
wasime ta dada binne kan ta kasa cikin jin nauyi cos prof ta dade tana son taga wasime tana gaisheta da yare.
Danne kunyarta tayi cikin sanyin murya tace..
“Im sorry ma nadan manta ne..sai ta danyi shiru can snn tace Olodudu agba,echo lpya? …shafa kanta prof tay with broad smiles tace ” emi lpya ozoza Nago! ..daga nan murmushi suka sakar ma juna mai sanyi,wasime tay shiru bata kara yin ko tari awajen ba.
Prof ta gama cin fruits dinta tana satar kallon ta,can ta juyo cikin harshen yaren take tambayarta ko zata iya shiga kitchen din yau sabida tun shigowarta taga kamar bida jikintan kawai takeyi saffa saffa tana nokewa.
A kunyace wasime ta dago kai suka hade ido tace “eh zata iya”…prof ta dubeta da kyau tace r u sure?In bazaki iya ai ni zan iya shiga kitchen din inyi..Kanta ta sauke kasa da wuri tace im sure ma..prof tace toh shikenan its ok..saikije ki masa kalar naki girkin da kukeso nasan bazai wani dade ba zai dawo,inde kinga kamr bazaki iya am alwys here,snn karki damu dani already anono ta riga tay mana abinci mun karya tin sassafe munci tare da ita.its just u nd ur husband now ok?
Kanta na can kasa tace “okay mommy toh bari naje…tana fadin haka ta mike tsaye a kakkame.
Prof nabinta da kallo tace “alright”…wasime tana ficewa prof tay dan murmushi sanin cewa ba lallaine ma’auratan su sake agaban su suyi rayuwar auren su ba.
Kuma dama alkwari taheer ya mata na cewa zai dan zauna da ita a gidan nan in ya dawo zuwa lokcin da za’a gama decorating da furnishing din sabon gidansa,at dat time sai su tare shikadai tareda matarsa su kyaleta anan itada anono.
Ahnkli ta jingina kanta da cushion cikin yin wani sabon nazari akan hakan cos she dont wanna be selfish with him anymore, can cikin nazarinta sai taga mezai hana tay musu suprise honey moon ticket zuwa wata ƙasa?
Murmushin gamsuwa da wann nazarin tay,Ta mike zaune cikin sauke ajiyar zuciya tace well,hakan zaifi nuna adalcinta da godiyarta wajen danta gameda dukkan abubuwan da yay dominta,babu karya taheer has been her comfort tun randa mahaifinsa ya bar duniya. Da Allah ya buda mashi kuma itakanta ta shaida kafin yay ma kowa alheri saida ya mata,ya bata kudi ya siya mata qaddarori ga wann fankacecen gidan daya sakata aciki,ahalin yanzu
Dai tasan dai babu abunda zata nema a duniya na abun duniya wanda baxata sameshi ba.Tunani tay aranta tana cewa “Danta derseve some rest, afterall shima ya kamata yaje wani wajen ya huta ya kuma samu nitsuwa mai kyau tareda matarsa Koda na sati biyune kafin ya dawo matan aganinta ai taheer ma yay kkri sosai.
Wasime tana isa sashen anono ko sallama batay ba suka hade ido tun a bakin kofa, anono ta tare ta da masifa tana cewa “wnn hijabin na menene haka wasime..?dan ubanki bazakiyi wanki kiyi kwalliya wa mijinki da safe ba kinwani sha doguwar hijabin kamar wata matar liman mai shan jini?da turin baki wasime ta shigo ta nemi wajen zama da kyar ta zauna sabida dan zugi zugi datake ji akasarta,
Tana kkrin gyara zamanta bata hankara ba anono sai kallon yanayinta take kamar me tana mamakinta.
Wasime Tana dago kai suka hade ido, ta wani hade rai cikin sigar shagwaba tace”Yo Inno wnn wani irin kallo ne haka?kyabe baki inno tay cikin jan tsuka da son jin bakinta batace komi ba ta nemi waje ta zauna sai can tace amma kinyi wanka kuwa?
Rau da ido wasime tay tace inno kamar ya nayi wanka?nayi mana..nifa bana son haka..ta fada a kunyace kamar zata saki kuka ta dauke kanta
“Toh laifi ne inna tambaya, Yo ba dole na tambaya ba,yarinya daren farko aganki garau kina yawo tsakar gida sai kace ba budurwa ba..ohh ni aishatu naga jalala yaran yanzu da shegen jarabar tsiya…ko cemin zakiy ke baki bi mijin naki dakinsa jiya ba?nafaga wani signa dakiketa masa wajen cin abincin nan..da wann tsinannen kayan da kika saka jiya ai kamata yay yau inzo in sameki rugugu akan gadonsa bakya ko numfashi.
