FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani bin inyace ta zabi abu dakanta har jikinta rawa yake saita kasa tabuka komi,nan take kuma sai taji kanta ya kulle ta kasayin komi daga karshe shidin zaizo ya zaba mata na daidai gwargado..ga english wears ma ubansu,
T shirts,tops,crop tops kala kala da nice nd crzy jeans da nities,sai famar zolayarta yake da cewa kullum bomb shots din nan zatana saka mishi a gida.

Shima dai haka ya dan sissiya makansa abubuwa mostly kayane wanda zai bar kasan nan tare dasu.

Wannan zagaye zagayen
Shoping din da sukayi yau bakaramin daukar su lokaci yay ba,tun fitarsu basu dawo ba sai wajajen biyar da rabi na yamma acikin su babu wanda bai jigata ba

Taheer Yanayin wanka sai can bayan sallahn magrib yaje ya siyo musu abincin da zasu ci dan ko kadan baison ya kara bata wahalar yin wani girki.

Washe gari da sassafe bayan sallahn asubahi wasime taje ta nuna mishi godiyarta har idanunta na kawo ruwa,bakaramin jin dadi aransa yay data nuna masa tayaba da abubuwan daya siya matan ba,daga nan suka zauna suka shishhirya komi awajen zaman sa,duk abunda bata san ya ake amfani dashi ba haka ya koya mata,wasu kuma ya gaya mata amfaninsu fa yadda zatay da su.

Abubuwan komawan makarntar daya saya kusan kowanne set bibbiyune banda uniform daya siyo yadinshi da dan yawa wanda zai ishesu ayi mata dinki har kala hudu.

Duka atampopi da materials da suka siya guda sha biyu da yadin uniform dana hijabs haka yasaka ta zubasu a cikib wani katoton leda yace mata anjima kadan Zasu je gaida bilti sai su kai mata ita bayar a dindinka mata.

The house was bubbling with new new things and happines,ga sabbin kayan qamshi na gida da suka siyo.Zuwa yanzu kam babu wani abunda zaka nema ka rasashi a gidan Sann wasime ma babu wani abunda bai siya mata na amfanin kanta ba.

Inkaga yanayin shakuwar su wanda datazo musu a bazata ynzu zaka dauka tunda can sun saɓa da junansu ne.

Duk da yana sake mata fuska,yana janta ajiki sosai bashine ya sa ta somajin aranta zata rainashi ba.

A madadin hakan ma wani sabuwar kima da daraja take jin zata bashi acikin zuciyarta da kwkwalnta,jiya tagani da idonta yadda ya kashe mata kudaden sa kamar bayason su,a tunaninta duk kulawar dayake bata halacci ne wanda bazata taɓa mantawa ba kuma bai kamata ta saka masa da rainin wayo ko yarinta ba.

Son da take mishi yanzu har yafara rufe mata ido sabida kyautata mata daya farayi,gaskiyar hausawa ne da suke cewa zuciya tana son mai kyautata mata ne.

dadin karawa da yadda ya sake ranshi kamar bashi ba yana tarairayar zuciyarta da zantukan soyayya da shaukin dayafi karfin kwanyarta
,hakan yasaka takejin duk duniya babu mai kaunarta kamarsa.
Kamar yadda zuciyarta take masa soyayyar da babu adadi ayanzu.

Batajin wani wanda zai kula da rayuwarta kamar taher,duk wani yabo da girma da ke bawa saheeb aranta adacan sai taga kamar nashi ba komi bane compare to yadda taga duk abunda take so a duniya taheer ne kawai yakei mata Ko bata tambaye abu ba zai batashi,snn ya rage yawan fushi da nuna iko da mulkin nasa akanta,ya dawo mata tamkar wani uwa da yaya da uba da ƙawa, yanajin tausayinta yana nuna mata so da gata.haka zai bata shawara mai kyau snn ya hanata yin dik wani abunda zai cutar da ita.

Sosai zuciyarta ya riƙeshi da daraja, idanuwanta kuma suna kallonsa a matsayin jigo, tamkar wani bango abun jingina Uwa mai share hawaye
Uba mai yaye damuwa da miji mai ƙima da nuna kulawarsa da damuwar sa akan yar matarsa.

