FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

bai iya daukr waya ba yabita kanta da sauri ya fixgota jikinshi ya rungumeta tsam yana mai rada mata subhanalla subhannallah acikin kunnenta ,rawa rawa jikinta yakeyi,haryan zu bata fasa fidda numfashinta ba..wani lamo tay akan kirjnshi yana famar shafa mata gadon bayanta ahankli cikin yanayin lallashi da son ya kwantar mata da hankli.

Iduwanta a lumshe ta lafe tana tuno duk abunda ya faru da ita yau acikon kwakwalwnta,

wani Shiru wajen ya dauka dashi,a tunanin shi nitsuwa ne yake son shigo mata yasatayi shiru, baisan sake sake kawai ta bige dayi acikin zuciyarta na yadda zata gudu ta rabu dashi ba

Motsawa ta shigayi dan ya saketa amma sai bai saketan ba,wani irin jan zuciyarta tay takaishi can sama snn ta mike zauna ta kwaco kanta ajikinshi da bala’in karfi…

Da mamaki ya kalleta ,sai yaga ta tashi tsaye a hargitse,shima tashin yay da niyyar kamo hannunta yana tabata ta callara masa wani gigitacccen ihu tamkar wacce taga dodo

A fusace cikin kuka ta shiga cewa ni wallh
Kadena taÉ“a ni..nika kyaleni…bana so..
Kabarni…ya matso kusa ta ja baya a borance tana kuka sosai..nakasshiyar ajiyar zuciya ya sauÆ™e
Snn ya rage sautin muryanshi ya sako dashi kasa kasa cikin lallashi
“yace …hey Please calm down..baki ganin bakida lpya ne?da sigar lallami da karya wuya ya dada cewa ‘infa bakiyi shiru kin dena kuka ba ciwon ki zai kara dawowa, kiyi hakuri mana kiyi shiru kinji.

Wasime data kankame jikinta ko jinshi ma batay ba..a fizge ta kama hanya cikin sauri zata barmishi dakin yay sauri ya jawota ta fada ajikinshi ya kankameta kallonta yakei hanklinsa tashe da sanyin murya yace “Ina zakije kuma,kizauna anan tare dani mana uhm?..bata amsashi ba ta kara fashe masa da wani matsanancin kuka acikin
Kukan ta tamke idanunta tashiga cewa “o’o o’o ni wa’lhy bazan zauna dakai ba..koma ina zanje ai babu ruwanka..leave me alone for godsake ni tafiyata kawai nakeso inyi..kkrin jawo hanklinta yake izuwa gareshi yaga ta dauke kanta da sauri tana mimmikewa ajikinshi tana naushin shi da iya karfin da Allah ya bata.

tun kafin ya hankara ya kamata subul ta kufce a hannunsa ta fado kasa snn tay saurin tashi tsaye da mugun gudu ta fice a dakin ta wuce nata dakin direct tasaka key taciki tanata kuka..
Sanda tay kukan ta ya ishe ta snn ta share hawayen da suka bata mata fuskanta

Jikinta a matukar sanyaye ta tashi tabar wajen bakin kofar tana tafiyarya a hankli harta karaso ciki ta tsaya a tsakiyar dakin,Daga ita sai yar towel din daya daura mata akirji.

zubewa tay a gaban wardrob dinta haryanzu bata dena gunjin kuka sai wani jan zuciyarta sama sama,sa hannu tay ta bude wardrob din snn tahau fidda dukkan wani kayanta dake cikin wajen

Jin ana buga kofa yasa kara rikicewa dan ko ba ‘a fada mata ba tasan taheer ne ya biyota yana son ya shigo ciki.

Muryashi ta tsinkayo kamar bashi ba,yana magiya yana cewa wasimé kiyi hkri please open d door nd listen..kinga baki da lpya
Dont hurt ursrlf anymore.
Wasime…wasimé..wasimé..

Tanaji yana kiran sunanta da zance kusan yafi kowa iya pronoucing dinsa with difrent disturbing tune,kuma tanajinshi amma haka tay shiru batako kulashi ba…

Kukanta ta cigaba dayi a hakli,jim kadan jin wajen ya dauka da shiru kwakwalwanta ya soma bata hala yaje dauko extra keys ne.

Batasan ta inda karfi ya zo mata, jin kanta kawai a tsaye hartay wani wuf ta tashi tana neman abunda zata kwashe kayanta aciki,da bataga komi nan kusa ba daya daga cikin hijabanta ta shimfida akasa ta tuttula kayayyakinta akai tayi sauri ta doresu,daga nan ko tsayawa saka wani kaya ko takalmi batayi ba,rungume kullin kayanta tma hammatarta ta bude kofar dakin tana dan lekewa waje,ganin ba kowa yasa ta fito tafara tafiyarta cikin sauri sauri da kayanta a damke a hammatarta kamar wacce zatayi gudun hijra
Ta koma kauyensu..

