
Amma Saboda fitsarin kwancen nan yasaka duka wani kuzarinta ya gushe agidan,kallon kanta take kamar wata kazama.
kunyar bilti takeji aboye har cikin kokon ranta tanajin nauyi shiyasa kawai ta yanke hukuncin wanke kayan fitsarinta dakanta Basai an wanke mata ba.
Duk shiyasaka bata son fitowa bare ta samu kyakkywar fahimtar juna tsakaninta da surakunanta gani take kamar izuwa ynzu duk sun san tana tsula fitsarin kwance,abun nasaka taji kunyar kanta bakadan ba.
Washe gari jumu’a da alaman yau babu kowa a gidan,bilti ce kawai a kitchen alhj qasimu da matarsa sun tafi ikko dansu basa wani zama.
Kirjinta na mata ciwo yau haka ta farka a bacci wani iska mai sanyin gaske ne yake kadawa yana ratsata har cikin kasusuwanta tanajinshi
,mikewa zaune tay akan gadonta snn ta kama handle din windown ta leka kadan ganin gari ya rufa,lekewa ta dadayi taga wani bakin haddarine a sama Cikin sauri ta ja windown ta rufe sabida wani iska mai ƙarfi daya busota hancinta.Tana kammala rufe windown ta sauƙa kasa ta tattara inda tayi fitsari snn ta nufo waje.
Ko takalmi bata saka a kafafunta ba tashiga saukowa ahnkli cikin sanÉ—a zatayi waje,kwata kwata batason bilti taji motsinta a sanyin nan tasan bazata taba kyaleta ta fita ba,ita kuma batason tazauna da kayan fitsari a daki mostly shitake fara kawarwa snn tayi alwala duk hanata da bilti takeyi amma batajin magana.
Yauma babu motsin kowa a waje ita kadai Tana durkufe agaban tap tana wankinta as usual tanata shafawa kamar wacce batada jini ajikinta,gabanta ne taji ya fadi,barin wankin tayi a hnkli snn ta juyo tana dago kai kuwa suka hade idanuwansu waje guda da wani kywkkwan saurayi wanda tunda take arayuwanta bata taɓa ganin mai irin kamanninshi ba.
Its 300# ka subcribe
via 0152983148
Mohd surayya sule
GTB send ur evidence to 08060712446
Or mtn Pin.
7/25/22, 19:19 – Kawata: FITAR RANA…
……faduwarsa
BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.
No.8
ACikin sauri tabar wankin ta miƙe tsaye tare da ja da baya tana mai tsura masa fararen idanuwanta tanata kallonshi shima kallonta yakeyi tun daga can nesa yana tahowa cikin takunshi mai sanyi daya gama burgeta.
kyakkwar fuskarshi dauke take da wata iriyar murmushi mai matukar daukar rai,hadadde dan gaye,sumewan tsaye wasime tayi..shikuwa aransa cewa yake..wow ive seen an African queen.”dan kuwa babu abunda yay mugun tafiya da imanin sa sama da shiny luminious dark skin dinta,wanda baiya bukatar ado ko wani kwalliya..he has neva seen a black beauty like this one.
har ya iso gabanta kwakwlnsa bata samu cikakkiyar nitsuwa,kallon junansu kawai suke basu kifta idanunsu.kunya da fargaba duk ya kama zcyar wasime,kyaunsa da gayunsa sosai ya tafi da ita, gashi duk tajiÆ™e jikinta da ruwa kamar wata yar bola,gayen ya kalleta snn ya kalle cikin bucket dinta,wani murmushi ne ya kufce mishi,miÆ™a mata hannunshi dayasha ado da diamond wristwach da saphire ring dark red in colour yay..yana murmushi mai taushi cikin murya mai sanyi yace “hey,hello beautiful Angel..,shiru tay tanamai sunkuyar dakanta Æ™asa. ganin bata motsa ba ya dauki bukitin kayantan Ya fara jera matasu akan clothline..”..Kyakkyawa baki maganane?kanta ya shafa kadan…ure so damn beautiful. ina mum dinki kika fito cikin sanyin safiyar nan kina wanki?u shud be on ur bed by now!!ina mama?kanta ta sunkuyar kasa sosai muryanta kasa kasa tana jin kunya kunya ahankli tace “tana cikin gida”..yace shine ke kika fito waje?tace ehm “dama wanki nakeyi”
Dan dariya yy yace “I seee”…what a beautiful voice u got,yana furta hakan ta sauÆ™e broad smiles a bazata..setin zcyrshi ya capke irin”ohh my gosh wat a smile, u will definately kill me kina kasheni fa…kanta ta sauÆ™e kasa dan kwata kwata ita bata fahimtar meyake cewa sosai da sosai,tsinta kawai takeyi dan ita bawani iya turanci tayi sosai ba dan zamansu a jos ne ma yasatake dan iya gamutsawa kadan kadan but not all the time takeji,saheeb yana murmushi ya aje empty bucket din a Æ™asa snn ya dan nuna chest dinshi da yatsa yace”Ahhm! sunana Doc saheeb..ni likita ne..”Kefa beauty?.meye sunanki mai shegen dadin nan?i know ur name most be special.Mayun idanunshi ya zuba akanta yana sauraron ta,dan kadan ta dago kanta tanajin nauyi nauyin shi a kunyace sosai tace “Emm Ni sunana “wasimé…
Murmushi yy yace “wow”yana mai jinjina dadin sunan har cikin zcyarshi yana wani lumshe idanunsa yace “uhm dats so unique!..ke yar uwan Tej ne ko?ive been coming here amma bantaÉ“a ganinki ba ya akayi hakan to..budan baki tay kamar zata bashi amsa kirjinta ya buga da wani irin Æ™arfi a tsorace ta juya ta kalli bayanta taga ashema biltice ke tahowa.
