FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wasime batace komi ba ta sauko akan gadon ta kimtsa kanta snn suka karya da shayi da chips da miyan kwai,bayan sun kammala ta fito raka anono zuwa bakin gate anan ma cin karo sukayi da malam jafaru da malam shehu sunayi ma juna sallama akan cewa shima yanxun nan yake shirin zai wuce ya koma kauyensu domin ya gama aiyukansa anan kenan.

Alheri sosai wasime tay ma malam shehu,ta bashi kudi da wasu kyautauka domin ya kaiwa iyalinshi,sosai innono tay masa godiya akan taimakonsu da yayi nan da nan sukayi ma juna bankwana tare da shi da anono suka wuce tasha snn wasime ta dawo cikin gida.

A fanin razia kuwa tunda ta farka a gadon asibiti jiya tsakar dare maman ta ta gaya mata yadda sukayi da saheeb,tsoro ne ya gumeta jikinta na ɓari ta kasa samun nitsuwa bare sukuni,nan tahau shiri tay marmaza akan zata koma kaduna state da sassafen nan tun kafin saheeb ya dawo yau yasan bata garin kaduna,nan da nan ta debo kayanta da sabuwar madubinta na jiya wanda dashi zata kira taheer dashi da daddaren nan wajen dinner su cimma burinsu.

Ahaka ma tasan bata tsira ba gashi bataso wani abunda zai shiga tsakaninta da saheeb dinta,tasan yay fushi sosai da tay missing wnn babban oppurtunityn na ta jiya,sanin kanta ne saheeb ya dora buri wa wann ranar,dukan su Sunso da ‘ace a bainar dumbin manyan sojoji da shuwagabannin kasa da suka halarci taron nan suka kunyatar dashi suka kuma karar da duk wani darajar kwalin karatunsa.

Jiya cikin dare ta debo hanya jirgin medview ya iso da ita kaduna around 3am midnight,hotel ta kama ta zauna zuwa safiya dan haryanzu bata jin dadin jikinta,a hankli ma take saka kafafunta a kasa tana takawa saboda zugi da zafin dinki da akayi ma kasarta wanda har iyanzu bai warke ba.

Yau da safe bayan Wasime ta raka anonon kenan tana shigewa cikin dakinta ko minti goma batay ba saiga razia ta dawo cikin gidan,ganin ko ina shiru ta wuce direct ta nufi master bedroom din taheer tana murda kofar site dinsa tajishi a kargeme da keys babu halin budewa dan tafiyar gaggawa tayi ranar bata dauke komi nashi ba.

Bayan tafiyarta da wasime ta tsaftace gidan tabi ta kwashe duk wani abubuwa na mijinta takai dakinta including all the spare keys na ko ina a gidan komi yanzu yana hannunta ne.

Tsaki razia taja can ta wuce kofar dakin wasimen ta tsaya ta dinga bugawa tana ce mata ta fito ta bata keys ta dawo,wasime naji tay shiru ta ba banza ajiyanta dan ayanzu bata jin zata iya ragar ma razia koda na miskala zarratin,ahaka ma danne zuciyarta takeyi tana so ne ta walakanta razia da hannunta kafun nan tasan ta huce takaicinta, har razia ta kammala buge bugenta ta hkra ta bar kofar dakin wasime bata san ma tanayi ba.

A bakin kofar dakinshi tabar duk wani kayanta da jakarta ta wuce restaurant da dan karamin purse dinta domin siyan abincin dazataci da safan nan.

Tana ficewa wasime ta bude kofar dakinta ta dan leƙo waje,ganin babu kowa awajen yasata isowa kan kayan razia data bari a bakin kofa,
nan ta tsuguna ta bubbudesu ta bincika sosai har saida ta zagwalo wann madubin tsafin dama kuma malam shehu ya gaya musu komi akan madubin.

A gefe ta ajiyeshi ta maida mata kayanta tsaf kamar ba a taÉ“a su ba ta bude kofar quest room tabarshi a bude ta wuce dakinta tana cewa “watan cin uban wata ya kama a gidan nan”.

A fannin saheeb kuwa da kyar ma yau ya farka a bacci sabida yawan giyan dayasha jiya da daddare na bakin cikin Abubuwan cigaba da daukaka daya faru da taheer wanda baiso hakan aranshi ba,duk inda ya ratsa da kunnensa jiya hirar taheer kawai akeyi musammn akan international appoitnment din nan nasa,snn ko ana hirarsa bazai taɓa jin an zageshi ba,saidai ayi admiring dinshi evrywhere Doc tej, doc tej,abun duk yabi ya isheshi babu hali ya kunna tv yasan zai iya ganin hidimar a news, ko wayar sa Sabida baison ma wani ya kirashi abata masa ransa da zancen.

