FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hakan kuwa akayi,within 25minute har sojoji sunzo sun dauke malam musa daga shi sai yar wandonsa yana ihu yana cewa ya tuba amma haka suka tafi dashi.

Tun bayan ficewarsu taheer bai iya motsawa daga wajen ba,jikin shi tayi sanyi,dukkan wani karfin gwiwarsa yarasa shi,hakama dukkan gabobin jikinshi atake suka ragwabe suka sace mai karfin jikin shi mai gaba daya,da kyar ya sauko kasa izuwa falo..,waje ya samu akan kujera ya zauna a falon snn ya jingina bayanshi da kujerar tare da lumshe idanuwan sa da sukayi jaa yana fidda numfashin sa da kyar.

“He just cant believe dat bilti is gone out of thy lives,ji yake kamar bazai iya rayuwa babu ita a gidan ba,bai damu dan kansa ba, anma ya damu wa zuciyarsa datake jin bilti a matsayin uwa kuma wata muhimmayar jigo ga rayuwarsa.

…yasan wat malam musa did to her was terrifyng nd uncalled for..taÉ“a mutunci da kimar mace kamar bilti abune mafi muni da raunanawa da mutum zai iya aikatawa,wanda yawanci mata basa cika mancewa dashi tacikin sauÆ™i .

Bare ma mace kamar bilti wanda take da shekarun girma,da kuma mummunan taɓo azcyarta mai rauni wanda take kkrin binnewa all her life domin ta samu farincikin yin rayuwarta cikin sauki..

Daga content din letter da ta rubuta He can deeply imagine her pain and agitations..yasan ta raunana sosai kuma zaiyi wuya ta sakejin sha’awar kasancewa da su.

Aynxu Zai iya mata uzuri dan tace ta bar gidan amma bazai taɓa iya mata uzurinta na yanke hukuncn datayi na ficewa a rayuwarsa ba.

Wasime dake can dakinsa duk ta kasa zama sai kai kawo takeyi da tarin tambayoyi masu saka tashin hankli da fargaba,ko wani motsi tajiyo saita dubi bakin kofa taga ko shine amma haryanzu shiru bai shigo ba,gashi ta balain matsuwa haka kawai take son tasan halinda biltinta takeciki,tana son tasan ina biltinta take.

Zama tayi dirshan abakin gadonsa ta zuba uban tagumi,after few minutes ta mike tsaye kawai ta doshi bakin kofa duk da fargaba ayanayinta amma bashi ya hanata ficewa ba..

Cikin sanda take tafiyar ta tana lekowa kasa ahankli,daga can sama ta hangeshi taga yana kkrin daddana wayar sa.
Hanklinsa duka nakan wayar.

Tsayawa tayi ta dan mannu da jikin bango tana lura da shi,tashin hankli ta dingaji ganin yanayinsa kamar ba shiba duk fuskansa ya sukurkuce da rauni yanayin sa ya bayyana tashin hankli da damuwa.

Cikin gaggawa taga ya dora wayar a kunnen sa
Haka ya dingayi har sau goma batare da yay wata magana ba,hakan yana nufin kirar wani yakeyi amma ba a daga kirar,taga ya zaro wani karamin waya a aljhun rigarsa ya hau kwafar wata lamba.

Sau biyu yana buga ba a dagawa,saican snn aka dauka,tsaye taga ya mike cikin gaggawa yana cewa”ina wuni kawu taheer ne..Daga ta dayan bangaren Aka amsa masa babu yabo babu fallasa..mutumin yace
“Taheer kana lpya?
Dan Shiru yy yana shafa goshinsa cikib sauke ajiyar zuciya,muryan sa kamar mai shirin yin kuka yace “kawu bilti nake nema..ko tazo ta wajenka?intana wajen dan Allah kaban itq zamuyi magana..yadda yy maganan a raunane yasa mutumin yin shiru na yan dakiku..”muryansa na rawa sosai “ya kara cewa kawu dan Allah intana wajen kabata wayar ina son inyi magana da ita…pls pls abeg u sir,dan Allah ka taimaka min inyi magana da ita yanzu..yana furta hakan hawaye suka cikko kwayar idanunsa ya rikesu tam yanajin wani bala’in karyewan zuciya.

Mutumin baice mishi uffan ba Jikinshi a matikar sanyaye ya juya ya kalle bilti datake zaune agefensa tana kan sauke hawaye,dan tun dataga kirar taher awayarta ta somajin rauni da kunci na dabaibayeta..she is already missing him soo much…tana ta tunanin yadda zaiji aransa in bai ganta ba.

