FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin wasime ta dawo hayyacinta sosai yasa bilti zamewa taje gidan ta sameshi yana zaune a falo shikadai yana kallo

Bayan sun gaisa ta kawo masa maganan wasime
Harta gama baice mata komi ba,dake tsafin ba ayi harda ita ba sai bai wani mata rashin kunya ba,magana daya tak ya furta mata daga kanshi bai sake ce mata uffan ba..”yace kije kice mata ta dawo gida amma inta shirya zama da matata inkuma bata shirya ba ta cigaba da rayuwarta acan ni banason shegen fitina..”..duk nasihar da bilti tay masa baisan ma tanayi ba,razia tazo ta dinga hararta danko ruwa ba a bata agidan ba haka ta tashi ta fita.

Bayan kwana biyu takai wasime wajen wata babban malama tay mata nasihohi sosai tace mata tay hakuri ta zauna a dakinta,koma yaya ne tasani aurenshi nakanta kuma hakkinta ne ta kula dashi,tunda shi aure ba don jin dadin juna kawai akeyinshi ba,challenges
,calamities nd detours wll come,marriage is not a bed of a roses,is a capert of rose md thorns yau zaka taka rayuwa mai dadi gobe zaka taka rayuwa mai muzantawa.

Kuma dama shi aure ibadace,dan haka ibada saida jajircewa ake cimmata..haka suka taru suka babbata karfin gwiwa akan taje ta zauna
Tayi tay ma mijinta addua snn karta bijire mishi ta sani acikin wnn yanayin ne yafi bukatar ta a kusa dashi.

Wa’azinsu sosai ya taimaka wa wasime daga wajen sukaje suka tattara kayanta bilti ta dawo da ita gidan mijinta
Sukayi sallama ta tafi.

Saidai tunda ta dawo gidan bata gane kan komi ba,sau tarin yawa taheer zai kalleta amma bazai taba zuwa inda take ba bare ya mata magana,gashi bata da daman zuwa nashi dakin ganin anan raxia ta tare dashi tana zama.

These few days has been the worst nd toughtest moments of her life,ganin ta zamto kamar ghost wife kominshi da razia yakeyi
Tanaji zasuci abinci suyi kallo koda tazo ta gaishesa baya ma kallonta bare ya amsa.

Sai wani dan iskan kinibibi da razia ta samo na lallabarta tana mata magana cikin saukin kai da nuna kamar babu komi daya faru.

Kan wasime sosai ya kulle akan sauyawar fuska da razia ta tareta dashi,ita take zuwa dakinta ta sameta tana ce mata tunda ta hakura ta dawo su hadakansu suyi zaman lumana.

Wasime tun tana kin kulata harta zo tafara jin maganganunta,sabida shirun taheer akanta yay yawa sosai,wani bin tana fara masa magana intaga yay mata shiru sai tay ta kuka,duk ta dauka fushi yay da ita..gashi Allah ya zuba mata matsanancin kaunarsa aranta bazata iya daurewa bata zo inda yake ba.

Adan dolenta ta fara sakewa razia fuska ko aganinta hakan zai saka ya sauko ya zo wajenta itama koma ya dinga amsa magananta amma ina saida ta gasu sosai kafin yafara kulata.

Hakan ma sabida razia ne yay mata magana,ya umarceta akan tanayin girki a gidan sabida razia tace tana so kuma bata iya ba.

Duk zuciyar nan nata saida ta nema ta rasa a lokci guda sabida tana matukar son mijinta,duk abunda ya umarceta tay takan daure tay aganinta hakan zai iya sawa ya dawo dede amma kullum abun gaba gaba kawai yakeyi In ya mata zafi sosai ne saita je gidan bilti tay ta kuka haka bilti zata kara lallabata ta dawo da ita.

Duk abubuwan dake faruwa razia tana gayama saheeb step by step kusan komi in zata aikata saita nemi izinshi
Wani abunma shiyake tsara mata yadda zatayi

Da wasa wasa Abubuwa sune neman su ja musu lokaci sabida razia ta gaya ma saheeb cewa tana shan wahala wajen kirar taheer a madubi,snn haryau yaki ya fara shan giya tana kuma jin tsoron yadda matarsa ta kafe tanabinshi sau da kafa takiyin fushi dashi bare ta samu damar rabasu kwata kwata.

Saheeb yace mata sam bai iya ji ba,kota kara kkri
Koya fasa zancen auren su..haka ta dawo tana tsafi agidan gadan gadan babu dare babu rana tana hada taheer da mugayen alkaba’irai.

