
karshe babban mai aiki kuma nannyn gidan wanda suke ambata da suna Bilti ita ta riƙo hannunta tajata izuwa ciki tayi mata wanka fesss ta shafa mata mai tasa kaya nan danan bacci mai nauyi ya saceta danko abinci bata iyaci ba,washe gari da asubahin fari taheer ya farka ya fice sallahr fajr shikadai danyau bai jin zai iya jiran dad dinsa kamar yadda ya saba dan harynzu basuyi wani dogon hira akan lamarin aurensan ba,kuma yasan da maganganu sosai a bakin mahaifin nasa,shidai baison yay tattaunawa maizurfi, he dont really care inde hakan zabinsu ne shimai musu biyayya ne ako wani irin hali so long as dis marriage bazai hanasa cika burikansa na rayuwa ba.guntun ajiyar zciya ya sauke ayayin dayake sauƙa ahankli daga kan matakala,jallabiya brown ce ajikinshi tasha karin guga ta masa damas ,a hnkli yake takawa alaman baison kowa yaji motsin fitarsa daga gidan,tunda yy alwala ya zauna cikin masallaci bai ƙara fitowa ba,yau sai wajajen bakwai saura ya dawo cikin gidan sallama yy a kofar falonsu,
Abbansa na zaune da jarida a hannu ya amsa,waje ya nema ya zauna a kasa sai ynxu ya lurada innono data fito ta shirya tsafff tana zaune a falon itama tana kallon tv tare da mahaifinsan bazaiwuce suna tattaunawa akan lamarin aurensa ba,wani haÉ—e ransa yay tamau kmar bai taÉ“a dariya arayuwarsa ba,mentally ya datse zcyrsa daga bugun datake snn ya dan cixa labbansa a asirce,idanunshi yay rolling snn yy Æ™asa dasu a miskilance “Anono kintashi lpya? Da sauri ta amsa shi…lpya lau dahiru Angon jiya har anhito kenan,ajiyar zciya ya sauÆ™e irinta cikin wuyar nan baice uffan ba
Tahau bada labarin shagalin jiya,da yadda aka tara musu kudi wajen gasar rawan ango da amarya da akayi,amarya ta samu dubu uku cas cas ango ya same dubu biyu da dari biyar,tace Sai dai fa kuyi hkri dashi na sallame yan biki kunsan abun bawai na shirya masa bane,alhj Qasimu yanata murmushi uffan taher baice ba,shikansa yasan jin sallamar san yasata ƙara himman maimaita maganar da sukeyi na batun auren na sa,hirarsa ma a sama sama takomo amsawa tana jaddada masa cewa tabar musu yarinya marainiyan Allah
.tace”nide ba zama zanyi anan ba saiku riÆ™eta amana inmakun zalunceta Allah na kallonku, nide zan tafi tasha can anjima motar shayibu zaibiyo tashar sai kacewa danka daheru ya ajeni can.,alhj qasimu dake satar kallon dan nasa yaga ya sunkuyar da kansa can Æ™asa ya bata shiru,yace babu damuwa mama ai gashi nan yanajinki,”my son kanajinta ko?kau da kai
Taher yy baice uffan ba ya gyara zamansa, suna cikin tattauna haka saiga shigowar matar gidan hannunta dauƙe da flask din ruwan zafi da wainar kwai da kayan karyawa
…ferfesun kan ragone cikin cooler da kayan tande tande an naÉ—e shi a babban leda wanda innono xata wuce da shi sabida yunwa dan sukansu basu san inata dosa ba zama innono tayi ta Æ™arya sann
Ta sassaka musu albarka,tare da zuriarsu.
