Ganin ko ina agaban madubinta cike yake da kayan kwalliya dana shafe shafe sai ta rasa inane ma zata soma dora hannunta ta dauka.
Set din man jergens din ta bude tay amfani dasu tanami jin dadin feeling din da man yake bawa jikin nata,fresh nd moisturising babu wani qamshin chemical mai lalata fatar jiki.,man is so soft nd mild suistble for dark nd fair skin da suke son suyi maintaining kalar fatarsu.
Yau kusan mintina talatin ta dauka wajen kimtsa kanta ajikin madubi,duk yadda ya nuna mata ake amfani dasu haka itama tay,bayan ta gama ta shafa turaren hammata ta shafa body mist,sann tay light make up akan fuskarta ta saka kwalli ta shafa jambaki nude colour mai dan sheki yadda tay lining lips din bakaramin fidda kyaunta ya karayi ba.
Kominta ta gamashi within few minutes sai kuma ta rasa wani kaya zata zaba ta saka ajikinta.
Tana cikin wannan zulumin saiga taheer ya bude kofarsa ya shigo fuskar sa babu yabo ba fallasa Suna hade ido dashi taga ya mata wani mugun kyau acikin dressing din sa na kanan kaya dayay yasaka maroon colour shirt na raymond da golden brown pants kalar booth din dake kafafun shi,hannun sa sakale yake da golden colour royal oak chain wrist watch da sabuwar wayar sa ta iphone da siyo jiya a hannun sa yana latsawa.
tsaye ta miƙe tanata kallonsa tana dan murmushi can kuma sai taji sauyin yanayi marar dadi yana neman mamayarta.
Take tafarajin kishi kishi,tanajin kamar ma tafiyar yana son ya fice mata aranta,ganinshi kyakkwa kuma hadadden namiji mai aji gashi fari tas kalar da mata suke matukar bibiya da kauna
Ta dubi kanta taga fa haryanzu ita yarinyace karama wanda batama gama girma ba Gata baƙar fata ita ba farar mace bace, bata da dogon suma da kyan fitan hankli irinna indiyawa da larabawa,
atake ta somajin kamar dai yaudaran zuciyar ta kawai takeyi akansa.
Haryanzu aranta tana dan masa kallon kamar yafi karfin sa’ar aurenta dan ko ayanzu ma gani take kamar yan mata zasuyi warwason shi snn ita batajin tanada wasu makaman da zata iya karawa da su.
Tunanin datakeyi kenan sai gaba daya Mood dinta ya lalace ya dawo na damuwa da sanyin jiki.
Tunba yau bama tafarajin aranta kamar she is being intimidated kawai dai an hadata aure ne da wanda ajinsu baizo daya ba..
Isowa yay har gabanta da mamakin ganin haryanzu bata gama shiryawa ba..kallonta yake ganin sauyin a yanayi afuskan cikin kulawa ya riko hannunta ahankli Yace “cuty meyafaru?me kike jira baki saka kayaba ko abun yazo ne?fuskarta dauke da damuwa ta sunkuyar da kanta can kasa tay shiru,can kuma ta dago kan ta kallesa kirjinta na bugu tanajin bazata iya fallasa masa abunda takeji akansa acikin ranta yanzu ba..cikin langwabr da wuya ta basar da tambayan ahnkli tace lapiyata kalau fa yaa, yaya ban san kayan da zan saka bane ko zaka dan nunamin irinshi?..hararta yay yace nikuma,to shikenan ai saina tafi in barki anan in bazaki nema dakanki ba
Yana fara tafiya acikin sauri tabiyo bayanshi da shagwaba tana rokonshi da kyar dai ya dawo ya tayata zabar kaya.
Da kyar da drama mai ban dariya tukun ta amince mishi zata saka jean da top kafin ta saka abayar kimono akai.
Hakan kuwa akayi yasa ta saka wani white t shits da matsatsen blue color skiny jean wanda ya bala’in ma jikinta kyawu,snn ta dora all black kimono abaya akan kayan tayi rolling kanta da dankwalinshi looking xtremely dashing gashi ta tadan riko sabuwar jakar channel side bag dinta,hannunta sakale da tsiririn agogo na fata,ta kuma tsaya akan sandal heels ita kanta sai dataga ta canza ma kanta kamanni.
kamanninta na yau gaba daya yamata kamar banata ba,duk sai taga ta dawo wata kyakyawa kalar yar gayu.
