
As usual anono bata gayama wasime inda taje ba,amma yanayinta sosai yabawa wasime akwai wani sabuwar lamarin da anono take kkrin boye mata,dai kawai ta basar.
Bayan ta kimtsa gidan tass ta shiga dakin mijinta tay masa thorough sanitation duk abubuwam da razia take amfani dashi ta kwashe tay waje dasu. Ta shimfida masa sabon bedsheet ta kunna hayaki acikin dakin..snn ta dawo ta samu anono suka samu zama da tattaunawa mai nisa.
Bakaramin kuka wasime tayi ba ayayin da take fayyace ma anono halin da ta shiga ciki ayan kwanakin nan da basu wuce wata guda ba,komi saida ta gaya mata hanklin anono yay matukar tashi ta miƙe tsaye in shock tana doka salati idanuwanta yana fidda hawaye masu rauni
Har sanda raxana da karyewan zuciyar ya saki jikinta kafun nan ta dawo cikin hayyacinta Tay sauri ta tsuguna gaban wasime dake kan kuka ta rusuna hadi da rungemeta ajikinta tsammm tana kuka tana cewa wasime kiyafe ni kiyafeni kiyafeni dana barki acikin wannan mummunan hali,wasime kiyimin aikin gafara ohh ni fatsuma naci amanan hassan da badiatu wasime kinsha bakar azaba Allah ya isa miki akan wann azzalumar mata idona idonta wallhy
Saina kakkarya kafafunta
Jikana dahiru zata tsafe?
Harnice za’a tsafe jikana ina raye Toh karyanta ko ita wacece ina gidan nan babu inda zanje harsai ta dawo ta sameni munyi gaba da gaba da ita anan ne zata san fada da aljani babu riba.Oh duniya ashe abunda yayta faruwa kenan ban sani ba?cike da jimami take furtawa yanayin ta a rikice hanklinta yay mummunan tashi tana ta shan mamakin wann lamarin ackiin zuciyarta.
Har wasime tay shiru tay calming kanta anono bata dawo cikin hayyacinta ba,karshe tagumi tay tayi zugum da hawaye masu rauni a idanunta tana lisssafin yadda rayuwa yake tafiya bisa tsarin qaddara,ta tuna ko iyayenta ma matsafiya ce tay sanadiyar shan azaban su a cikin duniya ashe abun zanen qaddarace wacce take bibiyarsu baki daya.
Sai can dayamma da sukayi wanka sukaci abinci ta nitsar da wasime tana tambayarta yadda zata hadata da malam shehu suyi magana yau da daddaren nan danji take bazata iya bari abun ya huce acikin zuciyarta batare da tasan matakin da zata dauka akan rayuwar jikanta taheer ba.
A fannin prof kuwa tun waccan lkcin datayi kwanciyar rashin lpya sabida bakincikin rabuwarta da danta tasha alwashin neman makanta mafita,tana samun saukin jikinta ita da uwar rikonta mai suna momy omatere suka kama hanyar suka je edo state wajen malamar kakarsu wanda ta kasance acikin yaren jukunawa amma a garin edon take aiyukan maluntarta,ita irin dai Alpha din nan ne masu bada taimako akan sihiri aljanu da sauransu.
Da wuya kafin suka samu ganawa da ita prof tabi ta daga hanklinta tana son sanin me ake ciki da makomar rayuwar danta shin hali ya canza koko sihirce shi akayi?
Kwana uku malama tana aiki akansaa,ta bawa prof wani ruwa tasha tace mata taje gida bayan kwana uku zata ga komi acikin mafarki..
aikuwa tun arana na biyun prof tay mafarkin razia da chidara Da wani mutum wanda ba a fayyace mata fuskan shi ba,dukkan shirinsu akan danta sai da taji ta kuma gane ma idanunwata yadda suka daure kurwan danta suna azabtar dashi suka bawa bakin aljani gadinshi suka kuma daure masa hanyar yin tunani.
Washe gari Prof tay kuka harda birgima akasa sanin cewa rayuwan danta da mutuncin sa kawai ake son ruguzawa ta fahimce cewa wnn mutumin da ba’a bayyana mata fuskanshi acikin mafarkin ba shine makasudin duk ababen dake faruwa da danta aynzu..
Da kyar uwar rikonta ta lallabata,tay mata nasiha da cewa tun farko laifinsu ne,da sukayi sake akan lamarin dansu
Bata nemi maganin kariya wa danta ba.