Ko a mafarki bata taba tsammanin samun irin wannan rayuwar ba.
Shiyasa haka kawai takejin kanta a rude

Wani Sabuwar yanayi ne ta shiga mai dadi mai tsafta dadin karawa da yadda yake kimanta ta yake bata dama dan tay expressing kanta da abunda yake cikin zuciyarta mashi,sam bai yi amfani da girma ko matsayin shi wajen kwace mata yancinta ko son nuna iko da mallaka akanta sosai ba.

Intay ba daidai ba saidai ya gyara mata ko ya nuna mata rashin jin dadin sa..ya dena mata tsawa da ihu ya dena daga hannu akanta.

Lokco guda Wasime ta susuce da lamarin soyayyar taheer acikin zuciyarta da gangan jikinta.

Aganin ta duk wano namijin daya san ya bawa matarsa daman ta acikin gidansa da rayuwar sa tamkar ya share mata hanyar kasancewa dashi ne har abada.

Dayawa wasu mazajen mu suka kashe kansu awajen matayensu ta hanyar nuna iyawa da mallaka,da iko akan komi

sai kaga namiji da matarsa a gida amma hatta kayan miya shizai tsara mata hakama yadda zatay da harkokin daya shafi kulawa dashi batare da yadan bata daman baje nata basirar ba.

Hakan Tamkar zalunci ne mai girma,ace ka aje mace a gidan ka snn kace komi kai zaka tsara mata batare da kaji opinion dinta,koda ma ace bazakay amfani da nata shawarar ba amma jin ta bakin tan yana da matukar muhimmaci da tasiri wajen nuna mata cewa ita ba baiwar gida ba ce,mace ce macen ma abokiyar zamanka

duba da kowacce mace a duniya tana son a darajara ssn a kimanta ta,mata halitta ne na Allah wanda basa son kaskanci ko a nuna musu tsatsauran ra’ayi da mallaka akan aurensu da rayuwarsu.

Karkiga anacewa namiji shine shugaba mai zurfin tunani,saike ki sake jikinki kice duk abunda yay dake a gidansa daidai ne,Hakan ma wani babban kuskurene sabida Basira da tattalin zamantakewar aure sai mata.

Komin isa da iyawar namiji qaddara kece gishirin rayuwar sa,in kika lalace kika koma baya da tunanin shine Abar bautanki,to babu shakka haka rayuwrki da na aurenku zata zamto fatak babu fasali tamkar abincin da ya rasa gishiri da maggi…..

Abun ma hakan yake awajen mata,duk dama mulki da nuna mallaka ba abu bane wanda yay yawa ata fannin mace,amma duk wacce ya fiye nuna ma namiji itace sarauniyar iyawa da bada oder aurensu da rayuwansu to babu shakka har abada bazata mori wannan mijin nata ba.

Sann duk mace mai nuna lallai sai kome ya tafi akan tsarinta batare da kulawa da opinion din mijinta ba,to qaddara tana jawo gushewar soyayyace da karewar kimanta da zubewar darajarta a zuciyar mijinta.

Yau wasime ta kasance cikin farinciki da nuna godiyarta wa Allah a fili dayasa ta same adalin namiji mai fahimtar ta ajikin wanda bata taÉ“ayin tsammanin har abada zai kulata bama bare har ya zamo mata abun tunkaho araywrta kamar hakan….
Na kudine 08069712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: SURAYYAHMS FR45..
Home coming: new life…

Na kudine 08060712446

Yau sai wajejen 10am saura suka samu suka karya sabida aikin shirye shiryen kayan da suka sissiyo jiya awajen shopping,bayan sun kammala karyawa ya tayata ta tsaftace ko ina agidan waje yay fes yana fidda qamshi mai É—aÉ—i,daga nan kowa ya nufi dakinsa domin yin wankan zuwa wajen bilti.

Tun jiya da safe taheer ya kirata,ta sanar dashi inda zasu zo su same ta.11am dadai wasimé ta fito daga wanka kirjinta daure da wani sabon orange colour towel wanda yakai mata iya rabin kan cinyarta, jikinta babu abunda yake sai zuba qamshin hadaddun sabulan wanka da tsadaddun mayukan shower gels din da jiya taheer ya sisssiyo.

Zuciyarta cike yake da farinciki da kwanciyar hankli,a nitse taja kujeran gaban madubi ta zauna snn tashiga kare ma kanta da jikinta kallo tana sauke sassanyar ajiyar zuciya,lumshe idanuwanta tay a hankli snn ta bude fuskarta mai dauke da wata malalaciyar murmushi mai karawa fuskan nata armashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button