FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta gama lura kamar aure ake shirin yi mata ba itama,ita ko ajikinta dan bayau ta soma ji ko ganin aure ba,zaman su a sansanin fulani yasata fahimtar komi,daga ya mace takai shekaru 9 xuwa sha 11 to a al’adance ma ta isa ayi mata aure,halan itama takaine,taga duk kawayenta nacan ma an bijiro da maganan aurensu duk dama bata san menene shi auren ba amma haka dai suke cewa.

Dattijon dayake bayani bazai wuce shekaru 60 ba, yace wa matayen sa da suke zazzaune agefensa akan da su shirya tarban É“aki dan Lokacin isowar waliyann angon kawai ake jira angama shirye shiryen komi afannin amarya,Innono tacigaba da masa godiya tana saka masa albarka da tare da danta Qasimu daya amince a aurawa jikarta dahiru aure da wasimé,”

Dama can angaya mata danta Qasimu yay sa’ar aure duk dama tasan Æ™abila ya auro amma ta lura kamar matarsan tana iya bakin kokarinta wajen yin musu adalci,sosai innono taji dadi da suka bata hadin kai ta bawa jikarta dahiru auren wasimé badon komi ba kodan sabida ta inganta rayuwrta na nan gaba.

Around 3pm na yamma saigasu kuwa sun iso,danta qasimu da matarsa da dansu taher wanda a shekaru bazai wuce ashirin ba,yaron kyakkawane na bugawa a jarida yafima iyayen nasa muhibba,yanada sigar mulki da kuma Æ™asaita irin na wayayyu yan birni,shi tunda yaxo baiyi magana da kowa bama, Hannu bibbiyu iyayensa suka amshe zancen aurensa wanda aka Æ™ullasa bayan sallahn la’asar ranar jumu’a.a bakin masallacin Kofar mai kasuwan anguwan mahuta ..”Taheeeru Elqasim junaid da matarsa wasimé Aliyou denge Akan sadaki dubu dari da hamsin lakadan ba ajalan ba.,aure yaci darajar dumbin jama’ar gari sabida ranace ta cin kasuwar kauyen,da wanda yasansu da wanda baisansu ba kaf an halarta ankuma sakawa auren albarka.

Nan danan mata suka tada Yan raye raye da kade kade na al’ada guda ya cikka tsakar gidan kamar dagaske,kan kace kobo auren da akayi tsammanin yinshi cikin sirri da tsagaitawa saigashi yayi armashi har andanyi wasanni na al’ada antarawa amarya da ango kudi,Matsala daya aka samu kasancewar wasimé yar karamace batasan ma me akeyi ba,shekarunta tara ne kacal,shima taheer sam baiji dadin hakan ba a xuciyarsa dan baisan yaya xaiyi da wannan premature auren da aka musu ba,shikansa he is not ready to be a husband yet musmn ayanxu daya saka zancen karatunsa agaba,

toh inaga kuma yarinya Æ™arama yar nine years wacce batama san zancen me akey ynzu ba,yasan wannan wani nauyi kawai aka dora masa,da kuma rainon Æ´a wanda aka laÆ™a masa akansa,saidai shi mai tsananin biyayyane ga iyayensa, shiyasa bai nuna komi a yanayinsa ba,kuma yake biye musu a duk da wayewarsa da ajinsa hakan bai hana ya amshe batunsun hannu bibbiyu ba..besides kawai auren aka daura musu ,ba’ac su zamto tamkar mata da miji aynzu ba,saidai yasan ixuwa wani lokaci inta
Girma hakan zai iya faruwa,Nasiha kam sunshata awajen su innono da mutanenta da ta bawa waliyayyancin wasimé.

Yaga ba’aje koina ba har iyayensa sun kwallafa yarinyar aransu, jin cewa ita marainiyace babu uwa ba uba babu dangi sai innono.,innono tasa a hada auren da jininta ne sabida gudun hannun da wasimé zata iya fadawa ciki inta tafi ta barta awani wajen.

Yanzu da akay mata aure tun tana yar ƙaramanta ai zata iya zama a karkashin surukunanta harsai ta girma snn ta tare a dakin mijinta,
Sannan shima dahiru zai iya cika duk wani burinshi nayin karatu da zamowa duk abunda zai zamo kafin wasimé ta gama balaga ta mallake hanklin kanta,Koda bata sani ba, tasan dai rayuwar wasime na nan gaba bazai sangarta a hannun wani jininta ba.

Washe gari sassafe suka bar garin suka doshi hanyar cikin garin kaduna bayan an kammala komi na al’ada.
Innono da danta Qasimu da matarsa sai amarya da ango wanda haryanxu acikinsu wani baice uffan ma wani ba,ya zamewa taheer jiki shi baiya saƙe fuskansa da kowa,da wuya kaga dariya akan fuskansa ko murmushi zaiyi baxai wuce na gefen baki ba.