Yana yin wanka baiko yi sallah ba yaci abinci sama sama ya wuce zonal office ya tada rikici yace sam bazai karbi certificate of honours dinshi a office ba,yadda aka bawa kowa a bainar jama’a shima haka yake so yau in anje dinner a kirasa bainar jama’a a bashi abunsa.

Superior din wajen basu wani kulashi ba sabida sun san da political powern ubanshi kawai yake nuna gadara da takama,harya bar wajen basu ce mai eh ko a’a ba,amma a zuciyansa yasan dolene ayi masa hakan.fitarsa wajen keda wuya ya kunna wayarsa domin kiran khalid yana so yaji labarin abunda yake gudana game da case din mai turo masa saÆ™o,To his surprise sai yaji Dukkan layukan khalid din a kashe,which is highly impossible dan khalid bai taÉ“a kashe wayarsa haka kawai ba.

Ya dau lokaci yana neman sa bai sameshi,ya kikkira bad boys gang dinsu ya tambaya suma sukace basu ga khalid ba,yana kan kire kiren sai ga kiran mahaifiyar khalid din ta kirashi hanklinta a tashe tana tambayarsa ko suna tare ne dan tun jiya daya fice a gidan ba a ga dawowar sa ba,inban da security dayace yagansa da wata mace sun wuce acikin wata mota bawanda ya bada wani bayani akan bacewarsan.

Saheeb yace shima nemansa yakei sabida shi yana Abuja ne bai dawo kaduna ba tukuna..

Bayan sun kammala wayar yafarajin kanshi very uncomfortable da batar khalid din,but jin ance da mace ya fita saiya soma tunanin ko yawon iskancin shi kawai yaje amma its very unusual of him ya kashe wayarsa abun dai da mamaki.

A fannin Taheer kuwa tun kafin safiyar yau ta washe hanklinshi ta dawo jikinshi fiye da yadda yay zato duk dama yana kan jin kanshi a rude,yanayinshi kamar wani bataccen daya samo kanshi awani duniya ta daban,tun asuba da yake karatun qur’anin mahaifiyarshi ne tadinga fado masa acikin ranshi,saiyaji ya kasa samun nitsuwa.Yanajin kamar fuskanta kawai yake so ya gani.

Dayay wanka ya shirya ya fara neman lambar Wayarta luckily enough sai uwar rikonta ne ta daukali wayar sukayi magana ta gaya masa cewa mamanshi tana nan a okene.

Shide yasan sun samu tsabani da mahaifiyarshi, kuma yay mata laifi mai muni amma baisan akan meye bane kuma bazai iya tunoda abunda ya hadasu ko ya haddasa shi yay mata hakan ba.

Yayi ta tinani ko zai tuno amma ya kasa,8ck na safe yay wanka ya shirya kansa cikin all black suits dinshi,baiko tsaya karyawa ba ya kulle room din lodge dinsa ya nufi filin jirgi aka kaishi kogi state,around 10 am sai gashinan a cikin garin okene.

Baima san location din gidansun ba,half grand ma dinsan ya kira yace mata gashi nan yazo okene,bakaramin mamaki hakan ya bata ba dan awaya bai sanar da ita cewa zaizo yau ba,batay wata wata ba ta aiko da mota akaje aka dauko sa aka kawo sa gidansu.

Tin shigowarsu yake ta kalle kallen wajen dan rabonshi da nan tun yana dan yaro karami,sai yaga komi ya canja masa thy are still living a middle class life dinsu babu wani rayuwar karya.

Tun kafin isowarsa gidan momy omatere ta gaya ma prof cewa danta yana hanyar zuwa gareta.

Prof tayi expressing shock dinta tana hawaye sai batace komi ba ta shiga daki ta zauna tsawon mintina acikin jimami da tuni dukkan abubuwan da suka faffaru.

Ita ayanzu batashi ma take ba,so take taje gida ta duba lpyar yarinyar nan wasime..god knws what she did was unfair to her inlaw,..amma ta bar hakan ne a matsayin jarabawarta da kuma sakayya Akan abubuwan dataso tay ma wasime akan danta da can baya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button