
Hannunta ya kama ta miÆ™e tsaye suna fuskantar juna,muryan sa kasa kasa yace”kiyi hkri kuje tare din, zanzo na dauko ki anjima..”da sanyin murya tace “okay..”i wll miss u today…murmushi yay ya bata light hug cikin haka ta sauÆ™e masa bye kiss agefen kuncin shi shima wanda yay daidai da shigowar mahaifyar sa wajen,Tun daga can take kallon yanayin su abun nata bata mamaki harta kasa yadda da yanayin datake ganinsu aciki.
Wasime najin sautin takunta ta ja baya,shima saiya dan dauke kanshi kadan sukayi tsege tsege kamar basu yi komi ba
Dauke kanta tayi akansu itama sanda ta wuce can gaba kafn nan tace in ka gama da ita saiku fito ka sameni awaje.
Tana ficewa suka biyo bayanta,suka samu harta bude motarta ta shige ciki tana jiran wasime.
Sadaf sadaf wasime ta iso kanta na kallon kasa ta bude motar ahankli ta shiga ta zauna.
Taheer na tsaye a tsakar gidan har suka nufi gate suka tafi,ajiyar zuciya ya sauƙe snn ya koma cikin gidan domin ya dauki wasu files na processing lettersa na scholarship.
Bai wani jima ba ya fito saiji yay ana horn a bakin gate da mamaki yaje ya bude saiyaga maman sa
Ne wai harta dawo,Suna hade ido ta dan takune mai fuska ta sauka kasa tana tafiyarta cikin basar dashi,bai damu ba yahau binta a baya Yana cewa mumy wani irin rough driving kikayi haka how minutes shine Harkin sauƙeta kin dawo?
Bata amsashi ba saida ta samu wajen tsayuwa tace “ni fa bankaita ko ina ba,yan schl dinsu na gani a hanya suna takawa da kafa shine na tambayeta ko zata sauka ta bisu su karasa tare tacemin eh shine na sauketa kawai tabi zuga suka wuce.
Atake annurin dake kan fuskan sa ya yanke cak sai baice mata komi ba
Ya lura kawai is like she is looking for his trouble so take wani abu ya hadasu ta saka mai dokokin masu tsauri akan wasime,dan kwata kwata bata son yadda taga sunayi kamar wasu adults abun baiya mata dadi aranta setaga kamar wani abu kamar sex zai iya shiga tsakanin su wanda aganinta danta bai shirya zamowa baba witout fulfiling his dreams ba
Sede kuma aranta bata taɓa jin kamarshine mai laifin,duk gani take kome wasime Ne take bibiyarshi duk dama tasan yarinyar tana iya bakin kkrinta wajen kiyayewa .
Tamkr wanda yake karantar zuciyarta ya basar da maganan baice mata komi ba wanda hakan ya jawo Bataji wani dadi aranta ba.
She is already thinking of sending wasime to a boarding schl musammn in a nigeria taheer zai karasa karatunsa.
Kishin sharing din zuciyarsa datakey da wasime yasa take Haba haba Allah ya bashi sa’ar jarabawarsa dan ya tafi can kasar waje inyaso in aka barsu tare tana ganin hanklinta zaima fi kwanciya.
Gyara zaman hularsa yay yace mum zan wuce.
Ganin yanayin yadda yay maganan atakaice bada sakin fuska ba yasa tace “okay”..Allah yasa muji kyakkwan sakamako.
Yace ameen,har zai fita tabiyo bayansa tanata kallon sa…can ta kwalla masa kira tace “taheer!
Jiyowa yay ya kalleta ta taho ahankli ta rungumesa tana fadin dont i also derseve a hug from u?kajimin warayya..
Ajiyar zucya ya sauke cikin ranshi ya kyabe baki
Snn ya cirota tare da sauke mata peg a goshi
Murmushi ta sake masa tundaga kasar zuciyarta tace tahts much bettr, i love you..kansa na gaba yace love u to ma..kan ta karacewa komi har ya shiga car dinsa ya rufe ya tada engine ya doshi bakin gate.
Tsaye tay awajen tsawon lokaci snn ta koma cikin gida,jin karar wayarta akan center table yasaka tay saurin kaiwa wajen ta dauka ganin lambar mijinta ne a ladabce cikin yanayin tausayawa ta gaishe sa tana tambayar sa kufan jiki,..
Dadi taji aranta da yace mata jikin nashi da sauki sosai ,snn gobe suna hanya zasu taho da shi da innono sabida yana son yay surprising taher awajen karban badge honours dinsa na gama NAMC wanda a gobe ne za a kawo tun daga Abuja..