Sulalewa kan kujerar wasime tay ta rufe fuskarta da tafin hannunta tasa kuka mai kara.
Inno ta mike tsaye tana dariya sosai harda rike ciki tace”ke danci ubanki nikam wallhy nagaji da shegen koke koken kin nan..katuwa dake kina matar wani kato,Daga anmiki magana saiki bare wa mutane baki kamar wata yarinya karama. Karya nay mikine?jiya ba jarabar bane ke damunku?
Baki ture cikin shagwabben kuka wasime ta mike zaune cikin yanayin bori hartana rufe ido cikin masifa tace”Inno bana so, bana son haka,yo Meyena wani cemin kamar ba budurwa ba,Haka kawai dama sai inje dakinshi inyi mishi me..?ni fa babu abunda ya sameni ina dai dan kinga kafana ne dayake min cuwo a fa a dakina na kwana,inbaki yarda ba ai zai dawo sai kije ki tambayeshi. Ni ai ba yar iska bace…kai inno wann sa idon fa?tana share hawayenta ta turo baki fuskarta a shake ta gama fada.
Dariya sosai anono tay ganin ta cimma burinta a saukake,dama so take ta san wani abu danta san wasime da shegen tsoron tsiya,kyabe baki tay Snn tace “Kinyima kanki wallh”>yo har wani abun fadane da zakice min baki kwana agefen mijinki ba?dan ubanki wakike jira ko sai kwayayen mahaifarki ya dafe kinzo anayi babu haihuwa..haba mana nide nasan za’arina karuwa da haifuwar dan shege.ke wallhy kinaban kunya inbanda kauyanci uban me ya hanaki zuwa dakinshi ki kwana?kan wasime na kasa lokacin
Ji take kamar xata nitse kasa don kunyar anono.
A daddafe ta mike tsaye zata fice anono ta rikota
Tay saurin rufe fuskarta da tafin hannunta “anono tace abar kunya ya kare a gindinki tunda ba’aje ko inaba kina nunawa namiji ke raguwace,nidama bakinki nakeji dan nasan halinki da shegen taurin kai duk nasihar ta nutsu da manyan mata suka taru suka miki anan bazai shiga cikin kunnen kashin nan ba,Allah na tuba aurenki shekara nawa keko kunya bakiji ba?zainabubu kawarki acan gida wallh yanzu yayanta sunkai biyar a daki..gakinan anan kin tsaya ragwanci jiya miji ya dawo yau aganki garau harkina mana yawo a tsakar gida”
Yo Allah sa nan da wata na gaba dahiru ya kawo min wata rangajejiya wacce aa daren farko ma wallh sai an hada da asubuti, na gaji da iskancinki wasime haka kawai zakina masa gwalo da wani motsatsen jikinki?hekara nawa zaiyi yana jiranki,durkushewa kasa wasime tayi ta fashe da kuka sosai jin anono tana mata dariya,cikeda haushi da bori tace”ni wallh ya isheki haka anono waimesa baki sona ne?yo haka kawai zakina min dariya kefa bakisan abunda ya faru ba..
Anono tana dariya ta tsuguna gaban ta tana kallon rikitattun idanunta da suka jikke da ruwan kunya cikin tsantsar neman tsokana tace”Yo meyey ya faru gayamin mana auta na?shirun da wasime tay mata hadi da yin banza da ita yasa ta kara cewa ‘”yo Ince dai irin jinkirin da kukeyi kenan harkusa majazen ku suje neman mata a waje.
Mikewa wasime tay cikin wani sabowar kuka tace “Allah ya sawwake yayana yay neman mata awajen..fatanki ya sare kashinki..ni wallh kinga tafiyata nagane take takenki dama tuntuni so kawai kike ki zageni.
Anono tana kan dariyarta ganin ta birkitata tace “Yo anzageki din inkinji haushi a gobe gobe inganki da cikin dahiru acikin tumbinki.
Wani Fuuu wasime ta tashi tay waje tana tafiya a hatsale tana gunaguni tanajin inono na rakata da dariya mai ban haushi.