
kamar wanda ta kwara ruwan sanyi acikin zuciyarsa haka yaji wani sanyi data furta masa hakan, ajiyar zciya ya sauke ya dan kalleta sai baice uffan ba yanata kallonta dai,,dauke kansa yay ya kalli inda jeep din dazu yay snn ya juya kadan ya kalle shago,can dai ya bawa zcyarsa hkri ya basar, babu yabo babu fallasa yace”..get into the car Lets go,Juyawa tay ta shiga motar ta zauna agidan gaba snn shima ya zago ya bude motar ya shiga ya zauna snn yajasu suka wuce gida..
Karfe 6 saura minti biyar suka iso bakin gate din gidansun, babu irin danna horn din da baiyi ba amma shiru babu wanda yazo ya bude,har kusan minti ashirin malam musa bai fito ba,tsaki ya dingaja yarasa inda malam musa zaije a wann lokacin ga dan banzan gajiya da yunwa da ya kwaso.
Saukowa yay duk ya gaji
Yanata maganan zuci ya karaso yazo dakanshi yaja gate din ya buÉ—e sann ya koma ya shiga ya jasu su suka shigo ciki..
Yana kammala parking ya umarce wasime data shige cikin gida harta mule ciki bai dena kallon ta,daga inda yake tsaye ya tsime yaja tsaki ya soma kwallawa malam musa kira.
“musa…musa..where are u?..kai musa…shiru baiji an amsa ba,a harzuke ya nufi dakinsa ya yaye labulen yaga shol babu shi,tsaki yaja ya nufo bakin gate din ya ja ya kulle,yace”..very stupid man zaizo yagamin inda yaje yau”
Baigama rufe bakinsa ba saiga wasime ta rugo wajensa aguje hartana dan haki,kallon ta yay da mamaki yaga banda jakarta data yasar a tsakiyar daki komina jikinta was intact.
Tsayawa yy da mamaki ayanayinsa Yana dubanta,a mugun tsorace ta tsaya can ta hau nuna masa hanya da yatsarta ta shiga cewa.
“Yaaa..yaya..Yaya wani abune acikin dakinmu yanata nishi,nishi….
yace mene?
Take idanunta suka ciko da ruwan hawaye,ta dora hannu a fuskanta cikin yanayin fargaba da sautin kuka dake son kufce mata tace
“Ai banga kowa bane a gidan,kuma kawai ina shiga daki sai naji wani motsi motsi,nifa tsoro nakeji.
Baice mata komi ba ya kada kansa yawuce fuuu yay cikin gidan tahau binsa a baya Sauri yakeyi har suka isa cikin dakin atare, suna isa ya somajin motsi motsin ta bayan gida cikin gaggawa ya isa bakin kofar bayin yadan lafe yana cewa”bilti?Bilti is that you…dan Allah ki bude kofar..meya sameki?bilti..jin anyi shiru yasakashi yahau bubbuga kofar bayin da dan karfi xcyarsa na bugawa da tunanin ko wani abu ya same biltin ne.
Atake jikin wasime ma yahau rawa rawa ta soma tunanin ko wani mummunan abu ya faru da biltinta ne idanunta take suka tara ruwa.
Taheer yacigaba da buga kofar yana cewa “bilti pls open d door?are u okay?..toh ki amsani mana!pls say sumtin..
Furta hakan yake da damuwa a muryansa
Malam musa dake cikin wani mawuyacin hali ji yay kamar zai sake fitsari ajikinshi don tsoro,..
Kuka mai tsanani ya fashe dashi a hankli sanin nashi yau ta kare
Dan saida ya farfado snn hankli ta shigesa ya soma tunanin abunda ya aikata ma bilti baibi hanya ba kwata kwata.
Tun farfadowan sa yake cikin mayuyacin halin tashin hankli da nadama mai tsanani gashi bilti ta rufesa kirif acikin bayin babu tayaddaa zaiyi ya bude kansa.
Yasan yau mai rabashi da taheer sai Allah halama ayi masa hukuncin dayafi na tolu tsauri…Wani irin gigitaccen ihu ya rushe da shi wanda baima san lokacin daya fito daga bakinsa ba Cike da rudewa da firgita yace Wayyyoo Allah na
Wallahi sharrin shaidan ne…sharrin shaidan ne..
Ni ba mazinaci ba…wayyo ALLAH NA.
