FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani daka tsalle tayi cikin murna tace haba?
Kace Allah zan ganta?
Dariya yay sosai snn yace eh mana amma ai sai bilti ta amince…dan shiru tay tana mai satar kallon biltin da gefen idanunta,gani tay kamar bilti ta hade fuska.

Gaba daya zuciyar bilti bai wani kwanta da abun ba amma dai zata kyalesu din suje kawai da sharadin saheeb zai cika alkwarin sa na dawowa da ita akan kari.

Tunda ta basu go ahead dukansu suke cikin halin murna at arnd 3 na yamma saiga saheeb ya shigo,yau half jumfa yasaka ajikinshi ta masa cas cas dake bugun kamfani ce ya sako hularsa mai shegen tsada. Riga da zani na leshi wasime ta saka sky blue in colour shima duk acikin sabbin dinkunan da akayi mata ne,saheeb yana isowa tay gudu taje ta hau jikinshi tanai mai oyoyo.Duk dama yau bataga wani sakewar fuska awajen bilti ba

Da zasu fita bilti ta kirawo saheeb gefe
“Dan Allah karku dade dayuwar taheer ya dawo yau kuma kasan dai bazaiji dadi ba inyazo ya tarar da cewa bata nan.

Cike da assuring dinta yace insha Allahu zan cika alkwari.

40min drive yakaisu makaken gidan su saheeb ko ina a shirye yake tsaf da kawatattun decorations wanda akayi su musamman don shagalin partyn,kusan rudewa wasime tayi ganin wnn gidan ma yafi wancan wanda sukaje shekaran jiya girma Surutu kam yau yashata harsaida yaji babu dadi.

Everything went well,saidai plan din saheeb na bayyana wasime ma mahaifyarsa bai samu yay aiki akan tsarinsa ba..

muhimman baki ne suka tsareta a babban falon gidansu cikin wata muhimmiyar zantawa ta kasuwanci.,tunda aka yanka cake da ita suka dan daddauki hoto shikenan bata ƙara samun daman lekowa wajen ba,su wasimé kam tuni ta saje cikin yan uwanta yara,saidai kaf cikinsu itace tay daban sabida yanayin suturarsu yasha bambam da nata.

Kusan kowani yaro awajen dan masu shine kuma ancan caÉ—a ma kowannen su kwalliya da hadaddun ready made gowns nd expensive suits, amma ita kam riga da zani nema ajikinta wanda a kiyasce kudin leshin bazaifi dubu takwas ba.

While da party is going on kowa yanata enjoying kanshi da abinci kala kala ana rawa ana games amma gaba daya hklin saheeb baya jikinshi,baida wani abunyi a zcyarshi face sake sake,And zee was there to annoy him more, dan tunda taga zuwansa wajen tareda wasime take famar tsine masa albarka duk inda ya zauna haka zata bishi ta nanike mishi Snn bata da wani magana mai armashi sai Aibata alakarsa da wasime.

Aranta ta tsane Duk wani abunda ya shafe taheer.
Ayanzu sosai take nuna adawarta da shi.

Da abun ya ishe sa ne yay zciya ya tashi yabar mata wajen yabarta a zaune ita kadai akan table a tsakiyar idanun mutane, Hakan dayay sosai ya bata haushi,aftr like 2 mint tana kkrin latsa wayarta zata turawa kawarta eesha text messg caraf sai idanunta suka sauka akan wasime.

Tun daga can ta zuba mata ido tanamai hararata, wucewar ta ta gani ta hanyar guest washroom tana doka uban sauri,mammtase kafafunta datakeyi ya nuna alaman fitsari ne ya matseta.

Wani Dariyar mugunta zee tay snn ta tashi tsaye a gaggauce cikin satar idon mutane tabi bayanta washroom din

ahnkli take lekawa cikin sanda a Lokacin data shigo lkcin har wasime ta kammala yin tsarki tana kkrin maida panties dinta bata hankara ba taji an wani fincikota tayi baya,wani irin bugawa da karfi kirjinta yay acikin yanayin firgita da tsoro har ta karkace baki zata saki ihu Da Æ™arfi zee ta buge bakinta sanda jini ya tsittu..,bata jira ba ta fixgo ta ta cakume mata wuya ta shaketa sosai tanamai hadeta da jikin bango”

tuni hancin cikin wasime ya cure, cikin nata ya duro ruwa tanajin kamar zata saki fitsari ajikinta
,”ihu tayi niyyar sakawa…zee din ta zare mata ido tare da daka mata tsawa “kiyimin shiru da bakinki,kikq yadda kikayi ihu anan saina kasheki,mayya kawai shahsha yau saina kasheki,in kashe banza.