Shi wani irin murdadden mutum ne dabaison cikia magana bare zancen shirme,yana da ƙarfi da izza,shiyasa Arayuwansa
Yake mutuwar son yay millitary school ya dawo land army amma haka firrr iyayensa suka hanashi.

alhj Qasimu da matarsa
Sun nuna kamar likita kawai sukeso ya zamo,amma son da sukeyi wa dansu yasaka suka ƙasa yankemai babban burinshi na sob zama soja dan wani son zuciyarsu,Shima anashi fannin son dayake ma iyayensa yasaka ya ƙasa yankewa kanshi hukunci
Dan a duniya babu wani abunda yake tsananin ƙauna yake kuma darajawa kamar iyayensa

Kaunar da yake musu yasashi yafara pursuing careersa ta zamowa likita, amma likitan sojoji.

Wanda Yana kammala sec schl ‘dinsa at age of 16yrs ya samu scholarship mai kyau bisa kwaxonsa a NEET exams da suka zana na xuwa military school india,HPSP wato health profession schorlaship program ita ta dauki nauyinsa tana biya masa kudin makarntarsa harya kammala cos is just 4yrs alkcin,ynzu haka baifi wata biyu da dawowarsa ba,ynzu haka Mahaifinsa yana kkrin nema masa wata dama A “NAMC” nigerian medical millitary corps service,dan yayi 2yrs medical functions, wanda daya kammala zasu turashi can USU (uniformed service university of health) dats the national medical center is bethesta maryland,acan washintong D.C,inda zai Æ™arkare karatun nasa sann ya dawo gida.

Dukkan wani jajircewa da tanadinsu arayuwa wa dansu taheer kawai sukeyi shima dukkan soyayyarsa da biyayyarsu naga iyayensa,sunada burin bashi ingatacce kuma tsaftacacciyar rayuwa dake shine kadai Allah ya azurtasu dashi a duniya
,Mahaifinsa al’Qasim baida wani sana’a face saida siyarwan motoci, ita mahaifiyarsa kuma malamar jamia ce amma yanzu tanata kokrine domin shiga matakin farfesa a fannin mecha-tronics and electrical engineering.

SHARE PLEASEEE👏🏽👏🏽💘💆🏻‍♀️🤌🏻
7/25/22, 19:19 – Kawata: FITAR RANA…
……faduwarsa

BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.

3️⃣
Saican wajejen bayan magrib suka iso cikin garin kaduna,lkcin kowa ya gaji,wasime kam tanata sharban baccin ta
A kofar gate din babban gidan qasimu sukayi horn mai gadi ya taho ya bude musu ƙofa, tunda sukayi parking taheer ya sabule jikinshi ya haura sama can dakinshi babu abunda ya kuma sauƙowa dashi,yana shiga dakinsa ya fada akan gado yana maida gajiyayyen numfashin shi dayake fitowa daga can ƙasar huhunsa a hankli.

kirjinshi da zuciyarsa sai racing sukeyi yabi ya rasa kwakkwaran dalilin faruwar haka,duk yadda yaso ya mance da zancen auren a zcyarsa ya Æ™asa,ynzu shknan fa yay aure..kwantaccen gashin kanshi ya shafa ahankli cikin jan numfashi ya furta”what the fuck,wani irin mixed feelings na i cant believe this shi ya mamaye sigarshi wanda yy kama da kamar zai yi murmushi kamar kuma zaiyi kuka a lokaci guda,daga nan miÆ™ewa yay gaban wani dan mini freezer ya buÉ—e ciki,2 rows ne mai dauÆ™e da chilled bootle water sai chapman ansha rabi an bar saura,Ruwan kawai ya dauÆ™a ya bude ya kurÉ“a kadan yana lumshe idanunshi after each sip snn ya mayar ya ajiye ya mike ya shige bathrum,wanka yy yabiya sallolin dake kanshi,tuna wayarsa a kashe yasashi kunnata,dan kadan yay scrolling baiga wani abu intresting ba ya Æ™ara kashewa,da kyar yau yay bacci dan aranshi babu abunda yake face juye juye da tunanin auren da aka dora masa,a bangaren wasime kuwa saiyau taga babban gida Æ™ere tunaninta,yo duk kauyensu bataga i irinsa ba,da xuciyarta kawai taketa shagalin hira tana maganganu kai kace nazarin wani abu muhimmi takeyi ,gidane irin na zamani yasha interlocks ga motoci a parke 1,2,3 saida ta tsaya kirgawa tass acikin zuciyarta,motoci guda uku ne harda wanda sukazo aciki making 4cars,sai kuma jincheng rubber rubber da tagani agefe,baki bude tace”laaah gidanma harda Achaba? Bakinta ta washe a tunaninta ai zatana xuwa gida tunda a machine kawai taga ake shiga kauyensu data fito,…sai kalle kalle kawai take abunta tana leken wajajen da suka burgeta kamar wawiya,da alama tamance wai yau an dora mata wani abu akanta waishi aure Hahaha inza a yankata aynxu ma bazata iya tuna komi ba .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button