
Daga zarar tay karatun ta gaji sai kuma taji ta rasa nitsuwarta gabaki daya akan taheer,haka kawai kwana biyun nan takejin matsatsin son kasancewa dashi atare da ita,daga ta danyi shiru saita lula duniyar tunanin shi da Dikkan lokutan da sukayi rayuwansu agidan su biyunsu cikin yanayin shakuwa mai dadi da juna.
Duk shirye shiryen da taheer yake na tafiyarsa wasime bata lura da komi,dan haryau bata taba kawo wani abu aranta gameda tafiyar san ba,ta dauka dai koma yaya ne zata dinga ganinshi,dan tunda tazo gidan abu mai wuyane kaga taheer baya gari sai da can dayake zuwa aiki a wasu wajeje shidin ma ya faffarune a lokcin da basu saba da juna ba.
Yau Alhamis da wuri ya shirya yaje ya dauko wasime a makarnta suna tafiya suna yar hirarsu mai dadi karfe hudu da rabi dot suka shigo cikin gidan,tabarshi a falo ita ta wuce dakinta domin ta kimtsa kafin tazo taci abinci dan yau bakaramin yunwa takeji ba.
Yana zaune a falo shikadanshi babu abunda yakeyi sai tunanin yadda zaiyi ya fahimtar da wasime akan tafiyar san wanda yasan bazata ji dadi akai ba.
Gabaki daya kansa ya kulle ya rasa ta inda zai soma fito mata da zancen ta yadda zata gane cewa inyatafi ba zai dawo nan kusa ba.
Dukkan wani shawarwarin da sukayi da mahaifyarshi da kuma anono akan rayuwarsu da yadda zai soma gina future dinshi shiya dan bashi sabuwar karin karfin gwiwa,barin ma da mahifyarsa tay masa alkwarin zata kula da wasime sosai, yanzu abinda ya rage masa shine kawai yay kkri yaga ya cimma burikansa domin ya dawo musu akan lokci.
Can da yamma wajajen bayan magrib lkcin ya dawo kenan daga masallaci dagashi sai wani long sleeve shirt da brown colour pants kafafunshi sanye da normal roaming sleepers
Ya shigo cikin gida.
Tun bayan shigowarsa a falo ya zauna,A hankali yake cin fruit Salad din dake gabansa kansa a sunkuye yana dan murmushin nan nasa mai kyau da ya kai ga har ana iya ganin boyayyen dimples dinsa,saida ya girgixa kai snn ya dago yana kallon mahaifyarshi dake xaune kan kujerar dake kallon nasa fuskarta a dan murtuke ta kafa masa ido tanata kallon sa da fuskan shagwaba
murmushi yyi mai sauti xai yi magana ta rigasa a agaggauce tace”ohh ga mahaukaciya na magana
Ko taheer,…toh bari na memeta maka kaji,..nace ba? tunda yanzu kai zaka tafi anema min sabbin ma’aikata agidan nan amma haryanxu banji kacemin komi ba Ko nice zanna fita ina kai wasima schl ina kuma yin sauran zirga zirgan gida?
Yana kan cin fruit dinsa ya dago kansa a nitse cikin yanayin kyabe baki
Acikin nitsuwar yace ok mum naji,amma ai nace miki kiyi duk abunda kike so,Ta harareshi tace kamar ya inyi abunda nakeso?kai bazaka fadamin naka ra’ayin akai ba toh yanzu kenan komi sainice zanyi agidanan saboda kai zaka tafi kabarni da aiki ko.
Dariya yadanyi yace mumy baga anono ba?ai ba wani matsala,indai zakina kulawa da dabiunsu shikenan kuma dakanku zaku iya nemosu but I just dont want wat hapen last time to repeat itself..shiru tay jin alamar kamr ana musu sallama Ata bakin kofa.
Muryan mace ta tsinkayo abun bai wani bata mamaki ba dan haryau yan gaisuwar ta’aziya basu dena shigo musu ba..
maman najaha ne da yarta najaha suka bayyana sunsha wani dogayen hijabai tare da anono suna shigowa ciki anono ta riko kaya riki riki a hannun ta da ta fito daga wajen wata yar uwanta datace zata wuni
Mata yau.
Kallonsu prof takeyi sosai dan kwata kwata bata gane fuskokin su ba,sukadai ne dama akaf arean anguwar wanda basu shigo sun musu ta’aziya sabida tun abunda ya faru tsakanin wasime da najaha mama takejin wani nauyin shigowa gidan aganinta hala taheer zai iya tona mata asiri.
