
Tafi awa biyu a gidan tana zagaye sai can data lura da kofar guest room ta ja tsaki ta wuce da kayan ta wajen ta zauna
Aciki tana jin haushin rashin bude kofa da wasime batayi ba kuma tasan tana cikin dakin tanajinta.
Wanka tay ta saka figigyar riga rabin cinyarta,gashi ta kashe wayarta domin bata son saheeb ya kirata harsai dare yay ta kammala cikamai burinshi akan taheer kafin nan suyi magana.
Wanka tay kafin nan tazo ta kwanta tay bacci bayan la’a sar ta farka ta fito falo jikinta sanye da wnn figgiyar matsatsun kayan sauri take jin daddan qamshin girkin wasime aranta taja tsaki tace kenan matsiyaciyar ta gaji ta fito.tana saukowa kuwa taga babu kowa sai hadadden plantain chips da noodles dayaji kifi an aje chilled orange juice a glass cup a gefenshi ga cutleries ga komi.
Atake razia tafarajin wani maiyataccen kwadayi marar linzami na neman janta izuwa kan abincin
Duk iya daurewa ta hana kanta zuwa tay amma kwadayin datakeji bazai barta ba.
Kan abincin tay wuf ta saka hannu ta waawushi plaintain takai bakinta sanda taci kusan rabi dadin na debarta snn ta dauki juice din shima ta kwankwade.
Jim kadan tanakan ci sai ga wasime ta fito suna hade ido razy ta saka fuska irin ko ajikintan nan ta cigaba da cin abincin…wasime tana tsaye tana binta da matsiyacin kallo basuce wa juna komai saida razi ta gama cinyewa tass kafun wasime ta karaso gabanta tana watsa mata harara tana cewa harkin cinye ko? Cike da rashin fahimta da masifan karfin hali razy ta tsime tace”Eh na cinye din,yo inbanda iskanci kinaji ina buga miki kofa zaki kama kiyimin shiru,ni sa’arki ce,ni kiban keys dina zan koma dakin mijina i cant stay in d guest room,wats all dis?wato dan ina sake miki fuska shine zaki nemi ki raina ni ko?
Wasime tay rolling idanu cikin katseta tare da sakin wata tsiririyar dariyar mugunta tay tsaki batace mata uffan ba kawai ta barta awajen ta nufi dakinta tana jiran lokacin cin uban razy yay,cinye abincin datay bakaramin dadi yay mata,dan malam shehu da ya bata maganin yace maganin bazai fara aiki nan take ba sai yay kamar awa guda ajikin razia.
Kwanciyarta tay akan gadonta bata ko kulle kofarta ba tabarshi a bude tanata murmushin jiran lokaci yay,.
batayi mintina goma ahaka ba saiga raziar ta shigo,hannu rike da kugu fuskrta dauÆ™e da tarin damuwa,tace ke wasime dana fita a gidan nan waye ya taba min kayana?..wasime tanaji tay banza da ita har saida ta harzuÆ™a ta kara maimaita mata tambayan,cike da jan aji da batsewa cikin yauÆ™i mai kularwa wasime ta amsa maganan batare da tajuya ta kalleta ba, da gatse muryanta ciki ciki tace “oho”.taja bakinta tay shiru,”hankli tashe razia tace Kamar yaya zakicemin oho?nifa ba wasa nake miki anje an dauka min abuna acikin jaka a daki naga dai ke kadaine acikin gidan nan.
Mikewa zaune wasime tay fuskanta a harde tace
“Yo ni na dauke miki abunkin kenan kome ?
Anty razy bana son renin wayo kinga dazu haka kika cinyemin abincina bance miki komi ba haka kawai zaki shigo har dakina kina laka min sata?tsawon zamanki gidan nan yaushe kika taba cewa abunki ya bata?kije kicigaba da dubawa mana..Karkiga inai miki shiru shiru inhar rainin wayo zai shigo cikin zancen nan bazan dauka ba fa..ta karashe hadi da jan tsaki.
Tsaki razia taja mai tsayi ta juya ta fice fuuuh a dakin batare da tace komi ba. Tabbas tasan wasime bazatayi gigin taba mata kayanta ba but she is sure madubin nan ta saka shi acikin jakarta ta san babu yadda za’ayi ace ta manceshi a wani waje ko ya fadi..
Tafi minti talatin tana neman mirror nan hanklinta a matukar tashe,can ta kira mamanta ta dada tabbatar mata da cewa ta taho dashi kaduna.
