
Bilti kuwa tunda ta shige kitchen take dannawa saheeb ƙira amma bai daga ba,gabaki daya saitaji hanklinta bai kwanta ba. ranta sai ya soma harzuka,bacin rai na neman ya rufe mata ido, acikn zcyarta tana cewa yaya yaron nan zaimin haka..toh ga taheer dinma ya dawo niyanzu mezanje masa gameda fitar wasime? Duk fargabanta kada Allah yasa su shigo su iske shi a falon.
Harta kammala hada masa abincin saheeb bai daga wayar ba.haka ta basar da lamarin ta danne fushinta ta fito fuska ba yabo ba fallasa ta kawo mishi abincin acikin yanayin dubara tace “inkai maka dakinka ko inaga can dinma ai zaifi..Nan wajen duk yay kura bari inzo indan goge
Kai saika shiga daki karna takuraka
duk salon wayon waidan ta koreshi ne ya shige room dinsa karyaga shigowarsu wasime cos at any moment tana tsammanin jin sallamar su…
Haka taheer yay taurin kai shima yaki tafiya dakin duk wayonta baihau kansa ba..
Yace kibarshi anan kawai bilti”Ni anan kawai zanci”
Bilti bata taÉ“a kasancewa a halin baraxana da razana irin na yau ba sai cizan yatsa takeyi a zucyarta tana mita “kassh amma yaron nan baimun adalci ba…ziriya takeyi ita kadanta a kitchen da waya a hannunta tana mai dada neman layin saheeb din
Taheer nadaga falo yanacin abincinsa hanklinsa kwance.
Duk A tunaninsa wasime tana can daki a kumshe kamar dai yadda ta saba.
Bilti ta kira saheeb yafi sau hamsin amma shiru bai daga wayar ba,kowani dakikanin wucewar scnds na agogo saita kirga
Hanklinta bakaramin tashi yake dadayi ba
Musamman dataga har an kusa a kammala sallahn isha i bai daga kiraba kuma basu dawo ba…
Wani zucyar nata tunzirata akan taje kawai ta gayama taheer komi iyakaci ne yay fushi ai ba dukanta zaiyi ba.
But dat isnt fair to him
Matarsa ce fa wasime, nd she rmbr how he gave
her Strict oders akan kar abarta tafuta taje koina face inshi ne ya bada izinin yin haka.
Ganin takwas yay har yana shirin gaucewa yasaka bilti ta cire ranta da tsumayin fushi da bacin rai ayanayinta
Fitowa tay jikinta a mugun sanyaye da niyyar kawai zata fallasawa taheer abunda ake ciki,tana isa falon ta samu taheer din bayanan da alaman sallahn ishai yaje gabatarwa a masjid.
Kwanukan dayaci abincin ta tattara takai cikin kitchen ta zuzzuba su a sink ayayinda wani tukukin ajiyan zuciya ya kufce mata..wanke wanke ta hauyi kodama zai gushar mata da tashin hanklin datake ciki amma ina abun saima karuwa yakeyi acikin zcyarta..tambayar kanta takeyi “meyasa saheeb zai mata haka?
Kallon agogo tayi taga
Har karfe takwas da rabi shaura Wayarta ta kama ta kashe ranta a mugun bace snn ta fito da niyyar dauƙo hijabinta zata je har gidan su saheeb din kawai dakanta.
Agaggauce ta haura sama ta sauko cikin shigarta na doguwar hijabi dark green in colour duk fargabanta kar Allah yasa ta gamu da taheer,ai gwara taje sharp sharp taji meke faruwa koma minene zai farudin yakasance dai ta dawo da yarinya gida.
Tana saka hannu a door handle din falo zata ja ta fito waje sai taji alaman kmr ankama ne ta waje da alaman ana kkrin shigowa ne ciki.
Bugawa da karfi kirjinta ya soma yi,she was seriously hoping taga wasime sai kawai taga taheeer ya shigo
Da Kallo daya yabita
Ina zuwa haka?
Dan shiru tayi kanta na kallon ƙasa wanda hakan yasashi fahimtar cewa da akwai matsala
Amma baice mata uffan ba ya wuceta yay zaman sa a falon yanamai harde kafa daya akan daya…
Dakanta ta yanke hukunci bayan tay doguwar muhawa da zcyarta snn ta juyo ta fuskance shi ta shiga fayyace masa halin da ake ciki
Baice mata uffan ba ya dauki key din motar sa kawai ya fice a falon…
Direct yay gidan su saheeb tundaga bakin gate na farko ya danna horn,take security suka sanar dashi cewa saheeb bayanan suna asibiti a sashen emergency.