Harta sauƙo falo tana sauri gabanta nakan faduwa danji take kamar ba zata isaga bakin kofar tay waje ba.

Saidai ko tsakiyar falon bata isa ba taji takun mutum a bayanta kirjinta na bugu ta juyo a farge dashi, zata rafka a guje kenan ya daka tsalle ya jawo hannunta da karfi ya kamota ta dawo baya gameda fadowa ajikinshi

muryansa harna rawa yace “oh my god what r u tryn to do?kuka ta kara fashe masa dashi jin harya matsota ajikinshi batada wani ikonyin wani motsi…

Ta rufe idonta gam cikin fada tana cewa
“Kabanni kabanni..nikam kasake ni..

Hanklinsa a tashe ya juyo ta tana fuskantar sa da mamaki da tsoro a fusknsa yace”wasime Ina zaki da kaya?..
Wher did u think ure going..innalillhi wa inna ilahi rajiun..ohhh guduwa wai zakiyi?

Idanunta a rufe gam gam tana kicin kicin tace babu ruwanka da inda zanje
Nidai Kasakeni inyi tafiyata..bana kara zama anan..xaman ya ishe tafiyata zanyi ainasan hanyar tashar garinmu.

Yana kallonta baisan sanda ya sauke ajiyar zuciya mai rikitarwa ba,hannun ta yaja cikin basarwa yana cewa

‘Toh ya isa haka Come here lets get back inside..yana riÆ™e hannun nata ta soma jajjja da baya tana turjewa…”kizo muje nace miki ni ba zan kyaleki kije ko ina ba.
Bakida hankli ne a cikin wannan yanayin ne zaki cemin zakiyi tafiyarki akan me?are u out of ur senses..ke zonan muje ciki ki kwanta kiyi bacci..cant y see ur body neeed rest,yanakan maganansa tana kkrin zare hannunshi akan nata da iya karfin da Allah ya bata

..ganin bazata iya ja dashi ba,karfinsu baizo daya ba ta gantsara wa hannunsa wata cizo snn ta tsala ihu cikin salo tana wayyyo Allah na hannu na hannu na namin zafi ka karyamin hannu na,maza ya sake mata hannun ya dauka ko da gaske takeyi ashe makircinta ne sabida kawai ta kufce masa ta gudu.

Yana kuwa saketa saiji yay ihun yay tsit da mugun gudu ta doshi bakin kofa harjikinta na bari tana saka hannu zata bude ya capkota tare da kwace kayan data riko din ya watsar dasu acan.

A ragwabe ta zube kasa ta kara fashe mishi da matsanancin kuka binta kasan yay hanklin sa a mtukar tashe yace “i said im sorry”..pls kiyi hkri karki tafi…
Dagota yay da karfi suna daga durkushe suna kallon juna..”idanuwanta a lumshe cikin kuka tace
Wallah tallahi saina rabu dakai..tafiyana garinmu zanyi babu fashi..
kazauna anan din kai kadanka inka ga dama ka je ka dauko najaha aizata zo ta tayaka zama..

Ya haderai ya matso daf
Kamar baiji metace ba,matsowa yy tamkar zai shige jikinta yace wai maiyasa bakijin magana ne ehhhh?banace miki kiyi hakri ba..hakuri fa nake baki.

cikin fushi ta bude idanunta ta kalle shi snn tace anji amma sai nima ka kyaleni natafi garinmu ai ba dole bane inzauna anan din…nidai gaskiya tafiyata kawai zanyi.

tsaye ta mike ya biyota tsayen ranshi na neman baci da rikicin nata

Yace”pls dont start kizo mukoma ciki kawai..
waike bakijin hakuri ne?

shiru tay bata ko kulasa ba ta doshi inda ya wurgan mata da kullin kayanta data kumshe su acikin hijabi tsugunawa tayi ta rarumosu ta kara rungumesu a hammarta tana juyowa zata tafi taci karo dash agabanta
,kallon shi tay fuskanta a dore,gani tay yay banga banga ya toshe hanyar da zatabi ta wuce din yana ta kallonta..
dauke kanta tay ta mayar da kallonta gefe cikin shesshekar kuka

ahankli sai ta kuma juyo
Jin ya sako wata sassanyar murya mai tsananin karya zuciya yana cewa “im sorry..kallon idanunshi tay ganin tsumayin nadama karara sun bayyano.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button