Daddaya razia tay ma kayanta batagani ba ta soma ziriya ita kadanta adakin tana jeka ka dawo
Cikin matsanacin tashi hankli,..can ta debo jiki ta dawo dakin wasime ta sameta daf ta daura towel kenan zata nufi wajen wanka.
Take ta sauya yanayin fusknta ya dawo na abun tausayi,jikin ta harna rawa ta karaso wajen da wasime ta ke tsaye cikin saukar da murya tace sister dan Allah kiyi hkuri
Mana,i knw ur angry dan naci abinciki am sorry i was just worried wallh abuna da yabatan nan yanada matukar muhimmcin shiyasa nake tambayarki ko kinga wanda ya shigo i mean dakike nan bakiji motsin kowa a gidan nan ba?ko me gadinku ma bai shigo ba?
Wasime ta yatsina fuska tace ni bansani ba,waima meye ne abunkin dakike nema ko baida suna ne?
Razia tace no no basai kin san sunan ba,just inkiga abun da banaki ba kibani dan Allah im really in need of it.. ganin wasime ta shareta ta wuce bayi saita fita taje dakinta ta cigaba da duba.
After like one hr cikinta ya fara mata tsinannen ciwo take zufa ya rufeta ta fado kasa tana murkusu tanajin kamar wuta aka kunna mata acikin yanacin hanjinta.
Wayyo Allah na ..ta danna kururuwa mai matsanacin kara.
Tana ta ihu cikin matsanacin azaba saida kururwan ta na neman taimako ya karade gidan tasssss wasime tana zaune agaban mirror ta gama kwalliyarta ta saka riga da wando tayi kyau ta bude drwer ta dauki zukekiyar dorinanta data karbi aro wajen malam jafaru mai gadi wanda tay kwanan mangyada jikinta yay tauri.
Dashi ta fito ta nufi dakin razi da madubin a aljihun wandonta
Tana banke kofar ta ga razia a kasa tana murkususu kamar zata mutu tana ihu tana fiffincike suman kanta kamar ana ƙonata da wuta.
Wasime ta tsaya akanta tanabinta da wani irin matsiyacin kallo
“Sister ki taimakeni kikaini asibiti im burning kamar wuta nakejin zafi acikina wayyo Allah na na shiga uku na lalace
Haushi ya kama wasime ganin wai tana mika mata hannu,nan ta daga bulalan dorinanta sama ta zuga mata akan cinyarta Zafi akan zafi yasa razia sake wata kangarriyar kara.
A zuciye wasime take faudeta da dorina ta ko ta ina ajikinta take kai mata duka babu ruwanta da inda dukar zai sauƙa tace dan ubanki harke kin isa ki shigo min gidana kina kiran mijina naki?karuwa kazama irinki watan cin ubanki ne ya kama abincina da kikaci shine azabanki na farko da zan gana maki,kisan kuwa wuta kikaci ma cikinki da kuma fansar duk abincin danake girkawa kinaci..
Azaba kuma yanzu zaki soma gani,razia ta fice a hayyacinta dan sosai wutar ya ke konata acikinta tanata ihu a gigigce babu bakin maida magana ko mikewa tsaye.
Tanaji tana gani wasime tay mata tsinannen dukan tsiya hannun ta da fuskan ta zuwa wuya da bayanta sun faffashe sun kumbura,tana fidda numfashi kadan kadan sann wasime ta ciro mirrorn ta kawo dede fuskarta tace inhar kinaso wutar nan ya dena ci ajikinki ki umarce kanki yanzun nan so nake ki dawo baiwata kamar yadda kika maidani baiwarki acikin gidana…
Baki na bari cikin rasa nayi razia ta aikata hakan..tana jiran wasime ta bata maganin da zai cireta cikin azaban amma sai shiru.
Fita tay taje ta debo wankin manyan manyan duvets da kayan sanyi masu dan karan nauyi ta saka ta agaba har backyard ta jibga mata su razia taci wanki ranan har karfe shida na yamma bata gama ba sabida azaba kala kala dake ci ajikinta tanajin kanta kamar acikin wuta.
Bayan sallan magrib wasime tazo ta zaneta tace bata yin aikinta da sauri lokci guda razy ta dawo abar tausayi idanunta ya kumbura suntum karshe awajen ta fadi tayi dogon suma Wasime taja tsaki ta tafi ta barta,can around 7.50pm ta nemi igiya ta daure hannunta da kafafunta ta kulleta awajen snn taje ta dauko madubin ta zauna tana jiran lokacin zuwa wajen dinnersu saheeb yay