Rainin wayon razy ayanzu shiyafi komi daga ma wasime hankli,tun da ta lura da cewa wasime ta kafe akan son mijinta bata son tay fushi dashi ko taga laifinsa akan duk abubuwan dayake mata yasa ta fara wahalda ita da oder,tamaida ta kamar yar cikinta zata saka ta girki a duk sanda takeso inta ki kuma saitaje ta gaya ma taheer yazo ya tursasa tayi ko ta debo wanki tay kadan saitaje wasime tazo ta karasa ko guga wani bin wasime tanayi tana kuka ga taheer yasha mata masifa akan hakan ita kuma batason tana saɓa masa.

Inta gama cutar da ita sai tazo dakinta da salon makirci tay ta bata hakurin karya,da wasa da wasa har wasime tafara sabawa da halayyarsu.

Sam baya kulata inde ba akan maganan razia ba,
Ita kuwa alkcin wani irin makahon so take masa duk dama baiya kulata,baya kwana da ita amma iya maganan da sukeyi akan razian ma yakan sanyaya mata zuciya duk dama duk dai cin fuska ne.

Gabaki daya zancawar taheer ya rikitar mata da yanayi,lokaci guda wasime ta rame ta kwankwade ta cusa damuwa sosai acikin zuciyarta,tana so taga ta jajirce wajen ibada amma batada nitsuwa gaba daya ,ko salla zatay harta fara ta gama tana cikin tunanin mijinta kishinsa mai yawa ya takura mata zuciya yana azabtar da gangan jikinta sosai.

Kullum ta kwanta bacci ta dinga tunani kenan,
Kota saka zoben daya saka mata agaba tana kallo tana tuno da alkwarukan daya ya mammata nacewa bazai taɓa dena sonta ba koda baya tare da ita.

Wani bin intana tuno da rayuwansu ta baya sai taji karin karfin gwiwan zama dashi ahakan,wani bin kuwa takanji matsancin kishi da bakin ciki mai zurfi dayake mamayeta.

Duk ta dauka kalar soyayyar da sukayi shine yake nunawa razia,ita kuma ya gama da ita ta dauki cikinshi ya kyaleta.

Ranan asabar da safe Razia ta fito daga dakinsa sanye da wandon jeans da wani tsinannen riga, daidai lokacin wasime ta kwaso hijabs dinta kenan daga machines data wanke zata shanyasu a waje

dan lekata tay taga hanklinta baiya wajenta atake karkace kafafunta cikin sanyin jiki tana tafiya atattale tana wash wash rike da gefen mararta tana wani yatsina fuskarta tamkar wanda zatayi amai..

Hanyar da wasime tayi itama ta nufa ta sameta tana kan jera kayanta a clothline Bata hankara ba taji an dafo kafadunta tana juyawa suka hada ido da razia,dada takune fuskanta tayi tanamai langwabar dashi.
Da kallo daya wasime tabita snn ta dauke idanunta akanta cikin dauriya tana cewa “Anty lapya kuwa?

Magana razzy ta somayi a sassarfe,cikin nishi nishi mai cikke da kisisina tace ina kuwa kiga lpya sister?wallh cikina ciwo yakemin tun dazu,nasha magani yaki denawa,goshh duk nayi stain kuma bazan iyayin wanki ba..dama ganinki kina wankin kawai yasa na dan fito, Allah yasa zaki iya taimakamin sai inje na dan tsaftace jikina a bathrum.

“…wasime ta cigaba da jera kayanta batare da ta juyo ba ciki ciki tace ayya Allah ya kara sauki anty
Amma Dame zan taimaka miki yanxu kinga ni cikine ajikina ban ajiye pads..

Wani kullin kaya raziya ta fito dashi daga bayanta yana kumshe daga cikin black leda bag wanda ta boye a bayanta snn ta mika mata,damke cikin tayi tana wani murde murden karya Muryanta kamar zai dauke tsabar kisisina A manakisance tace “a’a ba pads zaki bani ba ga taimakon nan pls my sister help me and wash them kinji?..

Amsar kullin ledan wasime tayi a hannunta
Batare da ta kula da meye aciki ba. Tace ok.

Razia tayi boyayyaar murmushin mugunta tana satan kallonta da gefen ido,cike da kisisi na ta langwabar da wuya tana kasa kasa da murya snn ta dafo kafafun wasimen tace”Thank u very much my sis,bari to na shiga ciki inkin wanke ki shanyamin anan kawai
Wasime ta gyada kanta
Tace toh,.wani irin tafiyar yanga raxy ta dingayi cikin salo zuciyarta cike da farinciki tana tafiiya tanai ma wasime dariyar mugunta ta ciki ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button