Murmushi tay tana cewa kai honey kajika da zumudi,wato har kayi concluding ya samu result mai kyau ko?
Cikin murmushin ya mayar mata da amsa yace eh mana,im confident about my son s intelligence,he is gifted kema kinsani..taheer zai kara sakani cikin farnciki da alfahari..
Lumshe idanunta tay a hankli tace “Ameen ya Allah may ur wish come true my love..yanzu ma ya fice zaije headquter danyaga ko ya ci kobaici ba.Yace okk ina ita kuma surkuwan namu.Tace ohh wai wasimé? ai ta wuce schl..yace amma dai komi lpya ata fannin ta ko?Sama sama tace mishi eh…yanzu ma ai taheer zakana tambayar haka, bayan yanzu matarsa kawai yake kallo agidan nan,kaima hala inkazo zakagane ma idonki taheer duk ya canza halinshi..
Dariya baban yay yace
Like how i dnt understand…
Cikin takune fuska tace ohhho nide Allah yasa ya samu gurbin karatun nan yay ya tafi can kawai dan wllh bana fahintar shakuwarsu da yarinyar nan ni kar yaje yy wani abunda zaizo ya damemu…cikin haka tafara tsakura mishi abubuwan datake gani hardasu runguma daa pegs..
Shikam Gaba ki daya ya gama dagota dama tun akansa yasan matarsa da kishin tsiya,amma baiyi tsammanin har zata soma jin hakan akan yar yarinyar da bata mallki hanklin kanta bama acikin xolaya ya basar da zancen yanamai cewa
“Kai oyizza…kin dauki abun nan da zafi..calm down nd look at it the positive way,ynzu ne fa dede lokacin da zai shaku da ita karki manta tafiya zaiyi mai dan tsawo,nd ure just here over reacting with him kema kanki kinsan taheer bazai yi wani abu stupid ba..
Cikin rashin jin dadin amsar daya bata tace i hope so,dama ai ka iya shan bakin danka..
Awajenka aishi baya lefi
Dariya yay baice mata komi ba sukaci gaba da hirarsu tana tambayar sa jikinshi har saida goma yay snn suka katse wayar ta nufi part dinta taje tana hutawa..
A fannin taheer kuwa bai iya biyawa inda zaije ba,har sanda ya biya ta makarntrsu wasime.
Kai tsaye ya isa offishin shugabar makarntarsu suka gaisa snn ya roki alfalmar yana son ganinta na minti biyar kacal.
Batare da musu ba Shugaban makarnta ta aika aka kirawota office.
Kirjinta na bugu ta iso da tunanin ko tay wani laifi ne,mamaki ta sha dataga taheer ne a zaune cikin sauri ta zo wajensa tana kallonsa,hannun ta yaja suka tsaya ata waje snn ya saka hannu a aljihunsa ya zaro kudi dubu daya ya dunkula mata a hannunta yana cewa “”Ur break fee” na manta ne ban bayar tabaki ba
Sassanyar murmushi ta sakar masa dan harta cire ranta akan kudin break yau duba da yadda mamanshi tay treating dinta like she dont fucking care, ahankli tace Yaya nagode..insha Allah ai zaka ci jarabawarka da kyau da kyau..yace toh Allah yasa nagode..toh kije aji,tace ok kai zakazo ka dauke ni ko?yaya kai nake son kazo kaji…gyada mata kanshi yay snn ya sake mata hannu yana kallonta harta wuce aji da murnan ganin kudin daya bata a hannunta…tsintar kansa yay yana sauke murmushin da bai wani shirya masa ba,godiya yay ma shugaban makarntar snn ya saka kanshi ya doshi hanyar inda zaije.
Samu yay daf har antaru za’a manna sheet din ajikin notice board.
Daga cikin motarsa ya tsaya yana kallon yadda yan uwanshi sukayi cirko cirko agaban wajen kowa kirjinshi na bugawa musmmn ma wayanda suka rubuta schorlaship exams irinshi dan akwai kashe kudi snn akwai wuyar yuwar samu.
Within some scnds ana mannawa wajen ya gaure da hayaniya kowa na kkrin duba sunanshi .
Wasu da suke fannin sojojin yaqi har sun gani
Wasu da suke na gida suma sun gaggani,tsabar kirjin taheer na bugawa baisan sanda ya maida kanshi jikin kujerar motan ya kwanta tare da lumshe idanunsa ba.