Ƙarfe Takwas saura wasimé ta farka bacci hannunta bisa baka tana kkrin tare wagegen Hamma daya taso mata hartakai hannunta baki saikuma ta firgita ta sauƙe tahau tattaba jikinta jin duk ta jiƙe da fitsarin datayi a kwance,subuhanalillah!!
da mugun gudu ta sauÆ™a akan gadon ta riÆ™e kirjinta dake bugawa da karfi fuskanta tamkar zatay kuka ta doÆ™a salati” innallahi wa inna ilaihi rajiun na Higa uku !!fitsari nayi,ta tattaba gadon sann ta tattaba jikinta”ayyy ashe fitsari nayi..yau na higga uku,a hargitse ta juyo cikin magagin bacci Da muryan tsoro tana neman innononta.innono
Ano..Cin karo da idon mutum akanta yasata yin tsit ta koma baya a tsomare kamar wata barauniya,”wata mata tagani agabanta sanye da riga da zani da wani baÆ™in hijabi,gashi Allah ya xuba mata ruwan ciki gaba daya sai taji hanjinta na curewa tsabar tsoro,suna hade ido taji gabanta ya fadi rass duk sai taji ta rude,duk damuwarta fitsarin datayi musu akan’ gadonsu tanayi tana waiwayen wajen,wayyo Allah rabonta datay fitsarin kwance fa yau yakai shekara guda kenan amma meyasa yau taga tayi kuma a gidan mutane?sai satar kallon jikakken gadon take da gefen idanunta da suka firfito tanayi tana damÆ™e zaninta da hannunta dake karkarwa, kiris ya rage Bilti ta fashe da dariyar yanayinta dan sosai ta bata dariya.
Cikin gyaran murya tace yan mata harkin farka?..zatayi magana bilti ta katse ta cikin sauri “natasheki kiyi sallah kince min toh ko harkinyi sallahn kenan?kanta ta sauÆ™ar Æ™asa kirjinta na bugawa fat fat,ta rasa mema zatace daga nan wani shirune ya dauÆ™e Wajen,murmushi kawai bilti tay snn tajanye hannun ta tay da ita bathrum,”Cire kayanki, ta umarceta sannan ta soma hada ruwan wanka mai dumi a bath,da kyar wasime ta kammala cire kayan nata ta tsaya daga ita sai pants,duk ta kame jikinta waje guda sabida tsoro da kunya jikinta duk rawa yake,haka ta dunkula kayantan a hankli ta ajesu kusa da wani empty bucket tana ta kallan inda tajikasu da fitsarin cikin nisan tunani,”Uuhum uhnmmm
Gyaran muryan matan ya Æ™ara firgitata ta dago kanta a firgice tace naam ‘brush ta gani a hannun matar sabo dal a ledansa aka budesa,a hnkli tace,”xo nan kiyi maza ki goge bakinki saimu tafiko?tune din lallami datasa yasaka wasime gyada kanta batare da tay niyya ba, Ƙarasowa tayi kamar mai tsoron wani abu ta tsaya agefenta,Sink bilti ta kunna ta mika mata brush din tana kallonta harta kammala yi dakanta,She was bit relieve dataga ta iya batayi wani kuskure ba,bayan nan tayi mata wanka suka jajjaba alwala,.dan karamin towl ta dora mata sann ta jawota dakin ta koma ciki after like 5mint ta dawo ta sameta a inda ta barta tana tsaye,Batace mata uffan ba ta kalli gaban madubi “mikomin vasaline”babu musu maza taje ta dauko ta kawo,tana ajewa bilti ta dan jawota kusa snn ta soma tsantsane mata jiki ahankli snn ta shafa mata mai ta mulÆ™e ta tass ta gyarata..ganin ta runtse idanunta tana kakkame jikinta yasata sakin numfashi ta kyaleta mamaki da fargaba duk ya cika kirjin wasime,a nutse bilti ta kammala mata komi ya rage saura saka Æ™aya saiga sallamar innono ta fado dakin fusknta murtuke,tsaye bilti ta miÆ™e da dan fara a a fuskanta tace “Kaka karde har an fito,kiyi hkri saura kiris inkammala shiryata,ganin wasime fess fesss yasa innono sakin fuska tana washe baki..”lahhh baiwar Allah harkunyi wanka.. kai sannunki da aiki,karki damu wallh dama ainice mai tafiyar ita kuma wasimé inazata ai tazo gidanta kenan, nima zuwa nay nan indan jira anan,ina ni ina kallon kayan takaici,mtsew Allah yabaka jika mai shegen mulki,”.kinga na shirya zan tafi dayakaini tasha in samu shayibu shine wai saina jirashi yay wanka kuma fa fess jikinshi yake,aikoda na shunshuna dandamalin rigarsa da zai wuceni harwani qamshin inibi yakey,yo saide in hammatar sa ne bai wankeba,kenifa na lura dahiru fa dan walakanci ne dama shide akomi sai anjirashi..neman yayi’ mun kora da haline kawai
A gidan nan..nide ina ƙara baku amanar ƴata yannan kusamin ido sosai akansa karyaga kamar sadaqa aka basa ya wofantar da ita da jan fuskarsa awajen fatashhh kamar anja baya an kalli agogo..
