FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dul jikin Wasime yay sanyi tana ta kallon bakin kofar, shirin bin bayanta take taji an wani fincikota baya har saida ta fado kan kirjinshi tare da kankame sa, lumshe idanuwanta tay atake jin inda qamshin jikin nashi yake mamayarta,yana shiga har cikin fadar zuciyarta “yace “wher did u think ure going Nabaki izinin fita ne? Kicin kicin tahauyi cikin shirin kwaco kanta daga rikon dayay mata tana dan turo masa baki Kamar zatayi kuka tace
“Yaya najaha zata tafi fa…shine zaka sakata taji haushi na?nikam ka sakeni zanje ne in dubata kartay fushi ta koma gidan su ta barni nikadai anan. tsaki yaja toh ta tafi mana…dama akwai abunda yake cinyeki ne inkika zauna anan din ke kadai?,she doesnt even look like ur friend ata ina wai kika samota?,dago kai tay ta kallesa da mamakin jin haka tace”yaya najaha ce fa.

shafa gefen fuskarta yay abazata yana duban kyakkwan fuskanta lumshashen idanunta data kulle yake kalla
Ahankli cikin kasalalliyar murya yace”uhum and so what?..ke baki ganin yadda tazo ne, ahakane zakuyi kawancen tana saka matsatsen kaya?…

Zatay magana ya zaro mata idonshi ya hade rai..”ke indai haka zatana zuwa nan gida toh kice mata ta hakura kawai dake kuma karta kara zuwa min gida.

shiru tay Batace mishi
Uffan ba ta sauke ajiyar zuciya tana kallon kasa jikinta a sanyaye..

Saketa yy ya koma can gefe snn ya jawo jakar laptop dinsa ya rataya a kafadar sa yaga haryan zu tana tsaye bata motsa daga inda take ba.

Kyabe bakinsa yay yanamai cusa hannun shi aa aljihu yace
‘Did u need anything else?Aikin iya tea ko zakiyi kisha kayanki..

A dan sakalce ta juyo ta kalleshi cikin turmusa fuska batace mai uffan ba ya basar da ita ya taho kamar zai wuceta ya fita,sauri tay wajen cafko hannun sa ta rike cikin nata,dan sanyin murya mai kashe jiki tace “yaa nayi maka tea
Ko zaka sha dan kadan?..

Xuciyarshi cike da tsumayin dadin laushin hannunta ya dubeta yace
“Tun yaushe kikayi?nifa nakoshi yana furta hakan yaga ta wani harde ranta tanata kallon kasa
..boyayyar murmushi ya saki yana kyabe bakinsa a boye…toh amma tunda kince dan kadan ne ai ba matsala jeki kawo..Cikin hanzari ta sake hannun shi taje ta dauko tea din,waje ya samu ya zauna akan kujera ta taho tare da rusunawa agaban sa ta mika masa tea din ya amsa tanata kallon sa har yakai bakinsa ya sha kadan snn ya sauÆ™e ya miko mata sauran.

Girarsa na sama a dage yace “Satisfied?..bata san ma tay masa murmushi mai sanyi ba..a sace shima ya mayar mata irin murmushin nata.

Yana mikewa yace
Comon Im going to be late baki fadamin abunda zan siyamiki ba

Kanta na Æ™asa tanajin kewarsa aranta tay da fuskarta kamar na wanda za ta fashe masa da kuka cikin sanyin murya tace “zan dafa dakaina ,Bakinshi ya taÉ“e “are u sure?to ko dan kawarki ta tafi shine bazaki karbi nawa ba?…kanta na kasa ahankli tace mishi a’a…ajiyar zuciya ya sauÆ™e toh ki dauko mayafinki saina ajeki agidansu inta shirya canza wancan kayan nata saita zo miki wani sati cos we are going out this week..

Da mamaki ta kalle sa saidai bata wani fahimci meyake nufi akan fitarsun dayace ba…tace toh nagode yaya..ya sabi jakar sa a hannu ya wuce gaba yana cewa kiyi sauri ki sameni a waje.

Yana ficewa tabi bayan sa ta wuce kitchen ta aje shauran tea din hijab dinta ta dauko ta taho ta same sa a waje harya tada mota cikin hanzari ta isa wajen ta bude ta shiga ta zauna suka fice acikin agidan .
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR29.
Desperate 13:am envious

Acikin nitsuwa yake tukasu har suka iso kofar gidansu najaha ya kashe motar ya juyo yana kallon fuskan ta babu yabo babu fallasa yanajin kamar ma yau ya tafi da ita makaranta yace did remeber ur promises?..shiru tay tana tuno dukkan wasu abubuwan dayace tanayi da wanda yace mata baiya so,numfashin ta taja sama abazata jin ya miko hannun sa gently yana dada gyara mata zaman hijabinta ata fuskanta ta cigabaa da kallon shi snn ta gyada mai kai a hankli…

cikin sauÆ™e ajiyar zuciya gameda bawa zucyarsa hakri yace “toh jeki” saina dawo.