amma abayanta kuma sai taga wani abu kamar inuwar mutum wanda tabbas tasan babu makawa shine.Wani hadiyar yawu tayi abazata dan ta dade kuwa bataganshi ba, atake ta zamto tamkar wata kurma tayi shiru bata ƙara kuma dago idanuwanta sama ba, bilti tana isowa daf suka hau gaisawa da saheeb din dake shi yana da son wasa da raha take ya shiga gaya ma bilti dk yadda sukayi da wasime.
Yace”Bilti dama wannan yarki ce?she is so damn cute…murmushi kawai bilti tay batace mai komi ba tajanye hannun wasime suka tsaya tare da ita agefe itakam tasan gogan na lura dasu kuma zai iyayin Æ™orafi akan yanayin da wasimé ta fito, lura da iyayensa sun riga sun dora masa nauyin jagorantar gidan kafin su dawo daga tafyarsu”
..Daga can baya baya taher din ya tsaya,bai ɓata lokcinshi ya iso garesu ba dan baison ma ransa ya ɓaci,kallonsu kawai yake daga can nesa da idanunshi da suka riga suka kankance da masifa, duk abunda suke fada yanaji daga inda yake amma yanayinsa kwata kwata bai nuna hakan ba.
wayarsa yasaka agaba yana latsawa sosai.da kyar ma yake daga idanuwansa sama barema ace ya musu wani kyakkwan kallo.muryan sa ciki ciki kuma a matse yace “guy cmon lets go in,saheeb yace toh am coming”..ya kalli bilti “bari naje ciki pls a cup of coffee.
Cikin sauri bilti ta riko hannun wasime tana kkrin janta ciki,ta amsa masa da cewa ‘toh za’a kawo insha Allahu..gefen fuskan wasimén yadan shafa daxai wuce snn ya wuce din yy ciki,lkcin tej har ya isa bakin kofa da naturenshi na fushi fushi ya bude ya shiga saheeb na biye dashi abaya.
Kallonta bilti tayi snn ta karkada kai “toh Zo mu wuce ciki,kefa bakijin magana wasime ai saida nace miki kidena fitowa wanki anan amma kikayi banza”toh wuce muje ciki. tsadaf tsadaf ta bar jikin tap din bayan ta kulle ,bilti ta cigaba da mata fada sabida sanyi sam Batason ciwonta ya tashi ko wani abu yazo ya sameta,Harta gama surutun Wasimé bata ce mata uffan ba tana famar juya hoton wancan kyakywan mutumin acikin kwayar idanunta,aranta tace dagaji yana da hankli.
Nannauyar ajiyar zcya ne ya kufce mata snn ta wuce bayi tay wanka ta doro alwala tazo ta sauya kaya,riga da zaninta tasaka na abc koriya da fari fari sosai ya mata kyau,kitchen ta nifa ta samu bilti ta kammala musu abun kari.da kallo daya bilti ta bita snn ta mika mata wani abu acikin kofi tace..”zauna acan kisha ruwan zafi ne…inkin gama zaki tayani kai abinci,babu gardama tace toh.akan plastic chair dake kitchen din taxauna takai cup din bakinta slowly,ahnkli tafara shan ruwan zafin har sanda wani zufa ya karyo mata a goshi,kafin nan bilti ta shirya tray na breakfast dauke da tea flask da sauran tarkace
Ta kalli wasime tace,riƙe min jug din toh,karba tay tana cewa toh snn suka fita suka doshi hanyar dakinsan a tare.