FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gaban razia take ya buga dum dum ta bata shiru awajen ta kasa cewa komi….

Hakan baisaka wasime ta ragar mata ba,tanaji tana gani taher ya dawo daga tafiyarsa baima ganeta ba yana tambayr wasimen wacece ita?

Bata gaya masa komi ba saida yaci abinci ya huta snn ta kira raziar tazo ta fayyace masa labarin komi da bakinta yaji..

Taheer yayita shan mamaki kanshi ya kulle sosai da kyar wasime ta dada fahimtar dashi komi.

Kwanan razia biyu a gidan suna gana mata azaba dan kuwa razia taga bakar rashin mutunci awajen taheer
Saida tay nadamar fara taka kafartta cikin gidanshi tay wasa da aurenshi da mutuncin shi,saida razia ta dawo abun tausayi kafin taheer ya dauketa yakaita ga hukuma ya basu madubi ita kuma aka kulleta.

A fannin saheeb kuwa saiyau ya same dawowa cikin hanklinsa.

Hanklin iyayensa atashe ganin babu abinda yakeyi sai kuka,da kyar aka masa alluran bacci ya samu bacci bayan kamar awa guda ya farka ya dauki wayarsa ya kunna da zimman kirar razia danya dau mummunan fansa,yana bude wayar saiyaga wani saƙo na yawo akan screen din wayarsa,bayan ya karanta sakon a firgice ya tashi ya kimsa kanshi batare da kowa ya sani ba ya dauki mota yabi location din da aka rubuta masa cikin gaggawa.

Wajen na da nisa sosai canta wajen garine inda babu mutane sosai sai jeji.

A sakon an rubuta masa kamar abokinshi khalid ne yake neman taimakon sa yanzu.

Yana isa wajen yay parking motarsaa ajeji yay neman duniyan nan baiga khalid ba,da kyar dai ya hakura ya dawo tun akan hanya ake turo masa sakonni da cewa asirinsa dana iyayensa yau zai tono a matsayin fansar abunda sukayi da rayuwar yarta.

Kan saheeb yay mugun kullewa ya rasa to waye wann? Wata yarta?tsaki yaja Yay dialling lambar sai shiru ya kira razia ma sai shiru.

Hanklin iyayensa ya tashi sosai da suka dawo dakin sa basu gansa ba.

Saheeb yana shigowa gidansu saiga motocin Dss abayansa yana shiga suna shiga nan yane suka tsaresa da bindigogi iyayensa da kowa aka firfito waje,ogansu yace yanxun nan aka tura musu sakon cewa saheeb ya dauko gawar wani mutum daya kashe a jeji a bayan motansa .

Zuciyan saheeb kamar zai fashe dan tsoro,haka aka bude booth dinsa kuwa saiga freshly murdered gawan abokinshi khalid an masa yankan rago.

Take saheeb ya yanke jiki ya fadi,aka kai case din dss office akahau bincike wani mutum ne manomi wanda da basusan daga ina ya fito ba ya bada cikakken shedar cewa yaga saheeb alokcin dayake saka gawar a booth dinshi.aka razana saheeb aka tambayeshi yace ehhh yaje wajen amma shi baiga khalid ba bare ya kasheshi,haka kowa yaki yarda dashi sabida yaki fadin asalib dalilinsa na zuwa jejin dadin karawa bai gayawa iyayensa ana threathning dinsa ba.

Case yay case aka kulle saheeb aka kawo masa lawyer nan ne yake bawa iyayensa labarin threath din dayake samu har suka fahimce cewa mutuwar khalid dinma sharri aka laka masa.

Hanklin mahaifinshi yafi na kowa tashi sabida zabe yay kusa kuma yaga dukkan shaidojin da mai musu barazanar ta tanada akansa masu qarfine nan da nan ya baza men dinsa aka shiga neman koma wacece mai tura sakon domin ya gana mata azaba snn ya kasheta.

Haka sukayi bulayin su Basuci nasara ba ranan washe gari tunda sassafe iyayen saheeb suka soma ganin bala’i kala kala na taso musu.

Maiyin musu barazanar ta bar saheeb ta dawo kansu gadan gadan tana turo musu sakonni masu razanarwa. ga mahaifin khalid ma daya birkice yace wallh bai yarda ba saidai akai case din mutuwar dansa har kotu ayi sharia…

kafin yamman ranan yay dukkan wasu sirrikan iyayen saheeb ya bayyana lokci guda komi ya rincabe musu aka kamasu suma aka kullesu anakan bincike kala kala akansu.