Turaren flower bomb ya dauka ya fetsa mata kadan kadan ajikinta dan baiya bukatar tayi qamshi sosai da wasu zasuna ji daga sun rabe gefenta.
Tun a dakin ya shiga dauka musu hotona masu shegen kyau da wayar sa yana nuna mata cewa yau tay matukar yin masa kyau da haduwa,É—an abun da ya bata confidence kenan taji hanklinta ya kwanta Har ta riko hannunshi suka sauko kasa tare,tana tsaye agaban bmw dinsa ya shiga ya dauko ledojin kayan dinkinta ya bude booth dinsa ya zuzzuba su aciki.
A fannin bilti kuwa duk ta rasa yadda zatay ta gaya ma kawunta cewa su taheer zasu kawo mata ziyara yau,saida ta hada da neman alfarma da magiya ata wajen matarsa snn ya bata izinin ma a walakance.
Ya amince amma tare da Doka mai tsauri daya saka mata akan yau yakasance shine rana na karshe da zasu zo masa gida,kuma kar suzo yau su dade masa a gidan sa shibaya so,taheer is busy gushing all over his little wife ita kuma sai aukin jin kunyarsa takeyi,ajikin motarsan ma saida ya musu beutiful coupl pics kowanne tana rungume ajikinshi style style da sukayi su biyu masu shegen kyau snn ya mammata hotunan ita kadai,videon da suka yi shi wasime take ta kalla tun farawar tafiyarsu har suka iso kofar gidan su bilti bataji gajiyar kallon su atare ba…
Yau tsabar rashin kudin da bilti ta tashi dashi har bata samu damar ta sissiya musu ko ruwan sha ba,dan komi nata ya kare,gashi kawunta ya karbe sauran kudaden ta wai bazaina ciyarda ita haka kawai abanza ba snn shi bazaina jira saita dauka ta bashi ba,tunda ta bashi kudadenta sai ya zamto da kyar ma take fixgar kadan a hannun sa.
Karfe sha biyu ya gauce kadan saiga ƙirar taheer awayanta tana daukawa yace mata gasu nan sun iso,hijabinta ta saka ta fito ta bakin kofar gidansu acan kan titin layinsu ta ga motarsa.
Wasime tana hangota ta sauÆ™o a guje taho suka rungume juna,ita dai duk sanda taga bilti sai idanunta sun fidda hawaye masu rauni…bilti ta riÆ™ota sosai tana ta murmushin ganinsu atare tana cewa”ke dalla zaki É“ata kwalliyarki kinga yadda kikayi kyau kuwa shine zaki bata fuskanki da kuka,toh sai ince ma taheer ya mayar dake tunda ke sarkin kuka ne…a shagwabe ta goge hawayen fuskar nata kafin nan taheer ya iso suka gaggaisa ta wuce dasu cikin gidan ta shimfida musu tabarma akasa suka zauna taheer na can gefe wasime na zaune kusa da bilti…
duk hnklin bilti ba ajikinta yake ba dan ko ruwan da zata basu su sha bata dashi gashi bata isa ta taɓa na gidan ba ahauta da zagi ace sai tabiya itakuma sam batason su taheer su fahimce halin da take ciki.
Aganinta wann rayuwarta ce bai dace ta saka ko dayarsu acikin wani damuwa saboda matsalar rayuwarta ba..
Zuciyan bilti yana cikin kunci amma ganin su ahaka looking calm nd happy yasa taji farinciki da kwanciyar hankli acikin zuciyarta.
Duk ta damu sai tambayar su lpyarsu take famanyi,tana saka ma taheer albarka dayake kulawa da wasime dan sosai taga canjin hali da canjin tarbiya awajen wasime ga kyau dataga ta karayi.
Suna cikin hirar su basu wani jima ba sai ga kawun nata ya fito da wani irin matsiyacin kallo yabisu zai wuce taheer ya miÆ™e tsaye cikin sauri yabishi yay masa sallama ciki ciki ya amsashi ya sakai ya fita,matar san ne ma tazo ta tsaya akansu da gatse tana tambayar bilti meyasa bata kawo musu ko ruwa ba,bilti data san jin bakinta kawai take sonji tace mata bata da kudin siyowa ne,babu kunya tahau yima bilti surutu agabansu Tanacewa Maimumatu kekam gaba daya kin dawo wata munafuka shine ko na randa bazaki deba musu ki kawo musu ba neman kawai kijawa mutane anai musu kallo wani iri kamar basu san daraja bako ba…