FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsaki taja ta wuce daki tanata surutan ta babu wanda ya kulata gaba daya jikin taher sai yay sanyi..”wasime dake rike da hannunta ahankli cikin jan tsaki tace”aimu bamuce mata zamusha ruwa ba..mufa wajenki kawai mukazo tazo tana wani miki masifa.

Shafa kanta bilti tay fuskarta kamar zatay kuka tana murmushin dayafi kuka ciwo ta dan kalle taheer tace taheer kuyi hkri ban baku ko ruwa ba…baice komi ba ya mayar mata da sansayar murmushi.

Sai can da wasime ta nace zatay fitsari kafin taheer ya hau tambayar ta ko akwai masala amma haka bilti ta boye mishi komi ta nuna masa babu abunda ke tafe sai dan abunda baza’a rasa ba na sabanin yau da kullum,dan ta kauce wa maganan saita kawo masa maganan iyayensa
Ta tambayesa ko yay waya dasu?yace mata ya neme su amma duka layukansu baiya tafiya snn ya bincika ance masa basa kasarne amma baisan wani kasa sukaje ba,itama ta sanar dashi akan takan nemesu amma bata samun su,dama damuwarta duk akan rayuwar wasime ne da ake kyaleta ita daya agida.

Kwantar mata da hankli yay yace aima ya kammala jarabawrsa yana hutu snn wasime yanzu tana yin abubuwa dayawa dakanta.

Sosai tay masa nasiha kamar yadda uwa zatay ma dan cikinta akan da yay hakuri da halin rayuwa.

Snn ta nuna masa jin dadin ta game da yadda ya amshe wasime arayuwar sa..ranar yasha Albarka wajenta bana wasa ba.

Matar kawun ne ta tsare wasime aciki tana ta mita tanai mata tambayoyi banda haraarta ba abunda wasime take can dai ta dauki wani kofin roba ta deba mata ruwan randa ta bata wai taje musu dashi susha.

Duk surutayyarta wasime batace da ita uffan ba ta amshe ruwan ta fito ta samu har sun kammala tattaunawar su yanakan mata bayani akan kayayyakin dinkunan wasime da yazo dashi yana cewa koda zata taimaka takai a dinka mata su kafin a bude makarnta ranar monday,bilti tace babu komi yaje ya kawo kayan zatay iya bakin kkrinta,tashi yay ya nufi wajen motarsa ya bude driver seat ya zauna aciki basu san meyakeyi ba duk sun dauka hala amsa waya zaiyi..

Ganin ya dade aciki yasa bilti ta soma jin labarruka dayawa abakin wasime na yadda yayanta yake sonta ya kuma sissiya mata sabbin abubuwa.

Duk wani labari saida ta bata har akan rabuwar su da najaha,bilti ta dade batay dariya irinna yau ba..sosai ta fahimce cewa wasime tafara son mijinta sosai amma duk da haka babu abunda ya sanyaya mata rai yasataji dadi sosai aranta kamar yadda taheer yake kulawa da ita

As usual bayan ta kammala bada labri haka bilti ta jajjaa kunenta ta gargade ta snn ta karfafa mata gwiwa akan ta kara yin kokari wajen yin biyayya da gyara halayyarta.

Nasihar data mata nacewa kyan halin mutum ne kawai yake sa asoshi ba kyan fuska ba ya dada wayar mata da kai akan yadda take daukar kyaun taheer harta ke ganin kamar ya wuce ajinta na aure.

Suna kan magana can saiga taheer ya fito suna kallon shi ya wuce bayan booth ya debo ledojin kayan, bude ledan kayan yay a sace cusa wasu envelopes aciki snn ya kawo ya miƙawa bilti duka kayan akan in angama dinkin zata nemeshi yazo ya karba.

Tana amsar kayan yace mata toh su zasu wuce saiya sa hannunsa aljihu ya dauko wallet dinsa ya bude ya zari dubu biyar daga wallet din snn ya bata ahannunta suka bar wajen cike da kewar junansu sosai.

Kawunta dake labe ajikin bango kamar dama timing din tafiyar nasu yake tun bata motsa awajen ba yay wani wufff ya fauce duka kudaden a hannunta yana cewa ke kawo nan dama bamuda da na cefanen yau yana karba yahau kirgawa

Bilti tana kallo haka shida matarsa suka raba dubu biyar din nan a tsakaninsu ita basu bata ko sisi ba.

