
haka aka ci gaba da kiran sunayensu har sai da aka kira duka students din sannan aka yi musu standing ovation tareda tafa musu dukansu a kan stage in kowannensu ya cire graduation cap inshi suka sa ihu ana musu hutu,kowa kujeranshi ya koma bayan nan, lokacin ne aka fara presenting beautiful prizes for the best overall graduating students.lkcin kirjin kowa na bugawa da fargaba.
Itadai kewar yayanta kawai takeji aranta mai tsanani acikin zuciyar Taso ace yana nan yau
Da bata san wani irin farinciki zataji acikin zucyarta ba.
Overrall Best in mathematics aka fara kira “wasime aliyou” tafi aka saka mata taje ta karba bata dawo wajen zamanta ba akace best in chemistry,best in biology best in further mathematics,best in computer science nd economics,best in agric science,best in physics,duk ita .Atake hall gaba daya aka mimmike tsaye ana tafa mata,prof oyiza was feeling extremly proud tana cewa thats my doter
Tafin ta haryafi na kowa Anono dake sauke hawaye kamar wanda ake saka mata barkwano a ido itakuma Iyayen wasime kawai take tunawa tana ta kuka tana matse hawayenta da bakin gyalenta,cikin sauri prof oyiza ta fito walking proudly ta haura kan stage taya wasime rirrike gifts dinta akan stage din photgrphers sunfi ashirin anata daukar mata hoto.
Tundaga wajen prof take saka mata albarka idanun wasime kamar zai zubda hawaye tsabar yadda zuciyarta yake matse da burin ganin yayanta anan wajen yanzu.
Har wani imagining dinshi takeyi a kusa da ita a duk sanda ta amshi kyautar,her heart was so weakend by diffrnt kinds of emotion,tasan duk duniya babu wanda yy desrving yaga wannn ranar face yayanta dayasha wahala da ita.
Sai wani mutumi da wasime tay noticing tun shigowarta yake daukar mata hotona da xpensive 3D cannon cameran sa, yanzu kuma videon ta taga yake da iphone cameransa kusan kowani motsawarta sai yay capturing ya tura ma taheer clip din yana daga can U.S yana kalla a system dinsa yanata murmushi a dakinsa shikadai duk basu sani ba..
Daga baya aka fara kiran sunan headboy mubarak ya karbi Nashi best in accounting,commerse english da technical drawings,Sauran daidaikun Kyautukan kuma aka bawa sauran students,Najaha tana ta tura baki ganin a home
Economics kawai ta samu kyauta.
haka aka ci gaba da bawa wasimé prizes asif today is her day alone har gifts na most brilliant,most obedient,uwa uba itace neatest..snn aka ba asisstant inta most punctual..akaba wasila best in socials duk da su mubarak,snn aka babba duka prefects din kyauta.
Dj ne ya kunna ma wasime wakan “unstoppable” by sia,mates dinta sunata mata murna suna zagayeta dan tafi kowa karban prizes a wajen Kowa na admiring dinta koma wacece ita Masha Allah tayi kokari sosai.
haka aka ci gaba da bidirin daga karshe aka rufe da addu’a,tun suna ciki suka fara daukar hotuna da yan ajinsu har suka fito waje,all eyes was on her kowa ma hirarta yakeyi sabida karramawar data sassamu..
Daga nan Kowa wajen family members dnshi ya wuce anono ta fara rungumewa tace mata Autana Allah yasanya Albarka,Allah ya taimakeki yasa kifi haka”, daÉ—i ya sata cewa Amen.
Daidai lkcin prof take karasowa wajen tare da su bilti da wasu friends dinta data gama koÉ—a wasime awajen su tana cewa ai dougther inlawn tace,kowa nata mamakin jin hakan, kawai saivsuka bari a irin engagement din nan ne dan batagaya musu yaushe akayi bikin taheer ba.,daga nan wajen bilti wasime ta koma suka wani rungume juna, da murmushin murna a fuskan bilti ta shafa kan wasime ahankli tana cewa “Sannu mrs taheer Allah yayi miki albarka wasime na kinyi kkri sosai..im sooo proud of u..gashi kinyi kyau kin dauka ma oga hoto kuwa.?