Harta juya zata sauka kamar wanda ta tuna wani abu ta dan sace kallonshi “Yaa zaka dan dawo da wuri yau?atke ya harde rai”Yace akan me?..Bakinta ta turo mai gaba sigar shagwaba “tace babu”..saita rasa mema yakaita yin masa wann tambayar dan tsaki yaja Baice mata uffan ba har sanda ta sauka snn ya ciro wallet dinsa ya zari dubu daya aciki yabata…yace gashi kirike wannan saina dawo,.
Ta amsa cikin ladabai, saidai ciki ciki tace masa
Tagode din bai kara kallonta ba yaja motarsa tsaye tayi awajen har sanda ya tafi snn ta sauke ajiyar zuciya ta nufi cikin gidan su najaha.

Lokacin najaha harta gama cin kukan ta tagaji
Tayi lumui da fuska kamar marainiya Jin sallamar wasimé ya balain bata mamaki dan batay zato har taheer zai
Barta ta kara zuwa gidan su ba. “Sosai tay nadaman saka dressing dinta na dazu..taji haushi matuka da hakan mata asarar damarta nayau.

Gashi zuciyarta ya bala’in kamuwa tare da yin zurfi akan lamarin taher,tun dazu babu abunda takeyi sai maimaita hoton kyakkwan fuskarsa sa a kwakwalnta musamman ma yadda taganshi yau so neat nd fresh wayyo Allah tanaji kamar ma shidin nata ne.

Tun dawowarta ta samu gidan shiru da alaman mahaifyarta tay wani wajen itama,bata iyayin komi ba da tulin bakin cikin abunda taheer ya mata ta tumu akasa ta zauna a falonsu tana famar sake sake..

Jin muryan wasime yasata ta firgita ta tashi tsaye tare da leÆ™a waje cikin gaggawa…

Suna hade ido ta wani turo baki tanamai hade rai…wasime ta karaso cikin sanyin jiki tana cewa”Haba kawata yanzu fushi kikayi?

Har falon ta bita suka tsaya suna kallon junan su.. tsaki najaha taja
“to akan me bazanyi fushi ba kina kallo yayanki ya walakntani
..aida saiyace inje in zanca kaya meye nashi na nuna kamar ma bai taba ganina ba..ni gaskiya bai kyautamin ba raina ya baci..

Murmushi wasime ta saki ganin yadda najahar ta wani dage akan maganan tana wani korafi dagaske Har kaman zatayi kuka

Neman waje wasime tay ta zauna abunta tare da dora kafa daya akan daya,saida ta gama Æ™are mata kallo snn taja numfashi “Yo kema meye naki na sako wayannan matsatsun kayan Ke kanki kinsan basu dace dake ba …da kyar fa kike motsa cinyoyinki..gashi kinje kinsa anmin fada
…gaskiya najaha in har zakina zuwa gidanmu ko?to ki nitsu kawai ki kama kanki kiyi shigar mutunci Ba shigar yan iska ba.Haba kinbi kin matse kanki sai kace wata yar kan layi?

Najaha kamar zata tashi sama take kallon wasime,a hargitse ta rike baki tanacewa”Buuuura ubeee…wasime wani kike cewa yar iska yar kan layi?

Cikin sauri Wasime ta rike bakinta tana rau rau da idanunta tace “kai najaha “kamar” fa nace!..

Najaha ta riko kugunta tana karkada kafa cikin jin haushi game da watsa mata wasu mugayen harara.

Tsaki wasime taja
Toh shikenan kiyi hakuri
Ha’a ke bada amiki magana saiki maidashi fada?

Idonta najaha kamar zai fado kasa tace Bazanyi hakurin ba.Wallah dagangan kika fadamin haka wasime,..waike sarkin wayo ko?hmm
..ina dan jiya nace miki tinkiya shine kika riÆ™eni aranki saikin rama…to ai shikenan tunda kin rama yanzu dai hanklinki ya kwanta mtsssss.
Tana kammala jan tsakin ta nemi waje ta zauna ta harde rai..

Shareta wasime tay bata ko kulata ba,sai can dataga kowa acikinsu ya tsime cikin fushi yaja yay shiru,tasan najaha sarai ta tsani tayi magana a shareta,infact she is an attention seeker normally inta na waje ko tay wani abu tana so taga duk an kula da ita duk a bata muhimmanci..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button