FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

FITAR RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Agigice cikin matsanacin kuka ta waushi zaninta ta killace jikinta Da uban gudu tayo daki tanata kuka.

Akasa ta sulale tadinga kuka mai tsuma ziciya tana kiran Allah azcyarta.
Bata tabajin zata bar aikinta ba sai yau,kuma bata taba tsammanin zata hakura da neman duk wani rayuwa mai inganci tabar tsabgar mutane ba saiyau.

Ko mai bata tsaya shafawa ma fatar jikinta ba cikin sauri sauri ta shirya kanta tasaka kaya sannan ta saka hijabinta ta kwashe dukka kayayyakinta acikin jaka,kulle malam musa tayi a ban dakin sannan ta sauko kasa da kayanta tana kuka sosai
Danji take kamar ta mutu tabar duniyan tsabar bakincikin abunda ya afku da itam

Wasika mai tsayi ta zauna ta rubuta ma taheer ta aje mishi akan center table a falo snn ta wuce tasha ta nemi motar garinsu kawunta
Tay tafiyarta can.
Is not free maison cigaba ya nemi 08060712446
7/25/22, 19:19 – Kawata: FR 23

Gone too soon

karfe biyar da rabi shaura wasimé na zaune a gindin wani bishiya dake ƙofar makarantan su tayi tagumi cikin yanayin gajiya tana jirar taher kusan kowani dalibi ya watse yayi gidan iyayen sa ita kadaice take zaune a bakin kofar makaranta har yanzu.

Kowani wulgawar BMW musamman ma navy blue in colour kalar motar taheer daga taga wucewar motan a titi sai ta zabura tabisa da kallo dan taga ko shi dinne saidai har yanzu batayi sa’a ba

Tagumi ta cigaba dayi snn ta tashi ta nufi wani red colour kiosk na indomie noodles tana tafiya kamar ana janta na dole daga gani kasan harcikin ranta bata son zuwa wann shagon, naira dari uku daya rage mata ta zaro daga cikin jaka, naira dari ta zara aciki ta siya egg roll da zobo mai sanyi aka bata harda straw snn ta dawo mazauninta ta zauna tana ci tana turasa da zobon ahankli.

Bayan ta kammala ci wani uban kasala ta dingaji, zuciyarta cike da tunanin yadda xata koma shagon ta mayar musu da goran zobonsu musamman ma daya kasance da akwai majalinsan yan gulma da suke zaune tawajen kullum daga ta doso wajen sun dinga kallonta kenan suna fade fade..

Sosai wasime ta tsane abun…

ba abun taki kawo gorar ba,matar shagon duk ta waye da fuskokin yaran makrantansu kuma tana da masifar tsiya baka isa ka mata abu ba next thing sai kaga ta kawo karanka wajen shugaban makranta an zazzaneka.

To avoid all these yasa ta miÆ™e tsaye da kyar ta nufi shagon matar da goran a hannunta, tafiya take a hankli kamar bazata yi ba har ta iso bakin shagon taja ta tsaya.. bayabo ba fallasa ta kalli matar snn tace”Madam bisi ga goranki.

Matar ta saka hannu ta amsa goran fusknta a daure,sai kallon ta takeyi da wani irin sigar gulma tana dan cuna baki zcyar ta cike yake da ita,gani tayi kullum wasime ta wulga ta wajen shagonta sai an samu wayanda zasuyi admiring natural beautyn ta, musamman ma yanzu data dan soma yin tsayi kirjinta ya soma fidda shatin kirgen dangi.
Most guys are fantasizing about her kuma ba komi yake mugun daukar hanklin su kamar kasancewarta baƙar fata Amma sai Allah yay mata kyaun fuskan da baiya bukatar ado ko wani kwalliya ba.

Ita kuma matar tana da yarinyarta mai suna omolara,fara ce sol takan kula mata da shagon so kullum tana zuwa tare da ita,yarinyar nata kyakkywa ce yar shekara 22 amma haryau babu mai tayata awajen sabida batada wani kamun kai duk wanda yace yana sonta ko awasane bazata taba jan ajinta taba kowa yazo sai tace masa yes yes,yawan zaman wasime a gindin bishiyar yasaka hanklin mutane duk ya koma kanta akan haka bakaramin haushinta matar takeji ba shiyasa kullum acikin kushe bakaken fata take sabida haushin jin ba a kula yarta ba sai wasimé.