Tambayar sunan asibiti yay akamasa kwatance
Wani iri ya dingaji a zciyrshi ayayin da yake tuki cikin gaggawa,duk tunanin shi mezai saka saheeb ya kasance a emergency by this time,to ina wasimen ita kuma? Duk sai ya dauka ko hatsari sukayi,.har ya isa asibitin hanklinsa bai gama dawowa jikinshi ba
Yana isa ya samu daidai lkcin likitoci sunfito har sunyi inviting dinsu ciki domin suga patient dinsu cos she is stable now
bayan zee ya hango daga can nesa Dake itace tay shigewr karshe,direct ya nufi dakin data shigen cikin sauri yana isa daf da bakin kofar Ya somajin muryan wasime cikin tsorata da kuka sosai ayayinda take maida wa saheeb duka labarin abunda xee ta aikata mata acikin washroom dazu
..idanun saheeb ya kada yay jaaaaa kamar zaiy mata kuka, He was sooo furious ransa sosai ya harzuka ya dagule akan lamarin.
…mannuwa Da bango zee tay tanata kukan munafurci just tryn to gain pity from anisa kanwarsa,duk wani abun da wasime take fadi saida ta karyata, kusan ma musu ne ya kaure a tsakaninsu. Kowa na kuka na fidda abunda kecikin ranshi.
Taheer yana daga bakin kofar yanajin komi da suke zantawa,wani irin zafi ya dingaji acikin zcyarshi, wani tukikin abu yaji aransa na ingizashi akan ya dauki mummunan mataki.
Jikinta is queit serious Likita yace subarta anan ta zama stable kafin zuwa gobe sai akaita gida.
“Shirin Æ™irar bilti saheeb yakeyi domin ya sanar da ita halin da ake ciki caraf saiga sallamar taheer akansu wanda yayishi ciki ciki kamar an sakashi dan dole, mugun haden ransa yy yana huci kamar wani mayunwacin zaki fuskarsa babu alaman rahma bare sauki
suna hade ido da saheeb kusan subucewa wayan shi Tasoyi a hannun sa zata fada kasa yy surin cabewa jikinshi a sanyaye, wasime tana ganinsa ita kankame jikinta tanamai runtse idanunta cike da fargaba mai gauraye da bugun zuciya mai tsanani.
..cike da karfin hali saheeb yy dan murmushi yanamai miko mai hannu suyi musabaha yace “
“Wow Guy yaushe a gari, kuma waya fada maka muna nan? Tsimewa Taheer yy Baiko kalle hannun sa daya miko ba bare ya kulashi bare ma harya amsa maganan sa,acikin yanayin fizga da bacin rai yabita gefen sa ya wuceshi ya nufi inda wasimen take yatsaya yana kallonta,take jikinta yahau rawa wani sabon kukan ta fashe dashi mai ban tausayi,yana tsaye yana shiru baice mata uffan ba
Igiyar ruwan da aka jona mata ya kama ya tsinke snnan ya zuba hannayen sa ya tattarota gaba daya ya dagata cancak a hannun sa ya rungumeta a kafadunshi ta lafe ya kama hanyarsa zai fita tare da ita
Saheeb kamar zaiyi kuka yabi bayansa da gudu kuma a rude,cike da hanzari yana cewa
“Taheer..’kamar baisan shi ba haka yay masa shiru,tafyarsa yake a nitse kamar ba tafasa yakeyi ta ciki ba.
“Taheer pls wait nd hear me out…ya zakay kazo ka dauke yarinya anakan mata jinya…wai meye haka ne?taheer pls now..
Listen to me give me a chnce to explain wallh ba laifi na bane..
Saheeb ya karashe maganan hanklinsa a matukar tashe
Da kamar bazai kulashi ba can kuma saiya juyo ya dubesa game da
haderansa cikin sigar kashe masa wata xaxxafar warning wanda tazo a xafafe dan lumshe idanunsa yay snn ya bude “muryansa a karsace yace”…Saheeb,
i do not want to see u near this girl again, har abada!!..kuma nafada maka kenan.
yanakaiwa nan ya juya abunshi ya saka kai yana tafiya yana huci
“Taheer no pls..”
Saheeb ya furta hakan a cikin sautin magiya sosai bakaramin faduwa gabansa yakeyi ba don yafi kuwa sanin taheer,he will say it once kuma bazai taba sauya ra’ayin sa cikin sauki ba yana cikin wannan yanayi saiga su anisa sun firfito atare da zee duka suka dunguma sukabi bayan taheer din har suka kai waje…….