Da bakin cikin haka ta shiga cikin dakin ta tay takumi,sai can bayan asr da zuciyarta yay sanyi snn ta jawo ledojin kayayykin tana dubawa acan cikin wani embelished wax mai kyau ta tsince envolpes din…da mamaki ta dauko ta bude taga sabbi kal kal din kudi ne yan dubu daddaya na kimanin dubu dari biyu da small note a gefe da handwriting in taheer yana ce mata kudaden nata ne tay amfani dasu makanta for the main time snn ta kula mishi da kanta,kuma kofarsa a bude yake a duk wani lokacin datake neman taimakonsa zai taimaka.

Dayan karamin envelope din kuma dubu ashirin ne aciki kudin dinkin kayayyakin wasime.

Fashewa da kuka kawai bilti tayi ita kadanta a dakin,tayi kuka sosai harta gode ma Allah snn ta share hawayenta ta nemi can kasar gadonta inda tasan baza ataba dubawa ta boye kudin tana tunanin yadda zatayi dasu nan gaba.

Dama can tana da plan din fara saida abinci a kofar gida amma bata da wani capital din da zata fara..but tunda yanzu kudi yazo aranta tasan yadda zatayi ta soma sana’arta cikin dabara da yin wayo sosai wajen boye kudin ribarta, duk dama tasan zata sha wuya da bakaken maganganu awajen su kawu amma dai wanm din shine mata hanya daya da xata dogara dakanta ayanzu

Da wann kudin tasaka aranta cewa sai ta dage da neman nakanta koda kuwa za’a taru akanta ne da bakaken maganganu.

Bayan kwana biyu shakuwar dake tsakanin taheer da wasime ba’ace mishi komi,ana washe gari zata koma schll bilti ta Æ™ira taheer yazo amshi kayayynkinta da aka dinkasu sukayi matuÆ™ar kyau kowanne dinki da akai mata ya dace da ita sosai.

washe gari da sassafe suka tashi suka shirya komi na zuwa schl komina na jikin wasime
Sabo kal kal ne sai murna takeyi acikin ranta

Yau kam All eyes on her a makaranta mata da maza kowa na kallon kayanta da su jakanta da sabon takalmin ta,musamman ma najaha datakejin kishin ganin yadda wasime tawani canza mata tay kyau tay fresh ga kamshi,taga komin ta data saka mai tsada ne, kowa sai son shishhige mata yakeyi tana basarwa kamar wata yar masu kudi..haka tay zamanta ita kadai bata kula kowa ba, kusan har aka cinye satin bata shiga harkan kowa ba ita daya take rayuwarta a schl da islamiya..abun bakaramun cin ran najaha yakei ba.

Ana tashi a schl haka taheer zaizo ya dauƙeta suje yawonsu ya siissiya abinci da kayan kwamulashe.

Tunda tafara zuwa schl baya kyaleta tay girki a gidan inba chan dare in yafarajin sha’awar cin wani abu ba,ahakan ma baifi ayi tea ko wainar kwai ko noodles ba
Sumtimes zasu kwana waje daya sumtimes kuma kowa na dakinsa
Lokaci guda wasime ta zamto wata yar gata.
In aka bata assigment haka zai zauna suyishi tare ko ya koya mata karatun qur’ani.

Yau asabar ranan zuwa islamiya sai wajajen karfe 6 da rabi na yamma yaje ya dauko ta suka dawo gida,wasime na shiga daki ta fada gado wani lumshe ido tayi tana tunanin abinda yake faruwa gaba daya da yadda yake sauke ta makaranta ya bata kudi,da bude mata kofa,da pegs dinsu na amana, da kuma tafiyansu wajen cin abinci masu kyau da abunda ya dinga yi mata jiya a dakinshi na runguma cikin baci

lumshe ido tayi tana tuno duk wani lamarin da yake faruwa wani iri ta dinga jin kanta, gaba daya ta kasa daina tunawa,jiki a sanyaye ta mike ta cire Hijabin jikinta da kayan uniform din islamiya ta shiga wanka, nanma tafi 15mins cikin bathrum da ta cika da ruwan zafi a tube tana wankarta dashi.

sai da ta gaji dan kanta snn ta mike ta fito bayan tay alwala nan ta gabatar da sallolinta,snn ta zauna a gaban madubi ta shafa mai ta fesa turarukanta masu sanyin kanshi sannan taje closet dinta ta ciro kayan bacci,wani red short sleeping gown ne da fuskan mickey mouse dagata gabanshi ta saka ajikinta sannan ta kwanta bacci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button