hahahaha Bilti ta kyalkale da dariyar yanayin maganan nata dayazo da yanayin barkwanci tace “kai kaka toh karki damu da wannan indan wannan ne ai zamu kula miki sosai da wasimé surutai innono ta cigaba dayi abunta,daga nan bilti batace komi kawai tajanye zanin gadon da wasime tay fitsari ta wuce bathrum dashi,ganin anbarsu su biyu ta riÆ™o kafadun wasimê data cuno bakinta gaba tanajinta tamkar wacce zata sakar mata kuka, “kema sai sime sime kike ban kayan toh in saka maki,tasa hannu ta fauce kayan,Riga da sket ne mai kyau na back of fish
Amber colour dinkinsu na karkara ba amasa style din komi ajiki ba,Sosai wasime ta tsane Saka sket a rayuwanta,ita tafi sabawa da riga da zani galau galau taganta Kamar yadda ta saba acan kauyansu a jos,wani langwame wuya tayi ta larne kamar zatay kuka,”Innono wannan matsatsen abun kika samin?,keyanta taji an dungure ta baya”ke kinci uwaki,ki tsaya ingama sakamiki tukun zaki gani bazai matseki ba,tafin hannunta takai saman fuskarta tana turo bakinta a shagwabe har innono ta gama sakamata kayan yai mata rass kuwa sabida tanada ginannen jiki ba ita tsiririya sosai bace”
“yawwa baga ki nan kin fito ba,innyeeeee gangariya tsiren mangu..wazai ganki ahaka fess yace katuwa irinki kina fitsarin kwance?,cikin gatse innono ta furta hakan tana hararta sabida ta tsare farfarun rikicinta dantasan wasime da naci akan abunda bataso yanzu saitasa acanza’ kayan nan,shiru wasime tay tana wasa da yatsun hannunta,kan gadon innono ta kalla snn ta kalli idanunta sai tafara mata magana ahankli Kuma cikin sigar lallami,yanzu fisabillahi wasimé saiki rasa abunda zaki kawo tsaraba a gidan surukanan naki sai fitsarin kwance?garinya akay haka..shiru tayi daga bisani idanunta ya cikko da ruwa ta dago muryanta a sanyaye tace
“Innono..ba laifina bane nifa Wani abu na dingaji yana fifitani cikin dare,sai naji kamar ana watsamin ruwa toh dana farka sainaga har waje ya jiÆ™a”
Wayyooo ahhhshh inno..no ..Kunnenta taji anÆ™ama, sai kuma aka sake aka rungumeta sosai,ajiyar zuciya ta saki tanamai Æ™ara sakejikinta a kirjin innononta data kwantar da muryanta Æ™asa kasa ta dada mannota da jikinta sosai,'”kinaji na ko?..toh karki Æ™arayi ina gaya miki nan ba inda ya kamace ki da kiyi fitsarin kwance bane..nan fa gidan surukunaki ne kiyi musu biyayya kinji?..lafewa tay tanamai gyada kai childishly,jinta kawai take amma batasan komi ba, “ga nan BILTI zatana miki dukkan abunda kikeso,bance kuma ki sake jikinki ba,yadda kike aiki a gida can nan ma ki saki jikinki kiyi,nan ma gidane,inkina bukatar abu ki tambayeta kada kuma inji anyi kuka dake.
