
Fridge ta nufa ta dauko bottle water Tana kawo ruwan ta aje agabansa ta juya zata bar wajen.
Kallo daya yay ma ruwan
Yace”Ke xo nan!ta juyo kanta a Æ™asa cikin sauri
Tace gani.
kallon dayay mata yasata komawa dauƙo masa kofi,cike da nitsuwa ta durkusa agabansa a hnkli ta kwance murfin gorar snn ta zuba masa ruwan dan daidai,tana shirin miƙa masa kenan ƙarar shigowar saƙo a wayarshi ya dakatar dashi,gefe tadanja ta tsaya da ruwan a hannun ta,zaro wayar yy daga aljihunsa ya ga sakon daga banki ne,..bai tsaya lissafin kudaden da suka shigo ba, idonshi yakai kan sauran kudaden da suka rage masa acikin main acct dinshi,abincin shi ya cigaba daci a nitse kamar wanda taunawar ke bashi matukar wuya yana tunanin yadda kudin zasu kaishi izuwa har wani karshen wata.
Kansa yay balain zafi,ajiyar zuciya ya dingayi a boye cos he needed money for his scholarship exams,ga karatunsa da ya sakoshi a gaba,ga biyan schl fees din wasime na shiga aji uku da sauran tarkacen respobsibilty nata da baza a arasa ba.
Duk wani bills din daya shafi gidan kama daga biyan ma’aikata da abincin da zasu ci,sutura da kudin asibiti duk iyayen sa ne sukeyi amma hidiman kansa dana wasime duka daga aljihunsa yake cirewa yayi kuma ayanzu ba wani matsayi mai yawa yake dashi awajen aikinsa ba.
Shiru wajen ya dauka dan saida yagama cin abincin sa snn ya ajiye plate kafin ya lura da tsayawar wasime akan sa,yi yay kamar baiganta ba,hannu yasa ya dauki bootle din ruwan dake gabansa dan sauran daya rage aciki ya kafa bakinshi yana sha a hankli har saida yaji ya koshi,hamdala yy snn ya aje gorar a kasa ya dora kafafunsa daya akan daya yawani shareta
hakan yasa wasime kankance idanuwanta akansa tunda bataga amfanin kofin dayasa ta komawa ta dauƙo ba yasan ba amfani dashi zaiyi ba.
Turo bakinta tayi a shagwabe tanamai takune fuskrta a boye tana hararsa da gefen idanuwanta..
Kallo daya yy mata ya dauke kansa Numfashin sa yasauke a hankli snn yace”Meyake hanaki zuwa schl?
tambayarsa ya dawo da ita cikin hayyacinta a dabirce sabida batayi tsammanin jin hakan daga bakinsa ba,ganin baiya da lokacin kansa kwana biyu batayi tsammanin yasan bata zuwa makarnta ba,dan langwame wuya tay,snn tace yaa daheeru.
Kansa ya dago cikin sauri ya kalli cute lips dinta yanajin wani zirrrr acikin jikinshi,cos Yadda ta sako maganan a sakaltacen yanayi sautin muryanra mai dadi ya bugi dodon kunnenshi cikin bada wata daddadan yanayi mai gamsarwa.
muryanta mai shaƙe da shagwaba da kilibibi ya balain shagaltar masa da zuciyar cikin wani zautaccen tsumayi.
hannu ya daga mata a kasalance snn ya watsa mata wani irin sasanyar kallo mai cike da ma’anoni, da wuri ta sauke kanta kasa cikin jin kunyar irin kallon daya watsa mata,cikin sauke ajiyar zciya gameda shan qamshi yace”Ke!wai dolene in zakiy magana saikin fara da Æ™iran suna na?Shiru tay tana famar jujjuya yatsunta acikin juna cikin jin kunyarsa sosai.
Cikin tausashiyar sauti mai dauke da kamala gamida nitsuwa Yace “Tambayar dana miki kawai zaki amsamin “nace meyake hanaki zuwa makaranta?”
Ajiyar zcya ta sauÆ™e a hankli snn ta dago kai ta kalleshi sai taga ya kara yin mata kyau hasken fatar jikin shi ya dadayin kyalli,fuskanta a shagwabe sosai ..tace “Yaa dah…saitayi shiru ta cigaba da murmuda yatsun ta cikin juna kanta na can kasa.
After like a scnds tace “uhmmm yaya,dama malamin mu ne faa yace wai kar inÆ™ara zuwa.