Acikin rudani taheer ya tsinkayo sautin muryan malam musa yana juyawa kadan suka hade ido da wasime wanda yaga alaman rudewar itama ayanayinta
Cikin gaggawa ya dauke idanunsa,Girgiza kofar yashigayi ganin bazai budu ba yay saurin barin wajen ya wuce dakinsa agaggauce domin dauko spare keys,a tsaye cak wasime ta tsaya kamar wanda aka dasata gabaki daya ta tsurama kofar ido yanayinta cike da rudani da tsananin mamaki.
Kanta sai ringing yakeyi da tarin tamboyoyi..
“Kwata kwata Bataga biltinta ba,Ina bilti?”Yo mezai kawo malam musa cikin dakinsu harma ya kulle kansa a bayan gida?..
Tana cikin wannan tunanin saiga taheer ya shigo dakin jikinshi a matukar sanyaye yana tahowa kamar wanda akayi masa duka yana kallon kofar bayin da wani irin rikitaciyar salo
Lettern da bilti tabar masa akan table ne a hannunsa, yaci karo dashi ne ayayin da yake shirin sauÆ™a izuwa dakinsa dauko key,tun a dakinsa ya zauna ya gama karantawa snn ya fito…
Idanunsa take suka sauya kala sukayi jaa yarasa wani irin masiface haka take shirin tunkarosu…
Wani duhu duhu ya soma gani,tahowa kawai yake tamkar wanda baiya kallon gabansa zuciyansa na wani irin halbawa da wani irin radadin da baiyi tsammani ba.
How can this happen to him,Bilti is more like a mother to him tunda itace ta raineshi harya girma
Wani irin zafi yakeji aransa,He is feeling the pain immensely tamkar mahaifyarshi aka taÉ“a haka yakejin radadin ta acikin zcyarsa…
Muryansa na rawa rawa ya dubi wasime da raunataccen yanayin sa da ya mugun bata tsoro, ahankli cikin raunataccen murya yace “jeki dakina kizauna kijirani awajen ina zuwa.Yadda yy maganan araunane yasaka Batayi gardama ta juya ta tafi….
Zama yay a bakin gadon su jikinshi a matukar sanyaye,a hnkli ya kara bude letter don ya sake karantawa hannun shi take ya soma bari,baiko iya kaiwa layin farko ba hawaye suka cikka kwayar idanunshi suna zubowa zirrrrr da wani irin turirin bacin rai da tashin hanklin dayake famar dabaibaye shi
Ya rasa meyasa abubuwa suke faruwa dasu haka.
First it was his best friend saheeb againts his lovely wife,ga case din tolu and now malam musa is trying to rape bilti,zuciyarsa ce ta dau nauyi ya rasa inda zai aje kanshi” what the hell is happening?..tambayan daya shiga yi makansa kenan,shiru yy cikin nazari yana tunanin kansa, “yace shin wasu irin mutane ne suke zagaye da rayuwarsa tunda can haka da bai lura da irin boyayyar halayayyar su ba?
Its pains him to stupor daya fahimce cewa ashe duk mutanen banza ne ke zagaye dashi,they all want to hurt him nd destroy his peace..mafi munin abunma shine sudin ne agefe da gefen sa wanda ya amince dasu tsawon lokaci..
yaga dai iya adalci suna yi ma maikatansu,kudi abinci muhallin kwana da duk wani hasafi ba’a gazawa..zai iyayin rantsuwa tsakanin shi da Allah bai taÉ“a lattin biyan su albashi koda na rana daya ba.
But why are they repaying them with sexual assaults?lumshe idanunsa yay snn ya bude yana maijin zafin abun,ya tuna how much
He trusted saheeb all his life baida wani aboki sai shi..Tolu da malam musa have been serving them for good 10yrs basu taba nuna masa alaman haka ba.
Hawayenshi ya share snn ya lumshe idanuwan sa sosai yana sauke nannauyar ajiyar zuciya
Wayarsa ya zare acikin aljihunsa,hannun sa na bari bari yay unlocking ya bude message yahau rubuta sako cikin gaggawa snn ya tura saƙon wa mahukuntan su na sojoji.
Shide yasan in yakama malam musa to babu shakka yau kam saida ayi waninsa amma bashi ba,the only justice he will do to him now is to send him to prison nd charge him for sexual assault.
Amma kafin nan so yake shima akaisa barikin sojoji a gana masa a zaba for biltis sake snn su hadashi da yan sanda a gurfanan da shi a kotu dan dolene kawai a kulle mishi malam musa agidan kaso.