Ruwane suka cikko idanunta muryanta na rawa tace”innono wai barina anan zakiyine komi?ina zakije Ano?nide wallhy bazan zauna ba zan biki ..Ayanayin tausayawa tana kuma hararata tace “Sau nawa zan gaya miki da kizauna anan?hannu tasa a fuskanta snn ta fashe da kuka ni yaushe kika fadamin Kawai cewa kikay inshirya zamuzo binni Jiya naji kina cewa anmin aure,yau kuma shine zaki tafi kibarni anan wajen yoo akanme?Æ™ara sautin kukan tayi,innono cikin kyabe baki ta miÆ™e tsaye ta doshi kofar fita dan tasan batada amsar wannan rikici”ai saikiyi
Ni kinga tafiya,harta fara takawa sai kuma ta komo ta leka bayi lkcin bilti harta kammala dauraye bedding din ta fito dashi a bucket zatakai waje rana ya bugashi ya bushe,innono ta washe baki…”baiwal Allah bilti ni na wuce saduwar Alheri nagode nagode da dawainiya Allah yamiki albarka Allah yajikan magabata ,bilti tana murmushi tace karki damu kaka ai aikina ne.
Allah kaiki lpya ya kareki
Innono tace ameen,tana juyawa ta kalli wasime harta kammala hada jakarta ta runguma asigar bori,da sauri ta dauƙe ido kamar bata ganta ba tayo waje
Wanii fuuuuu wasimên ta biyo bayanta tafin hannunta bisa kan fusknta tanajin aranta kamar bazata Æ™ara ganin inonon ba,wani jan zuciyarta take dagske kamar wata mai aljanu idanunta na tara kwalla har Æ™asa suka sauÆ™o cikin babban falon gidan,lokcin babu kowa a falon face Alhaj Qasimu da matarsa duk sun miÆ™e tsaye da shirinsu zasuyi rakiya wa innono,”matar gidan ne ta jawo hannunta tsakiya kowa na mata barka da safiya
Har suka kammala maganansu batace dasu uffan ba.Tana hankare da inononta,tana fita itama tabita kafa da kafa”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un innono dan ALLAH karki tafi kibarni anan wajen.ni wallhy saina biki,ni wallh bazan zauna ba. Wayyyo Allah na na sshhiga uku ta tumu aÆ™asan tiles ta dora hannunta aka,innono na innono na wayyo innono nikam saina biki ..Acikin rudani da firgici ta furta hakan tana tsananta kukanta daya kufce mata bazata.Kuka kawai wasimê take babu kakkautawa kowa na kkrin rarrashinta
Innono kam ko ajikinta danko kallanta batayi baretaji tausayinta,
zamanta anan din shiyafi,dan wannan shine rayuwa mafi daraja da inganci data bawa wani wanda ta taimakawa arayuwanta,ta haÉ—a jininta da wasime aganinta tayiwa iyayen wasimé dukkan halacci da amanan daya dace ace tayi musu izuwa ynzu,acikin zuciyarta tana matkar kaunar wasimenta amma haka tayi kamr batasan anayi ba Allah Allah ma take tabar wajen “Suna fitowa waje wasimé ta bude sabuwar shafin kuka “wayyo Allah na,innono innono,innono zanbiki dan Allah zan biki,wayyyooh Allah na kaf gidan saida ya dauÆ™a da ihun ta tana bubbuga kafafunta a Æ™asa tana kuka sosai.,kusan hanklin kowa awajen saida ya tashi banda innono data cure bakinta sama tayi gum,tasan sukam sabone basuyi dajin kukan yaro ba barinma yaro mai rikici,a sace ta kalle wasime da’ gefen idanunta aranta ta kyabe baki ganin yadda ta turje ana fama da ita,dan kada kanta tay tace “zataxo ta saba ai,”danta Alhj qasimu ne ya riko hannunta cikin lallami kiyi shiru mama na,baya taja tace o o o o cikin sheshehka, kanta take girgizawa tana rabza ihu tana kiran innonon da Æ™arfi,hanklin matarsa ya tashi ta rirriko kafadunta tanata lallashinta amma duk hakan baisa tay shiru ba,sunai mata kallan yarinyane amma basusan aranta tasan mame takeyiwa kuka ba.
Duk sanda innononta tace zatayi tafiya wani wajen dabaida suna toh tasan zata iya daÉ—ewa sosai bata dawo ba.