Cike da gatse da nuna izza tacema wasime
..Ke wai kullum sai anyi lattin zuwa daukar kine,wai shin inane ma gidan ku da baxaki na zuwa ba?baki da iyayene ko me?..mtsww hausawa kenan, sai an sako yaran makaranta snn a barsu a titi da wayo suna neman maza hmm daga haka dai ake koyan ma yara karuwanci.

Wasime ta juyo da mamaki tana kallonta dan takune fuskan ta tayi snn ta kyabe baki cikin kadadi da rigima tace
“Uhm naga kin damu da zama na acan, toh zakina kaini gidan mun ne? Matar tamata shiru,tsaki taja..toh nide inada iyaye kawai basuga daman xuwa bane!!..cikin zaro ido Matar tace..keee bana son rashin kunya daga tambaya shine zaki nemi kimin rashin kunya?wani Hade rai wasime tayi tana turo baki cikin kukkuni “Yo ina ruwanki dani…ainima amsa na baki babu ruwanki dani tunda bake kika haifen ba…tsawa matar ta daka mata saida ta firgita ta koma da baya A fusace Tace “Dallah get out of here,wawiya marar kunyar yarinya kawai,look how innocent she looks ashe shedaniyace ji yadda take amsamin magana kamar wata sa’arta.Ki wuce ki tafi anan konazo na sameki awajen.

Tsaki wasime takara ja cike da kumburo baki tana tafiyar yanga
tana cewa eh din magulmaciyar mata kawai,wallh badai inyi karuwanci ba..fatar bakinki ya sari guntun kashinki!

haushi ya kama matar tana shirin fitowa ta capketa wasime ta juya a guje tay bakin titi adaidai lokacin wani haddaidyar lancruiser jeep x20 irinta gwamnoni yayo kanta kamar zai hankadeta

Wani kiiiii motar yasha gabanta sai da taji gaban ta yay mummunan fadi ta raxana,jikinta ne yahau rawa a mugun raxane taja da baya tana kkrin dago idanuwanta nan taci karo da babban jeep wanda yasha tinted all out bata iya ganin ko waye aciki,,

wani guluk ta hadiye yawun bakinta, tsabar tsoro da baya baya tafaraja ganin kamar ana kkrin sauke glass din jeep din,kirjinta ya shiga bugawa da karfi,daf za’a sauke glass din kenan saiga motar taheer ata bayanta yana mata horn ya iso wajen cikin tukin gaggawa Da alama Shima Kallon jeep din yakeyi tundaga can nesa.

Haka kawai yaji duk ya tsargu da ganin motar wani abu aransa ya shiga bashi cewa kamar saheeb ne aciki

Ai Tun bai kammala parking ba ya bude motarsa cikin gaggawa ya sauko, zuciyarsa na wani bugawa cikin hanzari ya iso gareta yajanye hannunta ta dawota gefensa ya rike mata hannunta dam dam.,wani irin lafewa tay ajikinshi ta tamke masa riga.

atare dukansu suka tsaya sukayi tsuru tsuru suna kallon jeep din da zuwar taheer din ne yasaka shi yay wani wawan reverse ya kara da gaba agurguce kamar wani marar gaskiya.

Boyayyar ajiyar zuciya taheer Ya sauÆ™e snn ya juyo a hankli ya dubeta ransa a dan harde yace mata”waye wannan din?

sake hanun shi tay a hnkli cikin sanyin murya ta kalle shi suna kallon juna tace”Yaya nima ban sani ba nima yanzu nazo nan..kafin ta cigaba da bayanin ya tsareta da idonsa mai cike da tuhuma yana kallon dan karamin bakinta da ya furta maganan da kyau
Girarsa daya na dage a can sama Yace”and where cud u have u been?Kafun ta amsa shi yaji ya harzuka ya dada tamke fusknsa cikin masifa da fada yace “bakida hankli ne?”Bana ce miki karki na barin nan wajen ba,yanzu toh daga ina kika fito? Dan Baya taja kadan da alaman batason yanamata ihu akai tanamai make kafadunta cikin shagwababben yanayi mai cikeda fargaba.,
kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta tace”..yaa fa yunwa nakeji shine naje wancan shagon na siyo abu naci”..bin inda hannunta yake nunawa yy da kallo yy yaga kiosk din cike da majalinsa maza a bakin wajen wani karin bakin ciki yaji ta cakke zucyrshi ,duk tana lura dashi ganin kishin ta duk ya sauya masa yanayi
“.dada cunkuna fuskanta tayi cikin sakaltaccen yanayi mai sanyi ta dan riko hannunshi,cikin sanyin murya tace,..yaa dan Allah kay hakuri yunwa fa nadingaji..!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191Next page

Leave a Reply

Back to top button