Mutumin yy yai da ita ta amshi wayar amma haka taki sam,mayar da wayan kunnen sa yay cikin sauke ajiyar zuciya yace
“Taheer kayi magana ai tana jinka,yana fadin haka ya saka mata wayar a handsfree

…Raunataciyar ajiyar zuciya taheer ya sauke game da furzan da nannauyar numfashi
…muryan sa harna rarrabewa a hankli yace
“bilti”…kuka mai tsuma ne ya kufce mata jin yanayin muryansa tasan yana cikin tsananin tashin hankli da damuwa
Cos she neva left his side for once all this while,ita ce mishi uwa da uwa itace kuma abokiyar shawaransa,sam bai saba zama babu ita a kusa dashi ba, saiyau datakejin bazata iya zama a gidan ba.

A hnkli wasime ta shiga takowa kasa izuwa falon jin ya ambace sunan bilti..Ata bayanshi ta ja tsaya bai lura da ita ba tay tsam itama tanajiyo kukan da biltin takeyi…

Jin sautin kukanta yasaka shi Yafara magana a sasarfe kamar mai shirin yin mata kuka…yace bilti kiyi hakuri mana,kiyi hakuri karki barni wa nake dashi inbake ba,Dan Allah kiyi hkri ki dawo gida namiki alkwari ko numfashi zai kare a duniyan nan saina bi miki hakkinki,bazan bar musa yakarajin dadin rayuwarsa ba…i truly understand ur pain but u dont have to leave us like dat Dan Allah kiy hkri kidawo..namiki alkwari hakan bazai kara faruwa ba.

Da kyar ta iya share hawayenta cikin sautin kuka da jin tausayin halin data jefashi aciki tace
“Taheer kayi hkri,bazan iya magana dakai yanzu ba…kayi hkuri ka kula da kanka…ka kula da wasimé,cikin runtse ido da tuna irin maganganun da malam musa ya dinga fada mata akan cewa tana bukatar namijin da zai cita, tace ..sai anjima taheer..tana fadin hakan ta katse wayar a kunnensa,wani lumshe idanunsa yy yanajin kamar zuciyarsa aka cannawa wuta mai tsananin zafi….
300₦ NE JOIN THE READING GROUP VIA 0152983148
MOHD SULE SURAYA.GTB 08060712446.
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR24
Changed perception

Taheer Yana zaune awajen Zuciyar sa a matukar karye,ahnkli ya zamer da wayan daga kunnensa snn ya kalli screen din wayar yana mai kawar da wayan izuwa gefenshi,Lumshe idanun sa yay yanajin wani irin zafi taciki.

Raunatacun hawayen sa da suka makale ne suka sauko bisa kuncin sa ahankli,cikin sauke nannauyar numfashi ya saka hannayensa yahau gogesu cikin gaggawa tare da sulalewa kasa ya zauna cikin matukar sacewar gangan jiki.

A daskare wasime take kallonshi ganin kamar ma ko motsin ta baiji ata bayansa ba,juyawa tayi cikin sanda zata bar wajen zcyarta cike da rudanin ganin sa a hakan,gani tayi ya miƙe kafafunsa akasa gameda lafar da kanshi jikin cushion idanuwansa a lumshe sosai.Tana daga kafarta zata zille awajen tajiyo sautin muryansa a kasale yana cewa
“…zo nan!Dawowa tayi tana tafiyarta a hnkli tamkar maijin tsoron wani abu har ta karaso ta taho kusa dashi,,a daf kusa da inda ya zauna itama ta zauna kanta na kallon Æ™asa…”shiru yay baice mata uffan ba itama batace mishi ba…
Har can saida yaji dan dama dama acikin ranshi sann ya bude lumsashun idanunshi da sukayi sharrr da nauyin dauriya yanamai sauke su akanta,gani yay har iyanzu Bata dago kanta ba tanata kallon kasa ji take gabanta na mummunan faduwa nauyin idanunshi akanta ne yake kkrin dagula mata lissafi da dasa mata mummunan fargaba.Dan karamin ajiyar zcyar ya sauke ya kalli agogon dake saman falon snn ya dubeta a takaice muryansa a dan sanyaye yace “zan fita.Me kike sha’awar ci.

Dagowa tayi suka hade ido sauri tayi wajen kawar da nata idon cikin gaggawa, haka kawai tausayin shi yafara ratsa mata zciya,kanta na kasa cikin sanyin murya dake rawa rawa Tace “yaa bilti fa?..tun da nazo naga banganta ba..yaa ko kasan inda taje?
…shiru yay kamar baiji me tace ba ya dauke kansa kadan yana firzan iska ta bakin shi..daga nan dukan su sukayi shiru for a moments kafin nan ya mike tsaye yana kallonta yace”Kinji tambayar da namiki?
…kafin ta dago kai,ya bita da dan harara wanda zaka gane kawai dauriya yakeyi bawai dan zuciyarsa tana cikin mood din yin wani dogon magana da kowa ba, yace “Look there is no one around here anymore,daga yanzu Babu mai yimiki girki,so ki gayamin abunda zakici kawai inna fita na taho miki dashi nd be fast about it inbadai da yunwa kikeso ki kwana ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button