Kukan bazata wasimevta barke dashi wani mari zee ta dora mata snn ta turata ta fada akasan toilet din cikin ruwan datti,karkar jikin wasime yake rawa jin kanta kamar wata mutacciya

Kuka takeyi mai tsananin nuna firgita saidai marar sauti sabida toshe bakinta da zee din tayi..”wato ke bakiji ko?Uban wa yace miki kizo nan…uban wayace miki kinabin saurayina?zare mata ido take kamar zata hadiyeta cikin masifa

Da baya baya wasime takejan kanta hawaye sungama wanke mata fuskanta tana famar girgiza kanta alaman ta balain jijjiga da tsoro.

Toh Daga yau saiyau
NaÆ™ara ganin ki a inda saheeb yake saina yanka ki…saina hallakaki kin bar duniya.. kina ji ko bakiji?Wasime Bata iya daurewa ba ta saki kuka mai firgitarwa.Au baxaki yi min shiru ba munafuka?Janta tayi akasa tanamai wurgi da ita..ajijjiya take ya soma rufewa wasime ido,cikin kokawa da numfashinta ta soma cewa cikin kuka”..anty anty anty dan Allah dan Annabi kiyi hkri bazan Æ™ara ba waayyo Allah na kasheni zakiyi anty? kallo daya kay ma wasime zaka tabbatar da cewa bata cikin hayyacinta dan bakaramin raxana tayi ba

Haka zee ta bushe idonta ta cakumo ta kamar yar tsana ta mikar da ita tsaye tana kallonta babu ko digon tausayawa a idanunta taja tsaki mtsww”bangama dake ba”..wani janta tay izuwa bakin water flush system suna kaiwa wajen ta danna kanta acikin bututun kashi ta murda flush ruwa ya rinka zuba akan fuskar wasime yana suffocating dinta,numfashinta ta dinga jaaaa da Æ™arfi tanajin kamar ranta zai fice ajikinta,yarinya sai bari take tana tsananta kuka mai ban tausayi amma zee bataji kamar zata dena muguntar ta ba.

Daga waje kuwa saheeb ne yaketa neman ta bai ganta ba,duk saiyaji hanklnsa ya tashi sabida biyar da rabi ya gauce yana matukar son ya maishe ta gida kamar yadda yay ma bilti alkwari…

Da kyar wani basira tazo masa ya fara bibiyar yara yaran yana tuhumarsu ko sunganta daya daga cikin kannen zee din ne ya ce masa ai yaganta dazu tabi nan..sai ya masa nuni da hnyar washroom.
Cikin gaggawa ya doshi wajen,yana shiga kuwa yasoma tuamali da ihun wasime,a guje ya isa kofar inda ihun yake tashi yana bankadewa daidai lokacin zee ta cakka kan wasimen acikin latrine ta danna mata ruwan flush akanta data wani fixgo ta sai gani tayi Yarinya ta sanÉ—are bata numfashi,……
Na kudine 300 naira,subcribe via
0152983148
Mohd sule surayya
Gtb send ur evidence to
08060712446.
7/25/22, 19:19 – Kawata: FITAR RANA 16

Da wani irin zafin nama saheeb ya karaso wajen Jikinshi har na rawa ya saka hannu ya finciko wasime a hannun zee snn ya juya yanamai dora ma fuskan zee din wani gawurtaccen mari mai saurin rikitar da kwakwala..

tattaba fuskan wasimen ya shigayi ganin batako motsi hanklinsa tashe ya runtse idanuwansa snn ya bude, yana cewa”oh my gosh,zainab What did u do?..tsawa mai cike da kufula ya daka mata,kuka zee ta fashe dashi snn ta koma gefe ta rakubu da jikib bango sosai tay narai narai da idanunta Cikinta duk ya gama durar ruwa a tunaninta mutuwa ma wasimen tayi.

Tattaba fuskan wasimen ya rinka yi hanklinsa a mugun tashe jikinshi gaba daya na rawa duk ya rude yabi ya rasa ta inane ma zai fara tunkarar abun,shimfidar da wasimen yay a kasa yana kkrin tabbatar makansa cewa ba mutuwa tay ba,wayarsa ya lalubo daga cikin aljihun wandonsa snn ya danna kirar gaggawa ma emergency,Acikin yanayin raxana sosai zee ta matsa kusa da su jikinta na rawa sosai

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button