Duk da haka sai washe baki take famanyi kallo daya taheer ya musu ya kauda kansa yacigaba da cin fruits dinsa ahankli shima yay da fuskarsa kamar baisansu ba
Tun daga bakin kofa anono take cewa ku shigo mana ciki, Allah sarki snnun ku da zuwa
Mariama ganan makwabtan ku tacan layin sunzo,nima anan bakin kofa na gansu atsaye waisun zo su mika tasu ta’aziyar.
Prof ta juya kansu fuska babu yabo babu fallasa tace”Sannunku da zuwa ku shigo ciki mana.
Bini bini suka shishgigo uwar ta zauna akan cushion najaha kuma ta nemi waje a ƙasa taxauna kirjinta babu abunda yakey banda bugawa tanayi tana sauke kai kasa kasa tana satar kallon taheer da ko daga idanunsa awajen baiyi ba
cike da barin baki Maman najaha tace ina wuni prof?ya hkrin mu,saita dan kalle taheer aggaugace tace ya kuma akaji da hakuri.
Prof ce kawai ta amsa tace alhamdullh Hkri mungode Allah
Shikam yana shiru baice komi ba
Cikin sanyin murya najaha ma ta rusuna ta gaisheta ayayin da dukan hanklinta yake kan taheer
Prof Ta amsa babu yabo ba fallasa..Tana kkrin tambayarsu kenan saiga can wasime na saukowa daga steps sanye da hijab ajikinta ta riko plates a hannunta wanda takai abincinta na tun dazu daki taci..
Tana haÉ—e ido da su najaha ta wani harde ranta ta sauko kasa fuskanta ba’a sake ba..sama sama ta rusuna ta gaishe su kanta na kallon gefe jin yadda maman najahar ta waske gameda da sakankacewa da bayanin cewa ai wasime babban kawar yarta ce,daga nan tahau yi ma prof bayanin location din gidansu a anguwar duk dama bawani fahimtarta takeyi sosai ba.
Suna cikin hirrarsu taher
Ya miƙe zai bar wajen,har sanda ya mike zai tafi snn yay gyaran murya yace ma wasime tabiyo sa da sauran fruits salad dinsa dakinsa.
Kamar wacce take jirar yace hakan ta amsa da toh snn ta wuce kitchen taje ta ajiye plates din ta dawo marmaza ta dauko fruits salad din tabishi dashi dakinsa dashi
Kusan dukansu wajen satar kallonta sukeyi harta lume kafin suka cigaba da hirarsu har wajen karfe tara basu tafi ba..dukan su suna ta tsammanin ganin fitowar wasime daga dakinshi amma sai shiru.
Tsuliya a zage suka ce zasu tafi,zuciyrsu tam da bakin cikin rashin samun hanyar da zasu nuna ma prof alakarsu da wasime
Koda ma za’ana dan welcoming dinsu a gidan insunzo Uwa uba ga taheer ma da ko kallonsu baiyi ba bare ya amsa maganansu.
Anono ce ta rakasu har waje prof kam tundaga bakin kofa ta musu sallama ta wuce dakinta sabida nauyi da idanunta suka farayi.
A fannin wasime kuwa tana shigowa dakin ta sameshi zaune a bakin gado yana latsa wayarsa acikin nitsuwa ta aje fruit salad din agabansa snn ta zauna kusa dashi.
Batare daya kalleta ba ya wani jawota jikinshi tafado yay maza ya kankameta yana shunshuna ta gefen fuskarta sabida dadin qamshin turaren data shafi mai balain sanyi da shiga rai dake fita a sassar fatar jikinta.
Tare suka zauna suka cinye sauran fruits salad din yana bata abaki itama tana bashi,sun ma mance da mutanen da suka bari acan palo.
Janta yay suka haura saman gadon suka kwanta side by side suna kallon juna”Ahnkli yana lullumshe idanunsa da tarin tunanin yadda zai soma rayuwarsa tsawon lokci batare da yaga kyakkwan fuskartan nan ba..itama kallonsa kawai take jin yadda kewarshi yake dada nanewa acikin zuciyarta,dada lumshe idanunta ty jin iskan bakinshi mai sanyi na wanzu akan fuskarta da sanyin muryanshi mai nakasa gabobin jiki yace
“Yau Allah ya kawoki wajena ko?bakinta ta turo gaba tace Ai kaine kullum bakada lokaci
Yana shafa gefen fuskarta yace did u miss me?ta gyada kanta snn tace alots..uhmm baka gama mkrntar ba to ina kake zuwa ne kwana biyu?Tashi yy ya zauna da ita ajikinshi ya fara mata bayanin abubuwan dayake yi game da tafyarsa,har yagama batace mishi komi ba.