana zuwa makarntarta, she was soo excited nd happy dan jakar school dinta ma har kashi biyu ya siya da wani hadadden gucci side back mai sandals dinshi da kuma hunch schl back na kamfanin nikki minaj kominta Masu kyau ne da tsada,hakama school cover shoes,toms,flat shoes,veridiles canvas booth da rigunan sanyi masu hula da marasa hula hadaddu.

Bayan angama na nan ya siya mata inner wears kala kala harda daan breziya lol,yabi ya mata shoping din kayan kwalliya da su turarrukan jiki da body mist sprays da sures na hammata.
duk dama bata taÉ“a gaya masa tana bukatar su ba,shibaima san man datake shafawa ba wann karon saiya zabar mata set na man jergens mai tattare da komi da kominshi ajikin pack dinsa.da skin/hands moisturizers da wani green alovera vaseline lotion..ya siya mata dan kunne da abun wuya masu tsada guda biyu yan dadai kuma guda uku da irin pack din jweries na kwali din nan mai dauke da small small earings da zobuna dats very cute for girls of her age Da barbie boxes na agogo wanda yawanci daga madina ake impoting dinsu acikin box daya zakaga one major wach head sai differnt colours na hannun agogo kala kala a manne,toh duk sanda kake sha’awar sawa sai ka zabi kalar da kake so kasaka ajikin head din saika daura a hannunka
Agogunan very cute nd slim daidai na yan yara mata irinta.

Sabida tsaftace gashin kanta haka ya sissiya mata set na kayan gyaran gashi daga kan natreatment,boosters,conditioners,steamers,har zuwa shampoos nd combs Kai harda hair dryerta.

Wasime duk ta kasa iya rufe bakinta dan ji take kamar a wani duniya na daban take yau din nan ba ma asalin duniyr data sani ba.

Gabaki daya Duk ta rude fuskanta yakasa boye farincikin datake jiki ganin yawan abubuwan da yake siya mata
Wanda bata taɓayin mafarkin samun irinsu arayuwarta ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button