Kuma dama mutum mai farinjini,samun cigaba da daukaka kusan makiyin kowa ne. Wasu a fili wasu a boye,muddin Allah ya daukaka toh bazaka taÉ“a tsallake sharrin mahassada da mugayen kaba’irai ba.
Jikin prof yy sanyi tunani masu yawa suka shiga birkita mata zuciya ta dawo bata da kwanciyar hankli sammm,bayan kwana biyu suka kara komawa wajen malama neman taimako.
Duk dama sukansha wuya kafin layin ganinta ya iso kansu amma haka sukayi dauriya har ta babbasu taemako.
Yanzu haka tasaka malama ta juyar da kan danta daga sharrin duk wani madubin maita da tsafi da zaina ambatonsa shiyasa razia take shan wahala kafin ta sameshi a madubinta,Snn tasa akan a lalata namansa da kuma jininshi ya zamto mai tsananin daci wanda ko ansameshi saidai agansa abarsa a haka amma ba a isa amasa komi ba,ire iren ababen su na al’ada dai ta kakkarba magunguna wanda zata kawo wasime da dan cikinta sabida ta katange su daga sharrin mayu da matsafa,malama tace mata sha da wanka kawai wasime zata nayi na kwana bakwai toh daga nan duk sanda wani maye ko matsafi ya hada ido da ita zai canza hanya bazai iya kuma cutar da ita da yaranta ba.
Sai dan hayaki data babbasu akan gidajen su yana maganin mugaye harda barayi.
Jiya cikin dare prof ta fara aiyukanta akan danta razia shiyasa ta bayyana ma razia a mafarki danta tsorata ta.
Fannin saheeb kuwa babu wanda yasan meke faruwa dashi kwana biyun nan face abokinsa khalid,tun ranar sunday da suka rabu da razia aka fara turo masa sakonni ta wayansa masu tsoratarwa ana masa ikirarin za’a tono asirinshi dana babanshi akan abubuwan da suke aikatawa a boye.
Tun abun na wasa har abun yazo ya soma kere tinaninsa,aransa yay ta zargin razia ce dan yasan dukan da dazu da safe yay mata, daga bisani shida khalid sukayi kyakkwan bincike suka gane cewa ba razia bace wata macen ce daban wanda basu san ko waye ba.
Duk wani sirrinkan sa dana mahaifinshi ta mallaka in audio,photos nd videos wanda take tura masa haka kawai danta razana shi.
A ranar gabaki daya Saheeb ya dawo baida kwanciyar hankli komi zaiyi arazane yakeyinshi dan yasan inhar asirin shi dana iyayenshi ya tonu toh tabbas komi nasu a duniyan nan ya kare musu kenan,shiyasa kwata kwata jiyan yake yawan kashe wayarsa daga ya kunna kuma sai a kuma turomai wani sabuwar video ko hoto ko recording dinsu mai razanarwa.
Hanklinshi duk ba’a kwance ba yay shirin zuwa Abuja dan yaune zaije yaga rugujewar rayuwar taheer kafin nan ya dawo khalid abokin sa ya tabbatar masa da cewa kafin ya dawo daga abuja shi zaisa a zakwalo musu koma wacece yarinyar datake turomasa sakonni kuma daga sun kamata kasheta kawai zasu saka ayi,maganganun khalid ne ya bashi karfin gwiwa har ya shirya zuwa abuja wajen taro.
Baiko yi tunanin neman razia ba don aranshi yasan yadda take mutuwar bautawa sonshi
Tana kuma jin tsoronshi yasan by now ta kammala shirya musu komi.
Razia tana isa calabar ta samu mamanta chidara kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah an sankame mata wuya da dinki,.ranar taci kuka ta gode ma Allah fushi ya kamata ta fidda madubi ta kwalla ma taheer kira kafin ma ya fito saida tasha wuya,yana fitowa sai taga ya juya mata baya .tayi tayi ya juyo ya kalleta ta umarce shi amma sai shiru daga bisani ba sai kawai ya dauke cak..hanklinsu a matukar tashe chidara tace mata tay marmaza taje wajen seven sisters goddesses ta gaya musu tana bukatar madubinsu na dacan wanda za’a iya amfani dashi sau uku arana…
Babu shiri razia ta bazama gidan tsafinsu dan secret cults ne so sunayin meetings dinsu da rana a wani hamshakin gida na alfarma da suke gudanar da taron tsafinsu aciki
Inde darene sai aje asalin cikin daji.