Hakama razia ta toni asirin mahaifiyarta aka daukota daga calabar aka kullesu suma anata bincike akansu.

Ata fannin su wasime kuwa sabuwar soyayya mai dadi da tsafta suke nunawa juna,duk dama a kullum sai taheer ya nemi gafararta ya kuma faranta mata rai da abubuwan da batay zato bama.

Lokaci guda shakuwansu ya dawo harya so yafi na dacan,bayan sati guda da faruwar komi saiga su innono da iyayen wasime sunzo dukansu garin kaduna,a gidan prof suka sauka kafin nan innono ta sanar da taheer komi shikansa ya girgiza da jin labarin wai iyayen wasime suna raye kuma har sunzo kaduna.

Bai iya gaya mata ba dan baisan ya zata dauke maganan ba wanka sukayi suka shirya sukaje gida duk ta dauka wajen prof kawai zai kaita su gaisa suga juna ,suna isa aka sada ta da iyayenta wasime saida tay suman wucen gadi snn ta dawo hayyacinta taji labarin duk abunda ya afku.

Ga iyayen nata kamar zasu cinyeta tsabar murnan da sukeyi na ganinta,haka kowa yaja jiki yabarta dasu a lokaci guda wasime taji tana matukar kaunarsu..

Haka sam sukaki barinsu su koma garin da suka fito kullum wasime da taheer sukanzo gidan prof donsu gana da iyayenta Fahimtar juna da soyayya mai tsafta ne ke gudana acikin gidan ayayin da aka kara kulla danƙon zumunci mai tattare da aminci da girmamawa.

Momy oma itama ta amince cewa zata dawo nan tana zama da prof dan kartay rayuwanta ita kadai,tunda anono bawani zama takeyi ba.

After one month…

Haka rayuwansu ta kasance mai dadi da tsafta saidai ata fannin su saheeb da razia case ne yake dada zafafa ana dada bincike akansu ana samun manya manyan hujjoji lokaci guda komi na iyayensa ya ruguje kusan kullum sai anyi breaking news da labarin mahaifinshi case yazo har aka fara binciko silar mutuwar mahaifin taheer
Wanda shima cunen cikakken shaida aka turo ma hukuma wanda ake zargin boyayyir mai musu barazanan ce ta turo.

Razia ta rame ta kwanjame ta fita a hayyacinta hakama mahaifyarta duk sun galabaice.

Ata nan fannin kuwa lokacin cikin wasime ya shiga watansa na biyar kenan,ranar da iyayenta suka shirya zasu koma taheer yay musu albishir da sabon gida a abuja ya hada musu harda kyautar mota.

Kowa yay farinciki sukabi suka rakasu har Abujan sukayi musu kwana biyu..

Daga dawowarsu ne aka nemi ganinsu a dss office domin a bude sabon sharia tsakaninsu da familyn saheeb da ake da tabbacin su suka hallaka mahaifinshi.

Nanma prof ta tuma tace bata iyaji ba,dole ne asamar ma mijinta justice tsanan saheeb datayi akan abunda yayi ma danta taheer sai ya ninku yay tsanani jin ance mahaifinsa ne ma ya kashe mata miji hakama anono tace sam bata iyaji ba sede aje dik inda za’aje..

Haka aka dinga case ana fafatawa abun harya kawoma zuwansu kotu

Babu shiri babu tsammani case yay mugun daci ma mahaifin saheeb,inda kaf wani boyayyar asirinsa saida suka tonu..aka zo kan saheeb ma babu sauki saheeb yaso yace ma kotu cewa shi baisan razia ba don haryau yana suspecting hala tasan me turo masa sakonnin barazanar,yanata kkrin daura mata lafin komi,mahaifyar Razia dataga abun nasa yay yawa saita ta tona asirin komi da duk yadda suka kulla shirinsu akan taheer dan ta wanke yarta daga sharrin dayake so yalaka mata.

Tasan muddin tabarshi yasa aka maida case din mutuwar khalid kan razia toh babu shakka tasan kashe mata yarta itama za’ayi.

Case bai wani ja ba sabida tonon asiri da shaidoji masu karfi da aka dinga tonowa akansu by the unknwn sender. Bayn shaida ma takan turo har da witnesses wasu politicians dinma tursasu tayi sukazo kotun suka fadi gaskiya akan mahaifin saheeb.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button