Sassanyar hawaye ta soma sauke wa bilti kamar wacce akace zaginta kawai tay, bilti tana kallonta sai kuka take mai sanyi ta sunkuyar da kanta can kasa cikin sanyin yanayi kmar ba ita ba,yarda zaka san kukan ya shigeta tun tuni dannewa take acikin zuciyarta hartana jan sheshheka
hannun ta bilti taja sukay gefe dan kar agane me take ciki
Sukabar anono da prof sunata rarraba abinci da drinks ma few invitees din da sukazo musu and oda guests anata raha ana dariya..Prof kam abin nema ne ya samu dan jin kanta take kamar ita ta training wasime harta sassamu irin wayannan karramawan.
Agindin wani bishiya bilti taja hannun wasime suka zauna ta inda ba’a kallonsu, tun kan tace mata komi tafara rarrashin ta tana bata hakri har sanda taji nauyin dake kan zuciyarta yay sauki snn
Ta tambayeta meye ne damuwarta
Ahankali wasime take sauke ajiyar zuciya saboda fargaba da tashin hankalin da zuciyarta ke ciki,
wani tsiririn numfashi taja hade dayin kasa kasa da kanta dan sam bazata iya kallon kwayar idanun bilti a wannan lokacin snn tay mata karya ba.
Ahankali tasoma magana muryanta kasa kasa cikin in..in..ina da sanyin jiki tace bilti daman..daman..”yaya na ne” daga nan shiru ta danyi tana fidgeting fingers dinta kanta asunkuye take idanunta suka kara tara wasu sabbin ruwan hawaye tanajin wani sabuwar feeling din tsananin kewarsa dake dabaibayeta,a cikin shagwabbiyar yanayi tanamai takune fusknta da sakalci tace,’..Toh Bashi ba ne..saiyana ta fadomin acikin raina..bilti wai yaushe ne yaya na zai dawo Dan Allah?
…shiru ta kumayi tana dago kanta sai zirrrrr hawaye masu rauni suka sauko mata bisa kuncinta, kara fashewa da kuka tay mai tsanani cikin kukan take cewa “ni wallhy na gaji da jiranshi, koyaushe inata jira ko zan ganshi yazo gashi harna gama schl din bai dawo ba.
bayan..bayan..shiya
cemin fa zai dawo…i really missed him soo much… Ni kwata kwata banji dadi da banganshi yau ba,ni banajin dadin komi,…. inata so yayana yazomin…Aida yazomin dana jidadi sosai, acikin matsanancin kuka ta karashe maganan fushin bakaramin shigarta yay ba.
Jawota jikinta bilti tay ta rungumeta ganin kukan nata yafarayin yawa tace “wasime kiyi hakri dan Allah…kinga za’ay ta kallon ki kina kuka anan wajen…kiyi shiru kinji?
Da kyar ta dena kukan ta dago kai tanajan shesheka bilti tana dan shashare mata fusktanta cikin sigar lallami har sanda ta danne kukan tas snn ta riko hannayen ta suna fuskntar juna da sanyin murya tace “wasimé nasan abun da wuya amma ki kara hakuri,ki daure.. nasan duk inda taheer yake shima hanklin sa baiya kwance kalau ynzu
..inamai tabbatar miki da cewa da yana nan da saiyafi kowa son ya kasance dake awann ranar taki ta farinciki
..kimasa uzuri kinsan bazai taba kyaleki hakan nan kawai ba ko?
Ta dafa gefen fuskarta acikin nitsuwa tace ki kwantar da hanklinki ki fahimce shi kinji wasime na?Ai Tafiyar ya zame masa dolene,even u wll like a husband with a good future nd capablity to take care of all ur future responsilites koba haka ba?jiki a sanyaye tace haka ne,”yo shine kuma bazaki karfafa masa gwiwa ki goya masa baya dan yanemo muku abunda zaku dogara dashi arayuwan ku tanan gaba ba?wai wayace miki soyayya is enough..Wat about ur future with him..ga yayan da zakuzo ku haifa..ko so kike yayanki su girma acikin wahala da talauci,yau ko taheer baiyi kudi ba atleast in yana da abunyi asirinki ne zai soma rufuwa wasime,duk abunda yakei arayuwansa domin kece dnt forget dat, ayanzu kece abu mafi kusanci da zcyarshi kece kuma mai rufamishi asiri..kiyi hkri kinji?ki kara yin hkri kijirashi wata rana sai labari kinji ko?