Idanunshi yy rolling a yangace cikin tsareta Yace “What?..saboda me….dan shiru tayi tana tunanin karyan da zatay masa,can Ta budi baki a dan tsarge zata bashi amsa kallon yanayinta ya dingayi cikin datsar numfashin ta tareda miÆ™ewa tsaye yace”toh ya isa haka banason ji,Ki bacemin anan wajen kije ki kwanta dare yay.
Batace mishi uffan ba Da sauri ta juya fa nufi sama cikin ranta dama bata son tayi masa Æ™arya,attitudes dinsa ne haryau bata saba dasu ba,mutum sai shegen fadin rai?tana tafiya tana kukuni tana cewa “Allah ya kyauta”..direct kan gadonta ta nufa ta kwanta tunani kalala suna bijiro mata acikin ranta masu firgitarwa.
Tasan hala zuwa gobe taher zai iya fahimtar karya kawai takeyi gashi kuma tana balain tsoron masifarsa,saita yanke aranta kawai gobe zata daure taje makarantar koma mai zai faru zata daure takumayi kkri wajen kare kanta daga mutanen da suke takura mata.
Washe gari asabar karfe tara na yi saigata ta fito sanye da green hijab dogo har kasa,kominta green colour kalar islamiyarsu,mamaki ne ya cika zuciyar tolu dayaga ta fito zai kaita makaranta,da barin jiki ya tarbeta yana Allah Allah ta shiga mota ya soma takura mata da maganan banza dan bakaramin damuwa ya shiga kwana biyu data bijire musu bata fitowa waje gaba daya ba.
Tana shiga motar ta maida kanta gefe ta bata ranta tayi tsamm, maganan iskancin duniya tolu yay mata donta harzuka ta amsashi amma har suka isa schl uffan batace masa ba ta bude kofa tayi wucewarta cikin makaranta…
Kallon bayanta ya dingayi harta bace na ganinsa,ganin yadda wasime soma girma sosai…inka gan dirinta zaka iya cewa ta wuce shekarunta musamman ma yadda kugunta yake dada bazuwa nonowarta suna dada fitowa dakadan kadan.
3:pm daidai bayan an tashe su yazo ya dauketa
Still bata kulasa ba,wani magana daya furta mata ne ya bata mata rai har taje daki tana ta sauke hawaye…
Tolu shine mutum na farko dayasaka ta soma tunanin kotana da iyaye a duniya, dan tunda ta girma anono kawai ta sani a matsayin uwa kuma uban ta ita bata da kowa arayuwarta sai anono.
Banda yanzu data zo nan ta gamutsa acikin rayuwar su bilti da taheer,bazata iya cewa tasan wani danginta ba
..yau tolu ya saka taji kamar alfarma kawai ake ma rayuwarta anan din,kullum sai yanace mata wai inta zo dakinshi ta bashi hadin kai shima zaina bata kudi da abun dadi.
Saboda wannan abun Yau kwata kwata bata fito a dakinsu ba,juye juye ta rinkayi akan gadonta ita kadai cikin damuwa ko zuwa taya bilti aikin kitchen din yau batayi ba..daf ana kiran sallan magrib ta mike ta doro alwala tayi sallah sann ta canza kaya izuwa doguwar rigarta dan daidai ready made ce da aka siya mata na shan iska,a nitse ta sauko ta samu bilti harta kammala aiyukanta tass ta rarraba musu abinci.
Tsayawa tayi tun daga bakin kofa tace
Sannu da aiki bilti
Bilti tace yawwa wasime
Har anfito..ya schl din yau naga gaba daya baki fito ba..ko lpya kuwa?
Dan shiru tayi zuciyarta namata nauyi tana son ta kara kawo karar tolu wajen biltin amma bata san ta ina zata fara ba.
Duba da wancan karon
Share zancen taheer yay ya dora mata laifin komi.
Ji tay idanunta sun ciko da ruwa sai ta soma jin wani iri iri acikin zciyarta
Kamar ma ta fashe mata da kuka..
Muryan ta na rawa ta Budi baki cikin yanayin damuwa zatayi magana caraf sai ga sallama akansu shuru tayi kirjinta na bugawa da karfi koda bata kalle wajen ba tasan taheer ne ya shigo..
Da kallo daddaya ya bisu snn suka gaisa da bilti
Itama ta juya ta gaishe sa a ‘ladabce ya amsa babu yabo babu fallasa yana tsaye Bilti ta kalli wasime Toh ki shirya abincinsa ki kai masa falo.Ni zan kaiwa su tolu nasu awaje..
Cikin hanzari wasime ta amsa da toh snn ta isa gaban table zata soma harhada masa dinner akan tray,duk yana lura da ita, kallon bilti yy cikin saukar da muryansa kasa yace kibata takai nasun ke ki hadamin da kanki..